Gwamnatin Badaru Na Kyautatawa Ci Gaban Matasan Jihar Jigawa –Alhaji Salisu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Gwamnatin Badaru Na Kyautatawa Ci Gaban Matasan Jihar Jigawa –Alhaji Salisu

Published

on


An bayyana cewa a duk kasarnan ba inda ake kyautatawa ci gaban matasa kamar jihar jigawa bisa lura da irin dinbin gudummuwa da suka bayar wajen kawo canji a kasarnan lokacin zabenda ya gabata. Mashawarci na musamman ga Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa akan ci gaban matasa. Alhaji Salisu Rabiu ya bayyana haka da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau a Kano.

Ya ce Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Alhaji Badaru Abubakar Talamiz tana karfafawa matasan jihar gwiwa ta sun rungumar harkar noma sosai dan dogaro dakai. kasancewar  Jigawa  jiha ce ta noma wanda kusan duk al’ummarta manomane don haka gwamnatin Badaru take bada tallafi ga matasa dan bunkasa noma ta samarda kayayyakin aiki da sama musu kasuwa ta yanda zasu rika anfana da ribar noman.

Mataimaki na musamman ga Badaru kan ci gaban Matasa ya ce a kalla akwai matasa samada 8,000 da aka koya musu sana’oi a fannoni daban-daban aka basu jari da suka kafa sana’a.

Ya yi nuni da cewa yanzu a jihar Jigawa babu wani matashi dake zaman banza don haka nema sukeda zaman lafiya fiyeda kowace jiha a fadin kasarnan.

Ya ce Gwamna Badaru yana zuwa ya samowa matasa aiki a matakin hukumomin Gwamnatin tarayya da suka hada da aikin Jami’an shige da fice dana hana fasa kwauri dana dansanda da soja da sauran hukumomi da dama.

Alhaji Salisu Rabiu ya ce Jigawa ta rabauta da hazikin Gwamna da yake da kishin son ci gaban matasa don haka yayi kira ga al’umma da matasan jihar jigawa su ci gaba da bai wa Gwamnatin Badaru Abubakar hadin kai musamman ma a zabe mai zuwa na dan dorawa akan ayyukan ci gaba na gina jihar Jigawa da yake yi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!