Connect with us

TATTAUNAWA

Yadda Gwamnatin Adamawa Ke Yaki Da Talauci —Ayyuba

Published

on

MALAM AYUBA AUDU shi ne mai baiwa Gwamna Umaru Bindow Jibrilla na jihar Adamawa shawara kan rage talauci da farfado da tattalin arziki, a lokaci guda kuma shi ne shugaban shirin koyar da sana’o’in dogaro da kai da Gwamnatin jihar ta bullo da shi. LEADERSHIP Hausa ta samu tattaunawa da shi, ya kuma yi mata cikakken bayani kan shirye-shiryen da Gwamnatin jihar ta bullo da shi na farfado da tattalin arziki da rage talauci, da ma shirin koyar da ‘yan gudun hijira sana’o’in dogaro da kai. A  sha karatu lafiya.

Wannan shiri na baiwa ‘yan gudun hijira horo, kamar mene ne gudumawar Gwamnatin jiha a kai?

Kamar yadda ka sani shi mai Girma Gwamna Sanata Umaru Bindow Jibrilla Sardaunan Mubi, lokacin da ita NUDP ta zo ta ce ta na son ta yi shirin tallafa wa matasa wanda aka zabo su daga sansanin ‘yan gudun hijira, to da suka zaga suka kalli irin abubuwan da muke da shi na koyar da sana’a a nan jihar Adamawa, sun duba a cikin jihohin da ake da matsalar Boko Haram babu jihar da ta ke da kayan koyon sana’a da yara ke bukata kamar irin na jiharmu Adamawa. Mun zagaya da su cibiyoyin koyon sana’ar da muke dasu guda 10 shine suka ce suna son a koyawa yaran sana’a a tare waje guda ne su 179 daga jihohin Borno Yobe da Adamawa, to yaran da yardan Allah da ikonsa suna koyon sana’a a makarantar koyon sana’o’i da ke Yola ta Kudu za su koyi sana’a na tsawon watanni shida.

To mu ko da wane lokaci muna dubawa ta wannan ofis nawa muga wace sana’a cw za a koya ma mutane wanda zai ba su kudin shiga, sai muka kirkiro sana’o’i guda biyu na koyan yadda ake windo na zamani da kofa ta zamani. Abin da ya sa muka kirkiri wannan sana’a, da ma a baya can ba a koyar da su a wadannan makarantun da muke da su, mun duba yanzu komai yana tafiya da zamani, an samu ci gaba, sai muka ga ya kamata a koyawa yaranmu aikin windo na zamani saboda kowaye yanzu in ya yi gini yana son in ya gama ya sa windo da kofa ta zamani, ka ga lokacin da suka gama sun fara nasu za su samu kudaden shiga ta yadda mutane za su rinka sayen winduna da kofofi.

Baya ga wannan sai muka duba kuma yanzu duniya gaba daya ta zama tamkar wani karamin kauye ta dunkule wuri guda, to sai muka ce akwai karancin yaran da suka iya gyara wayoyin hannu, sai muka ce kirkiro da yadda za a koya wa yaran gyaran wayar hannu, shi Mai Girma Gwamna da yake kodayaushe yana hangen nesa, mun tattauna da shi muka sayo kayan aikin gyaran wayan na zamani ta yadda ba sai an bude waya ana ta kwakole-kwakole ba, sai aka sayo Kwanfutar zamani da na’urar zamani, wacce da ka sa a waya zai gaya maka matsalar waya, idan matsalar earpiece ko mouse daga an shigar ma na’urar za ta fada maka, ka ga abin da muka yi saboda a koya wa yaranmu wadannan sana’o’in guda biyu, domin su ma idan sun koya su samu kudaden shiga saboda mutane za su kawo musu aiki.

 

Bayan sun kammala aikin horon, ko akwai wani tanadin da kuka yi masu?

Abin da zan so na sake nanatawa shi ne, su wadannan yaran da muke koya masu sana’o’i, wani abu ne na daban da Gwamnatin Adamawa ta ke kokarin bunkasawa domin a yadda yaran za su dogara da kansu, su wadannan makarantu can baya bama baiwa yara su kwana makarantu ne da aka yi su a Kananan Hukumomi guda 10 yara ne suke zuwa su koyi sana’a su koma gida su kwana. Amma kamar yadda nake fadi, shi Mai Girma Gwamna da basirar da Allah ya yi masa da tunani muka duba yaya za mu yi, yaran ba na Adamawa ba ne kadai, wasu sun fito daga jihar Borno, wasu daga Yobe, sannan kuma ko wadanda suka fito daga Adamawa ma sun fito ne daga Kananan Hukumomi bakwai, wadanda aka samu matsalar Boko Haram, sai muka samar masu da wajen kwana a nan cikin makarantar da ke Yola ta Kudu, a wajen za su rinka kwana saboda abin da ya kai su koyon sana’a shi kawai za su yi, kuma da tsarin koyar da sana’o’in na wata uku ne, amma su wadannan za su koyi sana’a na tsawon wata shida ne, don wanda za ka koya masa sana’a na wata uku ba zai yi kamar wanda ya koyi na wata shida ba, wanda aka koya ma na wata shida in ya fita yanayin sana’ar za ka ga akwai bambanci. Yaran nan tunanin da ita UNDP da kuma gwamnatin jihar su ke yi shi ne za a tallafa masu a saya masu kayan aikin da suka koya, domin su ma su je su bude nasu, sannan kuma su ma su samu mutum daya ko biyu su koya masu, to shi ne tunanin mu.

 

Kamar mene ne manufar Gwamnatin na bullo da wannan shirin?

To, dama Mai Girma Gwamna kamar yadda ka sani matashi ne, kuma lokacin da yake yakin neman zabe ya yi wa matasa maza da mata alkawarin idan ya zama Gwamnan Adamawa zai koya wa yara sana’o’in da za su dogara da kansu, saboda ba ya son yadda yara suke yawo ba su da abin yi, ba sa zuwa makaranta, yara suna bangar siyasa da kuma mata.

To da ikon Allah dama can akwai makarantun da gwamnatin Baba Mai Mangoro da ta shude ta gina, amma dama an rufe makarantun ba a yin komai da su, da Allah ya sa Gwamna Bindow ya zo ya kuma kirikiro wannan ofishin na bashi shawara kan rage talauci da tattalin arziki wanda nake jagora kuma ni nake ba shi shawara akan farfado da tattalin arziki da rage talauci, sai ya nada kwamiti, shi ne Shugaba, ni kuma Sakatare.

Muka za ga makarantun guda 10 muka duba yadda makarantun suke da kayayyakin da makarantun ke bukata, to a yadda muka ga makarantun, ba zai yiwu mu iya budesu gaba daya a lokaci daya ba, saboda ko gida ka rufe tsawon shekaru biyu, yaya kake gani? Dole yana bukatar gyare-gyare, ga shi kuma yanzu ba a samun kudin shiga kamar yadda can baya suke samu.

To sai muka bude gudu uku a kowace ‘Senatorial district,’ mun bude guda daya, to sai muka duba kuma girman ‘Southern Senatorial’ sai muka kara bude daya a Numan, to mun bude makarantun nan guda 4, saboda yana cikin alkawuran da mai girma Gwamna ya yi wa matasa da mata, kan cewa za a koya masu sana’a, za a kuma ba su jari su dogara da kansu, da muka budesu sai muka fara da daukar yara 60.

Akwai wani kamfani da ke kera keke Napep, wacce ake kira ‘Simber’ muka shiga yarjejeniya da su su koya wa yaran yadda ake gyara wannan keken, yaran 60 da muka ba su horon sun gama an basu sufanu sannan gwamnatin jiha ta ba su kudaden da za su samu shago, kuma sai muka sake shiga yarjeneniya da ITF dama ita ta gwamnatin tarayya ce tana koyar da sana’a. To sai muka hada kai suka koyawa yara 400 sana’a, mata an koya masu yin abin wuya da abin hannu, wasu matan kuma sun koyi aikin gyaran wuta na gida na zamani, don haka ba duk matan ne sun koyi abin wuya da na hannu da sake-sake ba.

Kuma yaro yana da zabin abin da yake son ya koya. Baya haka ne muka debo yara 197 da na yi bayani, ba mu tsaya a nan ba, muka sake shiga wata yarjeneniya da kamfanin da ya kware a harkar yanar gizo, ita Google ke nan da ita gwamnatin tarayya suka kulla yarjejeniya suka koyar da mutane 1247 a Kananan Hukumomin jihar 21 aka zabo yaran aka yi masu cibiyoyi 6 na koyon sana’ar. Yanzu muna kokarin mu shiga harkar koyar da yara a makarantun gadan-gadan kamar yadda aka saba a da can baya.

 

To, su ma mambobin Majalisar Dokokin jiha suna gudanar da irin wadannan shirye-shirye (bada horo kan sana’o’i) a Kananan Hukumominsu, kuma ka kai ziyarar gani da ido a wasu daga cikin cibiyoyin, kamar ka gamsu da abin da ka gani?

Eh to, a kashin gaskiya ni dai na rufa shekara 51 a rayuwana a duniya yanzu, kuma na dade ina harka da ‘yan siyasa inaga irin abubuwan da ‘yan siyasa su ke yi, gaskiya zan fada maka ni tun da’ake siyasa ban taba ganin ‘yan Majalisa na Kananan Hukumomi sun yi ayyuka kamar yadda ‘yan Majalisarmu na yanzu su ke yi ba.

Saboda na samu daman a ziyarci Kananan Hukumomi 21 na ga irin ayyukan da su ka yi, ‘yan Majalisarmu sunyi rawar gani, kuma ina jaddada masu su ci gaba da ayyukan da suke yi, domin dama cin moriyar siyasa daga kasa ya kamata. Yanzu ba Karamar Hukumar da za ka je ba ka samu aikin dan Majalisa ba, wasu sun samar da ruwa wasu sun yi makarantu wasu sun gyara kasuwanni wasu sun yi hanya sun kai har wuta. Wannan yana nuni da hadin kai da yake akwai tsakanin bangaren Gwamna da ‘yan Majalisun jiha da na tarayya.

 

Wato dai manufarku a karkashin ofishinka shi ne farfado da tattalin arziki da rage talauci ga jama’ar Adamawa?

Eh shi ne manufarmu, kuma In sha Allahu in ka duba rage talauci da farfado da tattalin arziki ya kunshi abubuwa da yawa, idan an ce rage talauci ya kunshi bada ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwan sha inganta hanyoyi, duk ya kunshi rage talauci. Saboda haka hanyoyin da mai girma Gwamna ya yi ya rage talauci da kashi hamsin a Adamawa.

Saboda da mai girma Gwamna ba kawai hanyoyin cikin gari ya yi ba, a’a yayi hanyoyi a karkara. Misali, ya yi hanya daga Michika zuwa Zaah, hanya ce wanda mutanen Zaah kafin su je Michika sai ya daukesu awa hudu, amma yanzu mutumin Zaah zai tashi ya je Michika cikin awa daya kacal, ka ga Gwamna ya rage talauci ya rage lokaci na tafiya, ya rage talauci ya farfado da tattalin arziki ta nan.

Sannan mai girma Gwamna ya yi hanya daga Shuwa zuwa Pall, sannan an yi asibitoci ta yadda matan karkara cikin sauki za akai su asibiti. Kamar yadda ka sani, mu a Adamawa mun dogara ne da noma, to tun Gongola ba a taba kawo taraktoci guda 105 ba a lokaci guda, kowace Karamar Hukuma an ba ta tarakta 5, ka ga wannan fanni ne na rage talauci. Mai girma Gwamna ya kawo takin zamani, wanda kowa zai samu taki a farashi mai rahusa, an kawo magunguna da sauransu, duk wadannan abubuwan su ne mai girma Gwamna yake yi domin farfado da tattalin arziki da rage talauci ga jama’ar jihar Adamawa.

 

Wace kira kake da shi ga al’ummar Adamawa?

Kiran da nake yi ma mutanenmu na Adamawa shi ne, su ci gaba da irin addu’o’in da suke yi wa mai girma Gwamna Sanata Umaru Bindow Jibrilla, in ba tare da addu’o’insu da hadin kai da goyon bayan da suke ba shi ba, da ba zai iya yin ayyukan da ya shinfida a kasa kowa yana gani yanzu ba.

Saboda da haka da addu’arsu da goyon bayan da suke ba shi ya sa koyaushe Allah Ubangiji yake ba shi basira da karfi da lafiya yake irin ayyukan da yake yi yanzu. Don haka su ci gaba da addu’o su ci gaba da ba shi goyon baya akan irin ayyukan da yake yi, kada su ji abin da ‘yan adawa suke fadi da sauransu. Da ma ko a ina ne akwai adawa, amma mai girma Gwamna ya taka rawar gani, wanda wannan ne ma ya sa kamfanin jaridar LEADERSHIP ya ba shi lambar yabo na kasa baki daya, kuma gidan jaridu da kamfanoni suna ba shi lambar yabo. Kazalika saboda abubuwan da ya shinfida, mataimakin shugaban kasa ya zo da kansa ya ga irin ayyukan da shi mai girma Gwamna yake yi. Idan mun ci gaba da ba shi goyon baya da addu’a, sauran shekaru biyu masu zuwa zai yi mana ayyuka masu kyau. Allah kuma ya ba shi wa’adi na biyu domin ya ci gaba da wadannan kyawawan ayyukan.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: