Connect with us

WASANNI

Cikin Ruwan Sanyi Za Mu Lallasa Chelsea Har Gida – Petr Cech

Published

on


Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Petr Cech ya ce tawagar ‘yan wasan Arsenal ta san hanyar da za ta bi wajen ganin ta doke kungiyar Chelsea a wasan da zasu kara a ranar Lahadi, sannan ya ce za su farfado daga cin da Liberpool ta yi masu a kwanakin baya.

Arsenal dai ta samu nasara a satin da ya gabata bayan da ta doke kungiyar Bournemouth daco 3-0 a filin wasa na Emirate da ke birnin London.

Rabon da Arsenal ta doke Chelsea a filin wasa na Stamford Bridge dai tun a watan Octoba na shekara ta 2011, sai dai mai tsaron ragar ya ce wannan karon sun shirya kuma yana da yakinin cewa za su doke Chelsea har gida.

Arsenal ta doke Chelsea a wasan karshe na cin kofin kalubale na kasar Ingila, sannan sun doke Chelsea a wasan karshe na cin kofin Community Shield duk a wannan shekarar.

Sai dai cech ya ce ya san suna sane da nasarar da suka samu dasu a baya kuma ya san ‘yan wasan na Chelsea za su dage, amma za su yi kokarin sun sake doke su.

A cikin wasanni hudu da aka fafata a gasar Firimiya a yanzu, arsenal ta samu nasara a wasanni biyu yayinda aka samu nasara akanta a wasanni biyu.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI