Connect with us

LABARAI

Uwargidan Gwamnan Katsina Ta Hori Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Kan Ayyukansu

Published

on

Uwar gidan gwamnan Jihar Katsina Hajiya Binta Aminu Bello Masari, ta hori kungiyoyi masu zaman kansu da gidauniyoyi, da su kara fadada ayyukansu don kara samar da tarbiyya a tsakanin al’umma.

Hajiya Binta Masari ta yi wannan horon ne a lokacin da ta karbi bakuncin jami’an gidauniyar horas da sana’o’in hannu ta marigayi M.D Yusuf a wata ziyarar ban girma a Katsina. Uwargidan gwamnan ta ce, baya ga horas da sana’o’in hannu a cikin al’umma don su zamo masu dogaro da kai, gidauniyar na da rawa muhimmiya wajen ingangta tarbiyyar matasa.

Hajiya Binta Masari, ta ce tabarbarewar tarbiyya a kasar nan, da ya hada da she-shayen miyagun kwayoyi, da sauran ayyuka n assha a tsakanin matasa, ya zamo wani abin dubawa da idon basira.

Ta kuma gargadi iyaye da su rika kula da daukar nauyin ‘ya’yansu, da zai hana su yawon barace-barace akan tituna. Hajiya Binta Masari, gta sha alwashin hada kai da gidauniyar MD Yusuf don cigaba da kyautata wa al’umma, har ma ta kara da cewa, a kodayaushe kofarta a bude take wajen taimakawa cibiyoyin horas da sana’o’i.

Ta yi kira ga gidauniyar, da ta yi iya yinta don ganin ta dora al’umma a hanya mai bulewa. Tun farko, jami’in dake kula da cibiyar Mal. Danjuma Muh’d yace sunkai ziyarar ne don shidawa uwargidan gwamna irin ayyukan da cibiyar ke gudanarwa, kamar yadda yace, cibiyar na aiwatar da horas da sana’o’i irin su dinki da kuma hada guiwa da ofishin hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wajen kai rahoton masu aikata laifuka.

Sai ya roki taimakon uwargidan gwamnan na su hada hanu da cibiyar don tallafawa masu karamin karfi. Jami’in da ke kula da gidauniyar ya kuma yaba wa gwamnatin Aminu Bello Masari, da take bullo da tsare-tsaren horas da mata da matasa sana’o’i.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!