Connect with us

ADON GARI

ADON GARI: Dalilin Da Ya Sa Muke Tallafa Wa Marasa Galihu — Asma’u Alkali

Published

on

HAJIYA NANA ASMA’U ALKALI tsohuwar Malama ce kuma Darakta a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kebbi, bugu da kari ita ce Daraktar Zartarwa a Cibiyar ‘Tallafi Foundation’ da ke aikin tallafa wa marayu da mata mararsa galihu a tsawon shekaru takwas da suka gabata. A wannan tattaunawar da ta yi da wakilinmu, UMAR FARUK ta yi bayanin tarihin rayuwa, aikace- aikacen da ta gudanar da ayyukan tallafin da cibiyarta ke bayarwa. Ga cikakkar hirar.

Za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu?

An haife ni a ranar 17 ga watan Satumba a shekarar 1964 a unguwar Zoramawa a Karamar Hukumar Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi. Na fara karatun Firamare a makarantar ‘Town model’ a 1971 zuwa 1976, inda na yi aji bakwai a wannan makarantar, daga nan na shiga makarantar Horas da Malamai ta ‘yan mata ta Birnin Kebbi a 1976 zuwa 1982, a nan na yi shekara shida, a wannan makarantar na kammala karatun Sakandare. Bayan na kammala sai na wuce zuwa Kwalejin koyon aikin malanta, wato (Maru Teachers College), inda na kammala karatun NCE a shekarar 1983 -1986.

Bayan na dawo gida sai na sami aikin karantarwa a makarantar ‘yan mata da na kammala a matakin Sakandare, wato Women Teachers College a matsayin Malama mai koyar da harshen Turanci, don shi na karanta. Bayan shekara biyu sai na koma Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato a shekar ta 1988 inda na ci gaba da karatun harshen Turanci ta hanyar Malantaka, wato (B .ed English). Bayan na kammala sai na je yi wa kasa hidima a Ilorin ta jihar Kwara a 1992, bayan na fito daga sansanin sai aka dawo da ni a jihar Kebbi inda aka tura ni wata Kwalejin ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Kangiwa a Karamar Hukumar Arewa, don bauta wa kasa a matsayar Malama mai bautar kasa.

A shekarar 1993 na kammala bautar kasa daga, nan sai na dawo wurin aikina a matsayin Malama a Kwalejin ‘yan mata, wato(WTC Birnin Kebbi). Bayan shekaru biyu sai aka ba ni mukamin mataimakiyar shugabar Kwalejin a matsayin mai kula da sha’anin ilimin Kwalejin a 1998-1999. Daga nan kuma sai aka sauya mani aiki zuwa ga mai kula da tsarin mulki ta Kwalejin har tsawon sheka daya.

Daga nan sai tsohuwar Gwamnatin Adamu Aliero ta ba ni mukamin shugabar kwalejin wadda na rike daga shekarar 2001 zuwa 2007. Haka ma na rike mukamin Mai Bayar da Shawara ga Uwar Gidan Gwamnan Jihar Kebbi a zamanin Aliero kan lamurran mata. A yanzu haka ni ce Darakta ta cibiyar kula da sashen ilimin mata a ma’aikatar ilimi.

Baya ga wannan kuma ni ke jagorantar shirin fadakarwa kan ciwon sankarar mama ga mata ‘yan makaranta a duk fadin jihar ta Kebbi. Shiri ne da matar Gwamna, Dakta Zainab Abubakar Atiku Bagudu ta ke daukar nauyi mai suna ‘Medicaid Cancer Foundation.’ Ina amfani da wannan damar wajen ilmantarwa da fadakarwa ga dalibai mata.

 

A wane lokaci kika kafa kungiyar tallafa wa marayu da mata marasa gata, kuma mene ne ya ja hankalin ki ga kafa kungiyar?

Alhamdulillahi. Na kafa kungiyar bayar da talllafi mai suna ‘Tallafi Foundation For Orphanage, Widows And Less Prebileged’ wadda ke da ofishi a nan Birnin Kebbi. Wannan cibiyar tallafi ta kai kimanin shekara takwas da kafawa domin tun a farkon 2009 aka kafa ta, har yanzu nan tana kan aikin ta da aka tsara bisa ga manufar da aka kafa ta. Kuma ni  ke da wannan cibiyar tallafi wadda nake matsayin Daraktar Zartaswa.

Kazalika daya daga cikin abin da Tallafi Foundation ke yi shine bayar da tallafi ga marayu domin tabbatar da cewa sun samu ilimi yadda kowa ne irin yaro mai gata ke samu, suma su samu hakan, sai kuma mata wadanda mazajen su suka rasu, na kan yi kokarin ganin cewa sun koyi sana’o’in hannu na zamani da kuma saye da sayarwa a cikin gidajensu domin su samu abin dogaro da kai, domin su rika daukar lalurar yara a gida.

Bugu da kari muna bada tallafi ga sha’anin addini ga yara mata da maza musamnn domin ganin sun hardace kur’ani. Wannan Tallafi Foundation ina gudanar da shi ne da albashina sai taimakon mai gida na da kuma ‘yan uwana, duk lokacin da na tunkari mai gida na ko ‘yan uwa suna bani goyon baya sosai shi ya kara mani karfin guiwar ci gaba da bada wannan tallafin, a halin yanzu cibiyar ta tallafawa fiye da mata da maza talatin a wannan jihar wadanda a yanzu haka suna furamare, sakandare da kuma manyan kwaleji kuma yaran su ne ke daukar matsayi na daya a makarantun su.

Har ila yau tun lokacin da na kafa wannan cibiyar ta bada tallafi ban taba zuwa wurin wani da sunan ya taimaka mani ba, amma Sanata Abubakar Atiku Bagudu Gwamnan jihar Kebbi ya taba baiwa cibiyar naira dubu dari  gudunmuwa, kuma a lokacin baya da wani matsayi a cikin siyasa.

Alhamdulillahi a yanzu wannan cibiyar tawa sai gaba-gaba ta ke yi domin hadaddiyar cibiyar nan da ta yi suna a duniya ta samu labarin irin tallafin da cibiyar tawa ke yi wato Bill/Melinda Gate Foundation ta kawo gudunmuwar ta ga cibiyar domin hadin guiwa a tsakanin cibiyoyi biyu, a halin yanzu akwai wannan hadin guiwar. A gaskiya ni yanzu dole ne na gode wa Allah da mai gida na da kuma ‘yan uwana ga irin gudun muwar da suke bani har na iya cinma nasarorin da na cinma a yanzu.

 

Ko akwai wani kalubale da kike fuskanta a wannan cibiyar?

A gaskiya babu, domin kamar yadda da na fada tun da farko cewa bana zuwa wurin kowa neman taimako kan cibiyar, kamar yadda na ce na kafa wannan cibiyar ce da albashi na sai mai gida na da ya ke taimaka wa sosai ga ci gaban cibiyar domin ko ofishin cibiyar shi ne ya gina shi, wanda ya lashe miliyoyin nairori. Haka zalika ‘yan uwana suma ba a bar su a baya ba wurin ganin cewa cibiyar ta ci-gaba, wannan tallafi ya samo asali ne daga mahaifin na wanda ya tarbiyantar da yaransa ga sha’anin ilimi da kuma tallafawa marayu da kuma marasa galihu a cikin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: