Connect with us

WASANNI

Barcelona Ba Za Ta Iya Zama Babu Messi Ba — Iniesta

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, andries Iniesta ya bayyana cewa ƙungiyar tasu bazata iya rabuwa da messi ba saboda haka yakamata suyi saurin ƙara masa sabon kwantaragi.

Iniesta ya bayyana hakane awanni kadan bayan ya sake sabon kwantaragi da ƙungiyar inda zaici gaba da zama a ƙungiyar har abada.

Yace, ƙungiyar bazata iya buga wasanni babu messi ba indai yana raye saboda haka baiga amfanin zama har yanzu basu sake sabuwar yarjejeniya da dan wasan ba.

Ya ƙara da cewa Messi dan wasane da babu kamarsa kuma bazasu yarda ya subuce musu yakamata ayi duk abinda yakamata domin ganin wata ƙungiyar bata dauke musu shiba.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar Josep Maria Bartomeu dai a kwanakin baya yana yawan cewa sun kammala tattaunawa da dan wasan abinda yarage kawai lokaci ake jira,

Sai dai wasu rahotannin sunce tattaunawar da dan wasan ta tsaya tun a watannin baya abinda kuma ƙungiyar ta ƙaryata inda tace tattaunawa tayi nisa da dan wasan kuma nan gaba kadan zasu sanarwa da duniya.

Shima dai iniesta a kwanakin baya ya taba cewa bai sani ba ko zai zauna a ƙungiyar ko kuma zai tafi kafin yasake sabon kwantaraginsa a wannan satin.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI