Connect with us

LABARAI

Cikin Watanni Bakwai Hukumar Kwastan Ta Tara Miliyoyi A Adamawa

Published

on


Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Hukumar yaki da ayyukan fasa kwauri ta Nijeriya (Nigeria Customs Serbice) reshen jihohin Adamawa da Taraba, ta tara sama da Naira miliyan dari daya da goma sha daya (111,000,000.00), a matsayin kudaden haraji cikin watanni bakwai.

Shugaban hukumar a jihohin biyu Mista Adetoye Francis, ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Yola, ya ce, duk da matsalar ayukan ‘yan ta’adda  da lalacewar hanyoyi da karyewar gadoji da su ke haifar da koma baya wajan samun kudaden shigar.

Mista Adetoye yace, wata matsalar da jami’an hukumar ke fuskanta itace ta rashin samun hadinkan jama’a mazauna kan iyakokin jihohin biyu da Jamhoriyar Kamaru.Ya ce, amma hukumar ta tara kudaden da kame wasu jarkokin man fetur dari hudu.“Duk da wadannan matsalolin mun tara wadannan kudaden harajin  Naira 11,745,317,43 mun kuma tara wasu kudaden Naira miliyan arba’in da biyu da dubu dari bakwai da hamsin da shida na  tarar shigo da motoci ta haramtacciyar hanya.”

Shugaban hukumar fasa kwauri ta jihohin Adamawa da Taraba yace adadin kudaden da hukumar ta tara ya karu matuka  da Naira miliyan ashirin da shida,  idan aka kwatanta da adadin kudaden da hukumar ta tara a shekarar 2016.

Mista Francis ya koka da cewa a wasu lokutan jami’an hukumar kan gamu da fushin jama’a wanda hakan ke kai su ga kokarin sha da kyar da taimakon sarakunan gargajiya a yankin kan iyakar jihohin biyu da jamhoriyar Kamaru.Baya ga kudaden shigar da hukumar tatara shugaban ya kuma mika  hukumar tsaron farin kaya ta Cibildefiance jarakun man fetur 400 ta da kame kan iayakokin jihohin biyun da Kamaru.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI