Connect with us

KASASHEN WAJE

Fursunoni Sama Da 100 Sun Tsere Daga Birtaniya

Published

on


Gwamnatin kasar Birtaniya ta ce fursunoni sama da 100 masu hatsarin gaske suka tsere daga gidan yari da ke Tsubirin Birgin Islands yayin da mahaukaciyar ambaliyar ruwa da Iska ta ratsa yankunan Birtaniya

Karamin Ministan Waje  Alan Duncan ya shaida wa majalisar Britaniya cewa wannan tsubiri na Birgin Islands na cikin hatsari saboda tserewar wadannan fursunoni.

Ministan ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro domin ganin an kama na kamawa da tabbatar da babu wani kazamin labari da ya auku.

A cewar Ministan,  Gwamnati ta yi kokari domin ganin mahaukaciyar ambaliyar ruwa da iska sun wuce kuma mutan 9 ne suka mutu bayan da ambaliyar ta wuce.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI