Connect with us

RAHOTANNI

Buhari Ya Jajanta Wa Kasar Irak da Iran Bisa Ibtala’in Girgizan Kasa

Published

on

Daga Mubarak Umar, Bauchi

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon jajensa ga shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da kuma illahirin al’ummar kasar Iran a bisa tsautsayi ibtila’in girgizar kasa da ta same su, lamarin da ya yi mummunar barna a yammacin lardin Kermanshah a kwanakin nan. Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwar jama’a hade da kuma samun dubban majinyan da suka samu raunuka a sakamakon wannan girgizar kasar.

Shugaban Nijeriyan ya misalta lamarin da cewar mummunar bala’i da kuma mummunar yanayi “mummanar lamarin bakin ciki da kuma bala’i” ya ce “tuni hankulan ‘yan Nijeriya ya karkata kan al’umman Iran a wannan lokacin, inda ya shaida cewar Nijeriya tana tare da Iran a wannan lokacin”.

Shugaban Nijeriyan ya yi addu’ar Allah jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon ibtila’in hade kuma da yin addu’ar Allah ya baiwa wadanda suka ji raunaka lafiya, gami da yin fatan Allah ya kare aukuwar hakan gaba.

Hakazalika, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa gami da jajensa ga gwamnatin kasar Iraki a bisa ibtila’in girgizan kasa da ta yi sanadiyyar asarar dumbin dukiya a yankin kasar da ke iyaka da kasar Iran.

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo, ya shaida a ranar Alhamis a lokacin da ke bude taron ministoci karo na shida D-8, game da hadin guiwa tsakanin ma’aikatu da kasashen waje a Abuja. Ya yi maganan ne a madadin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari inda ya mika sakon jajensa ga gwamnatin kasar Iran da kuma Iraki a bisa wannan girgizar kasar da ta auko a kashashen biyun.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: