Rukunin Mutane 10 Da Za Su Bijirewa Sake Zaben Buhari A 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Rukunin Mutane 10 Da Za Su Bijirewa Sake Zaben Buhari A 2019

Published

on


08062333065  hardawamuazu@mail.com

Sanin kowa ne akwai mutane da dama da suka taimaka wajen zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekara ta 2015, kuma duk sun yi wannan zabe ne da nufin rayuwar su ta inganta, amma sai aka wayi gari wahalhalu sun shiga cikin rayuwar mutane yadda ake ganin a zabe mai zuwa yawanci wadannan mutane ba za su sake zaben gwamnatin APC ba musamman idan har aka ce ta sake tsayar da shugaban kasa Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa. Duk da cewa kaunar Buhari a jinin mutane take amma da dama sun saduda saboda a yanzu an bayyana cewa ya yi alkawurra sun fi dari biyu amma bakwai kacal ya iya cikawa, bayan kuma kowane mabiyin addini ya san cewa alkawari abin tambaya ne tun daga duniya har zuwa lahira.

Don haka na zakulo rukunin mutane goma da na ke ganin a baya sun zabi Buhari amma a zabe na gaba 2019 yawanci ba za su kuma maimaita zabar sa ba saboda ganin yadda mutane basu amfana da samun ingancin rayuwa da walwala ba, sai fatara da yunwa da tsadar kaya da talauci da rashin tallafi ko jin kai da sauran matsalolin da suka shafi rashin aikin yi, don haka ga mutane goma da nazari kan su:

Rukuni na farko na magoya bayan APC da suka rabu kashi da dama sune a kan gaba wajen gwagwarmayar kawo shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar canji dole da yin zaben a kasa a tsare a raka ajira a fada, sun yi gwagwarmaya ta hanyar tura kudin kamfen na sayen katin Buhari da yin rokon Allah da tayar da jijjiyar wuya da bijirewa ‘yan PDP masu mulki a wancan lokacin ko da tsiya ko da arziki har sai da hakar su ta cimma ruwa. Amma bayan wannan kokari wasu a halin yanzu an mayar da su gefe ba a yi da su sun zama ‘yan kallo, musamman ko bugawa shugabannin da suka zaba waya suka yi basa dagawa wasu sun rufe layin su wasu kuma ko zuwa mazabunsu basa yi. Wadanda suka samu mukaman siyasa kuma cewa suke yi su ba ‘yan siyasa ba ne, don haka wadanda suka yi wannan gwagwarmaya sun tashi bawan bawan karatun dan kama, don haka a bana zai yi wahala su sake yin irin waccan shahada, sun koma gefe sun zama ‘yan kallo suna jiran lokacin zabe ya dawo su da iyalan su dauki fansa.

Irin wadannan mutane sun hada manya da kanana’yan siyasa irin su Injiniya Buba Galadima da su Naja’atu Mohammed da su Alhaji Atiku Abubakar wanda ya koma PDP kuma akwai irinsa masu yawa da sun yi dawainiya wajen dora Buhari a kan mulki amma yanzu sun zamo ‘yan adawa da suke jiran daukar fansa nan gaba, duk da cewa sun jima da Buhari suna ziyartar sa ba dare ba rana suna buga masa waya ana nuna masa goyon baya yanzu ya zamo labara kamar almara.

Kuma akwai yiwuwar da zarar an fara kamfen idan magoya bayan PDP suka hada kan su da wasu jam’iyyun adawa suka fito da kudi tunda duk barazanar cewa su barayi ne da ake musu, har yanzu akwai masu kudi kuma suna kyauta ta fitar hankali fiye da ‘yan APC, don haka za su jawo mutane da dama saboda sanin kowa ne duk wanda ke yin siyasa baya jiran ladansa a lahira ya fi son ya gani tun yana duniya.

Saboda suma masu cewa wasu barayi akwai alamun idan sun sauka suma za a tallata tasu satar ta fi ta mutanen PDP musamman ganin yadda su basa iya kyauta, alhali shi dan Nijeriya ko sata za ka yi ka bashi ba ruwansa shi sanyi ya ke son ji a rayuwa. Saboda talauci ya baibaye dan Nijeriyai ga tunanin ya yi adawa maras amfani kuma lokacin da zai amfana ya zo amma an nuna masa bai yi komai ba sai cin zarafi da jona masa talauci da fatara da yunwa da tsadar abinci da magani da kudin makarantar yara da sauran wahalhalun rayuwa.

Rukuni na biyu sune shugabannin addinin kirista da musulmi wadanda a 2015 sun yi ta kamfe a gidajen su har da wuraren ibada, wasu har sun samu sabani da magoya bayan su. Wasu kuma shugabannin PDP na lokacin har kujerun zuwa makka da Jerusalem sun basu da su tare da magoya bayan su don su je su rokawa gwamnatin PDP Allah ta samu nasara. Amma an wayi gari yawanci sun yi ta rokon Allah da ya kawo canji saboda ganin halin da aka shiga na rashin tsaro a wancan lokacin don haka, ko ni a gabana na sha ganin wadanda ke dawafi a kasa mai tsarki ta Makka suna cewa Allah ya ba Buhari mulki duk da cewa alamu na nuna PDP ta tura su, amma an wayi gari yanzu ko kujerar zuwa Abuja ba wanda ke basu wasu sun kasance basu da farcen susa wasu hatta abinci da za su ci babu.

Bayan haka kuma hatta ginin masallatai ko cocin da suke ibada an fara cewa za su fara biyan haraji wa gwamnati, bayan haka kuma wasu limaman sun dogara da dan abin da gwamnatin PDP ke ba su na alawus ko domin yin addu’ah wa kasa, amma wannan gwamnati ta Buhari ta ce ba ruwanta, gwamnoni duk sun soke irin wannan taimako.

Alamu na nuna wannan gwamnati bata damu da addu’ar su ba alhali lokacin da suke neman mulkin duk sai da suka yi ta bin masallatai da cocin suna neman goyon baya da taimakon addu’ah inda limaman da mabiya suka yi hangen dala ba shiga birni ba da nufin idan gwamnatin Buhari ta kafu za su samu ingancin rayuwa da walwalar addini fiye da tunanin kowa, amma sai wahalar kullum kara nunkuwa ke yi saboda hatta masu ibada a irin wadannan wurare suma samun su ya koma baya wasu sun tsiyace.

Akwai misalin da zan iya bayarwa na wani limamin masallaci da ya rika kamfe wa Buhari a daya daga kasuwannin cikin garin Bauchi, har ya rika samun matsala da magoya baya domin yadda ya halasta kamfe kan munbari, amma an wayi gari Allah ya jarrabe shi da karyewar jari a wannan lokaci saboda dama yana samun ciniki da kwangila daga mutanen gwamnatin PDP da ta gabata ne yanzu kuma babu. An wayi gari wata rana za a tsai da sallah ya tsaya zai yi limanci jiri ya dauke shi, zai fadi aka rike shi ya zauna da aka tambaye shi ya ce yunwa yake ji don kwana biyu bai dora girki a gidansa ba saboda jarinsa ya kare, nan take aka nemi taimako a masallacin aka hada masa naira dubu 21 aka sayi abinci aka kai gidansa aka bashi sauran canjin ya zuba a aljihu ya murmure na dan lokaci.

Rukuni na uku sune “Yan shi’ah almajiran Sheikh Ibrahim Elzakzaky, wadanda kowa ya san suna da yawa a Nijeriya a baya basa zabe amma lokacin zaben Buhari ganin yadda wasu manyan ‘yan siyasa suka rika zuwa markazin su da ke Zariya don yin kamfen, lamarin ya sa sun sassuta ra’ayi wasu sun zabi gwamnatin Buhari da nufin rayuwar su za ta inganta su samu rangwame kan matsalar da suka fiskanta na fada da gwamnati a baya musamman ganin yadda lokacin PDP ne a gwamnatin Goodluck Jonathan aka kashe musu mutane sama da talatin ciki har da yaran Elzakzaky guda uku, don haka suma suka himmatu suka ba Muhammadu Buhari goyon baya.

Kwasham bayan hawan gwamnatin ba da jimawa ba sai aka samu akasi shugaban sojan Nijeriya Janar Burtai zai wuce ta garin Zariya a daidai lokacin da suke bikin da suka saba na gangami daga ko’ina har aka samu sabani suka tare wa soja hanya har ta kai ga sun bude wuta sun kashe sama da mutane 20 nan take duk magoya bayan Elzakzaky. Madadin hukunci ya tsaya kan wadanda suka jawo fitinar sai ya zarce ga dukkan magoya baya wadanda duk inda aka gan su kan hanyar su ta zuwa Zariya sai a bude musu wuta ko a kama su kamar yadda aka kashe mataimakin Elzakzaky wato Sheikh Mahmud Turi kan hanyar Kano zuwa Zariya.

Ba a tsaya nan ba aka yi dirar mikiya a markazin Husainiyya da ke Zariya soja suka bude wuta suka kashe mutane sama da dubu, cikin har da yaran Malam guda uku da ke karatu a kasashen waje, shima Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zinatu aka raunatu su, aka kuma musu kaca kaca aka tsare su har yau kusan shekaru uku kenan. Hatta markazin aka ruguza aka mai da wajen fili kabjurburan iyayen sa da ke wannan wuri an ce sai da aka tone, aka rusa gidan da masallacin wasu magoya baya an ce da ran su aka yi ta tura su a cikin wuta, lamarin da ko wa mai bautar gunki bai dace a ce gwamnati ta yi wannan hukunci ba tare da an kai mutum kotu ba balle musulmi.

Kuma abin mamaki Buhari yana Kaduna wajen taron mawaka da suka taimaka masa yakin neman zabe amma bai tsawatar an kama mai laifi an gabatar a gaban kotu ba, duk da cewa sai da aka yi kusan kwana giyu ana gewaye da su a cikin gaidan ana tankiya.

Daga baya sun garzaya zuwa kotu don neman hakkin su kuma Alkalai sun tabbatar cewa an yi kuskure kan abin da aka musu don haka a saki wadanda aka tsare da malam Ibrahim da matarsa Zinatu a kuma biya su diyya a gina musu inda aka rushe, amma gwamnati ta ki bin umarnin kotu. Duk da irin ikirarin da ‘yan aware na Ibo su Namandi Kanu ke yi na fita daga Nijeriya da wagaza hadin kan kasa a gwagwarmayar neman kasar Biafra, amma gwamnati ta kama su kuma an bayar da belinsu harma sun fice sun bar kasar. Kuma na san cewa ko rantsuwa mutum ya yi ba zai yi kaffara ba ‘yan shi’ar da suka zabi Buhari saboda kishi sun fi mutanen Biafra yawa da magoya bayan Kanu yawa.

Sanin kowane wadannan mutane almajirai ne duk da cewa suna da banbancin akida da mutanen Nijeriya Ahlissunnah, amma kowa ya san ba a musu adalci ba, kuma a kullum suna ta rokon Allah don ganin bayan wannan gwamnati saboda haka zancen su sake zabar Buhari ba ya ajandar su, wadanda basa zabe daga cikin su yanzu sun himmatu suna ta karbar katin zabe bayan miyagun addu’o’in da suke na ganin an samu rugujewar gwamnatin ta kowane hali, kuma kowa ya sani Allah na amsar addu’ar wanda aka zalunta tun daga duniya kafin a je lahira.

Rukunin mutane na hudu sune ‘yan adawa masu sassaucin ra’ayi wadanda suka yi wake wake a lokacin zabe a sama su zabi Buhari a zaben gwamna da ’yan majalisu sun zabi magoya bayan su, amma suma basu sha da dadi ba saboda wadanda ke cikin APC suma kuka suke yi basu koshi ba balle su da suka yi anti party muhajirun da nufin rayuwar su ta inganta, amma yanzu matsaloli sun dabaibaye su wasun su har sun bar siyasar sun koma gefe sun gyara guri’un su suna jiran lokacin zabe 2019 su dauki fansa.

Rukuni na biyar sune ma’aikatan da suka rasa aikin su ta hanyar kora ko ragewa ko tantancewa ko ganin sun yi yawa ko ba a bukatar su a bakin aiki ko ta hanyar kora da hali su ajiye su kama gaban su da sauran nau’o’in ma’aikata da a halin yanzu suka rasa farcen susa.

Bayan haka wasu kuma sun yi ritaya tun lokacin PDP ana biyan su hakkokin su suna jira a zo kan su yanzu kuma an wayi gari a jihohi da kananan hukumomi gwamnoni sun kame kudin sun ki biyan su hakkokin su, yayin da hatta albashin da suke biya gani suke yi alfarma ce har suna sanya shi cikin nasarorin ayyuka da suka samu. Wasu kuma kamfanoni suke aiki da bankuna amma tsari irin na jari hujja ya sa an sallame su da nufin ana neman sabbin jini ne.

Wasu kamfanonin kuma sun karye saboda hauhawar farashin dala ko bashin banki ya tarnake su. Wasu kuma yawan neman kudin haraji daga hukumomi dabam dabam ya sa sun rufe kamfanonin bayan haka ga uwa uba rashin ciniki saboda karancin kudi a hannun mutane, suma irin wadannan mutane na san ba za su sake zabar wannan gwamnati ba kuma suna jiran lokacin zabe su dauki fansa ta bijirewa zabar APC.

Rukunin mutane na shida sune mazauna kan iyakokin Nijeriya inda ake da boda sama da dubu biyu amma rubutatta sune sama da dari bakwai, kuma kowa ya sani duk wanda ke zaune kan iyaka ko ta Amurka ce abincin sa na wurin ko ta hanyar yin fito ko ta hanyar saye da sayarwa, da kuma yin sumoga ta halartacciyar hanya ko haramtacciya. Tun daga zuwan wannan gwamnati ta rufe kan iyaka an daina walwala ba tare da tunani ko tsara yadda za a tallafi mutanen da ke kan iyaka ba, saboda kar rashi ko talauci ya kai su ga shiga miyagun hanyoyi na ta’addanci don neman abin da za su ci. Madadin a tsara rufe kan iyakar Nijeriya a karkashin wani shiri na shekaru da za a yi don tabbatar da manufofin, sai aka kawo su kwatsam aka rufe, don haka mazauna kan iyaka musamman matasa wasu sun kama fada da kwastam wasu kuma sun koma aikata laifu kamar su fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka. Iyayen su da iyalan su kuma suna gani rufe iyakar ya haddasa wannan matsala don haka sun gyara guri’un su duk suna jiran lokacin zabe su ramawa kura aniyarta.

Rukunin mutane na bakwai sun hada da ‘yan kasuwar da suka karye a cikin garuruwa manya da kanana wadanda ke ganin karancin kudi ya haifar da rashin ciniki yadda tun suna cin riba sun koma cin uwar kudi har sun koma cin dukiyar iyayen gida da abokan hulda wasu har sun kai ga sun rufe shagunan sun koma dauke yadda za ka ga mai jarin milyan goma ya sayar da shago bayan ya kare ya koma bulaguro ko yaro ga wani abokin hulda don ya samu yadda zai ciyar da iyalan sa, duk irin wadannan suna jiran lokacin zabe su dauki fansa wajen ganin kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba.

Rukunin mutane na takwas sune ‘yan sumoga da a baya ke tafiya da kudin mota daya ko biyu zuwa Kwatano su sayo mota su shigo da ita su biya kwastan su nemi abinci, yanzu an rufe shigo da motocin ta kan iyaka sai ta ruwa lamarin da ya sa ‘yan kudu suke walwala amma ‘yan arewa suka koma wahala. Wadannan mutane sun hada da masu sayo motocin da masu gyara ko fanalbitin ko fenti ko yin fito ko kiliyarans da makamantan su. A yanzu duk sun koma ‘yan kallo yadda gidan sayar da motocin da a baya za ka samu mota dari yanzu dakar ka samu talatin tsoffi, don haka duk masu ci ta wannan hanya basa tare da wannan gwamnati musamman ganin ‘yan arewan sune suka zabi gwamnatin ba mutanen legas ko Kalaba ko Potakwal ba.

An wayi gari mutanen da ke shigo da motoci ta ruwa an ninka kudin fito da gwamnati ke caji don haka sumoga ta karu a kan iyaka ta arewa kullum fada ake yi da jami’an tsaro da kwastam. Haka suma jami’an basa jin dadin irin artabun da ake yi saboda suma uwa ce ta haife su kullum rasa rayukan su suke yi a sanadiyyar dauki ba dadi da ‘yan sumoga saboda rashin iya tsara yadda lamarin zai tafi har mutane su saba an abko da wannan manufa ta rufe kan iyaka ce lokaci guda don haka mutane da dama sun fada cikin wahala da rashin sanin tudun dafawa suma yanzu sun shirya tsaf don kin zabar wannan gwamnati lokacin zabe mai zuwa.

Rukunin mutane na tara sune ‘yan kudanci masu kaunar zaman lafiya daganin an samu sauyi a Nijeriya don ingancin rayuwa amma sai suka ga akasin haka, yadda an wayi gari kamar yadda dan uwa ke tallafa wa dan uwa a arewa a kudancin Nijeriya lamarin da kamar wuya ba kowa ke yin hakan ba.

Don haka yanzu wahala ta musu yawa, musamman ganin yawanci dama basu yi Buhari ba sai kalilan albarkacin su Rotimi Amaechi da Bola Tinubu da Obasanjo da irin su Rochas Okorocha da su Adam Oshiemole da makamantan su. Yanzu kuma yawanci an raba gari da wasun su wasu kuma ana tafiya tare da su amma tafiyar babu dadi inda suke korafin sun kashe kudi don Buhari amma an wayi gari wasu basu samu komai ba in baicin wadanda suke jikin gwamnati ake tafiya da su.

Sanin kowane ‘yan kudu dama basu yi Buhari sosai ba an tattaro masu sassaucin ra’ayi ne, saboda hatta Lagos da ake da kusan mutane milyan uku da aka tantance guri’un su dakyar Buhari ya samu guri’a dubu dari shida daga Lagos, don haka a bana yadda suka ji a jikin su talauci ya rungume su harkoki basu garawa yadda suke so da wahala ace sun sake zaben Buhari a 2019 ko da kuwa zai sanya kuros a wuyan sa ya rataya littafin injila yana shiga coci don yin kamfen zai yi wahala ya samu guri’un rabin wadanda suka zabe shi a shekarar 2015 . “Yan arewan da ke fama da rikicin makiyaya da manoma da garkuwa da mutane da sauran gyauron boko haram sune gatar Buhari a siyasance ko a zamantakewa balle kuma a fannin addini da kabila duk an wayi gari yawanci ba a ci moriyar canjin ba.

Rukunin mutane na goma sune matasa da suka kasa suka tsare suka raka suka jira da tunanin idan gwamnati ta kafu kakar su ta yanke saka za su samu abin yi za su yi walwala, amma sai aka wayi gari duk inda ka je ofishin jami’an tsaro ko kotu ba wanda za ka samu cikin wahala sai matashi saboda basu da abin yi kuma basu da hakuri da talauci don haka nema suke yi su rayu ta kowane hali kuma cikin jin dadi.

Lamarin da ya sa zukatan su suka gurbata yayin da wasu bata gari ke amfani da su wajen yin ta’addanci. Wasu kuma da suka yi karatu sun rasa aikin yi yadda an kai matsayin da kusan milyan biyu ke gama NYSC a duk shekara amma ba wani shiri na basu aiki sai N-power wanda har yau bamu taba ganin dan minister ko gwamna ya cika N-powar ba sai aiki a manyan ma’aikatu ko fita kasashen waje. Wani abin takaici kuma shine yadda babban mutum da ke cikin gwamnati da ya motsa sai ya razana matasa da cewa kar su yi karatu da tunanin za a basu aiki don haka su dogara da kan su wajen sana’a.

An wayi gari sun koma kan sana’ar tura kurar sayar da kaya ba ciniki suna kasa kaya a bakin hanya ba ciniki, idan sun dauka a kan su suna yawo ‘yan ruwa ruwa na gwamnati sun kame su a zuba kayan a mota su tafi da su duk ciniki da suka yi a kwace haka kayan da kyar za su ceci kan su su kubuta, anya wannan kasa ana son gaskiya? Wallahi idan amarya bata hau doke ba bai kamata a dora mata dutsen nika bag ammo ba. Kuma wadannan matasa za su ci gaba da zuba ido suna kallon dukiya na gilmayya a tsakanin wasu mutane kalilan da iyalan su masu mulkin alhali matasan sune suka yi gwagwarmayar kawo wannan gwamnati, daga karshe ta zamo kura da shan bugu gardi da amshe kudi.

To an ce kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba bayan haka kuma kowa yayi na gari don kansa, talakawa suna nan suna jiran masu jiniya su koma kauyukan su domin neman goyon bayan jama’a don su sake zabar APC, saboda tun daga yanzu sun ga yadda idan sun je taron biki ko daurin aure a ke bin su da ihu an ace barayi, lamarin ba dadi mutane har sun zamo basa tsoron gwamnati ko masu mulki, wadamda le cewa suna son APC kuma su na yi ne da nufin ko za su samu wani abu, amma idan tafiya ta kare suka ji wayam za su sake layine su bi siyasar masu zub da ruwa don a taka danshi da fatar Allah ya kawo mana mafita cikin wannan lamari yasa a yi zaben a gama lafiya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!