Connect with us

MANYAN LABARAI

Haƙar Mai Da Harkar Tsaro: Buhari ya Gana Da Gwamnonin Arewa Uku

Published

on


Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

A jiya Litinin, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wata muhimmiyar ganawa da gwamnonin jihohin arewa uku, waɗanda suka haɗa da Gwamnan Sakkwato Aminu Tambuwal, Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, Gwamnan Yobe, Ibrahim Gaidam. An gudanar da ganawar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Haka nan kuma gwamnonin sun samu ganawa ne da shugaban ƙasan, a lokuta mabambanta, inda suka yi mishi bayani dangane da al’amuran da ke faruwa a jihohinsu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ganawar, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa, sun gana ne da shugaba Buhari dangane da shirye-shiryen haƙar man fetur da za a fara a Jihar Sakkwato.

Ya ƙara da cewa, banda wannan sun tattauna akan wasu ƙarin batutuwa, musamman ma ɓangaren zaman lafiyan ƙasar nan.

Tambuwal ya bayyana cewa: “Idan dai ba za ku manta ba, a kwanakin baya na zo da kaina zuwa hedikwatar Kamfanin NNPC inda na samu Babban Daraktansu dangane da shirin fara haƙar mai a Sakkwato, wannan shi ne abin da na zo yiwa shugaban ƙasa ƙarin haske a kai.

“Domin akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta taimaka wurin ganin wannan lamari ya cimma nasara, domin mun yi imanin cewa akwai man fetur da iskar Gas kwance a wannan yanki namu.” Inji Gwamnan

A ta ɓangarensa, Gwamnan Jihar Yobe, Gaidam ya ce: “a ganawar da muka yi da shugaban ƙasa na sanar da shi cewa ya zuwa yanzu mun samu sauƙin rikicin da ke addabar yankinmu. Sama da shekaru biyu ba mu samu rahoton hari a faɗin jihar Yobe ba.

“Haka kuma na yi mishi bayanin cewa dukkan ‘yan gudun hijira sun koma gidajensu da bakin sana’o’insu. Yanzu abu ɗaya kawai ya yi saura shi ne, gyaran wuraren da wannan rikici na Boko Haram ya rutsa da su.” Inji gwamnan.

Gaidam ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin ta mayar da duk wasu abubuwa da ta’addancin Boko Haram ya rutsa da su. Ya kuma ce gwamnatinsa na yin iya ƙoƙarinta. Sai dai suna buƙatar ƙari daga alƙawarin da shugaban ƙasa yayi musu na tallafawa.

Gwamna

A nashi ɓangaren, Gwamna Badaru ya bayyana cewa sun gana da shugaban Ƙasa Buhari ne dangane da irin ƙoƙarin da kwamitin da yake jagoranta yake yi; wanda kwamiti ne da ke lalubo hanyoyin da za a samar da wasu fannonin dogaro don rage nauyi da jingina ga arzikin man fetur.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI