Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Nau’o’i Da Salailan Fassara A Idon Masana Da Manazarta

Published

on


An tsamo wannan makala ce daga kundin nan na  Champion Of Hausa cikin Hausa, wanda Sashin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka ya tattara domin karrama Farfesa Dalhatu Muhammad Na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a matsayin kadan daga cikin irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa ilimi.

 

Gabatarwa

Fassara dangantaka ce ta cudanya tsakanin harsuna wadda ta samu asali daga rarrabuwar al’umma kabilu daban-daban da kuma bukatuwa tsakanin kabilun. Masana da masu nazari daban-daban sun bayyana ma’anar fassara. Wadannan sun hada da Dabid (1992:344), da Lebchner (2006:12) da Eftikhari (2008:2) da sarbi (2008:1) da sauransu da dama. Amma a dunkule kuma cikin Hausa, fassara tana nufin mayar da ma’anar abin da aka fada daga wani harshe zuwa wani (sarbi 2008:1).

Fannin fassara fanni ne mai tsohon tarihi ta fuskar aiwatarwa, amma sabon fanni ne ta fuskar nazari, amfaninsa ba sabo ba ne a tsakanin kabilu daban-daban. Ko shakka babu, fassara ta taka kuma tana kan taka muhimmiyar tawa wajen ci gaban al’ummun duniya ta fannoni da dama da suka hada da bunkasa addini da ci gaban kimiyya da fasaha da bunkasar harshe da adabi da fannin sadarwa, kai har ma da bunkasa aikin yi da kuma samar da ma’aikata da sauransu (Sarbi 2011:1).

Ganin irin rawar da fassara take takawa a fadin duniya da sauransu dalilai, masana da masu Nazari suka yi ta kokarin samar da ingantattun ra’o’i da za su taimaka wajen cim ma  manufofin fassara. A irin wannan gwagwarmaya, masana sun fito da rabe-raben fassara da salailai, domin ganin kwàlliya ta biya kudin sabulu. To sai dai da take fahimta fuskar ce, ana samun ‘yan bambance-bambance. Abin da wasu suke kàllo a matsayin nau’in fassara (type of translation), wasu suna daukarsa a salon fassara (translation method/procedure) ko ma wata dabara ta magance matsalar rashin takwara/abokin burmi.

Saboda haka babbar manufar takardar ita ce, a tantance matsayin nau’o’in fàssara da kuma salailanta. An tattauna a kan kowanne salo dangane da yadda yake da amfaninsa da kuma cikas dinsa idan akwai cikas dinsa.To sai dai kafin a yi hakan an fara tattaunawa a kan nau’o’in fassara kamar yadda muke kallon su a fagen ilimi.

 

  • Nau’o’in Fassara

Dangane da nau’o’in fassara, Simpson (1981:137) ya kafa hujja da Jacobson (1959) cewa: Akwai nau’o’in fassara guda uku. nau’i na farko shi ne, wadda take kunshe da harshe daya a matsayin tushen fassara kuma harshen fassara (interlingual translation). Abin nufi a nan shi ne, a wannan nau’in fassara ana bayyana ma’anar sakon da yake tushen fassara da wasu kalmomin daban na tushen fassara din. Misali, Kano is just a stone through from here. Idan za a yi amfani da irin wannan nau’in fassara, wannan magana za ta zamo Lamar haka: Kano is not far away from here, ko Kano is bery close from here. Haka ma a Hausa idan an ce: Mai hannu da shuni ake ba murjin zare. Ana nufin: Da mai akwai/wadata ake yin shawara ko shawarar mai akwai/kudi ake dauka. Simpson(1981:137) ya kawo Steiner (1985) yana cewa: Nau’in fassara ne da take tallafawa wajen fahimta da kuma isar da sako.(fassara).

Nau’in fassara na biyu shi ne Wanda ya kunshi harsuna biyu (interlingual translation), wato tushen fassara ( mai kunshe da sako na asali) da kuma harshen fassara ( harshen da ake mayar da ma’anar sakon asali cikinsa). Misali Kano is a Stone throw from here, a matsayin tushen fassara. Wannan sako zai koma harshen fassara kamar haka: Daga nan Kano ba nisa.

Nau’o’in fassara na uku shi ne Wanda ya kunshi bayyana ma’anar Alamomi ta.hanyar amfani da kalmomin harshen fassara (semiotic translation). Wannan nau’in fassara tana hada har da bayyana ma’anar; ma’anar kurame da kuma irin fitulin da ake amfani da su a mahàdar tituna domin bayar da hannu. Misali, koriyar fitila/wuta tana nufin a wuce. Rawaya kuma tana nufin a yi taka-tsan-tsan, wato kashedi. Ita kuma ja tana nufin a tsaya ( akwai hadari idan an wuce). A irin wannan nau’in fassara, har Ila yau, ana iya mayar da ma’anar ma’anar da aka yi da wani harshe zuwa alamomi. Sai dai ya kamata a lura cewa, yadda ake sanin alamomi a harshe haka ma ake sanin alamomi kamar yadda idan mutum bai San kalma ba, ba zai San sakon da take isarwa ba, haka ma idan ba a San alama ba, to ba za a San ma’anar da take wakilta ba. Me nan wajen yin amfani da alamomi, tilas ne a yi amfani da wadanda mutane suka sani kuma ta yadda suka San su( babu jirkitawa ko sauya kamanni) Misali idan hukumar kasa da gidaje ta sa alamar da D a jikin bango ko gida, wannan alama tana nuna an dakatar da ginin wannan gida.

To amma idan hukumar ta yi alamar T a kalla akwai kokonton abin da ake nufin, saboda alamar ba irin daya ba ce da ta farko. Saboda haka, sakon da take isarwa zai bambanta da na alamar farko. Wannan bayani tana nuna mana cewa, za a iya mayar da ma’anar alamomi cikin kalmomin harshe kamar yadda ake daukar tunanin dan’adam da take wakiltar kalmomin da Wanda ya San su zai iya fassarawa. Simpson (1981) ya kara fayyacewa: alamomi za su iya kasancewa a tushen fassara (fassara dalamomin zuwa kalmomin wani harshe) ko harshen fassara (fassara kalmomin wani harshe zuwa alamomin wani harshen), ko kuma suka biyun (fassara alamomi ko kalmomin wani harshe zuwa kalmomin ko alamomin wannan harshe kowannensu. Dangane da wannan nau’in Simpson ( 1981) ya dogara da Tweney (1973) da kuma Hoemann (1976) a matsayin wadanda suka fayyace wannan na fassarar alamomi dalla-dalla.

yayin da wasu masana suke kallon nau’o’in fassara ta fuskoki uku, wasu kuwa na kallon lamarin ne ta fuskoki biyu. Kuma wadansu fuskokin sun sha bamban da na farko. ken an ana kasa fassara kasha biyu.

Kashi na farko shi ne na fassara nan take, nau’in da Simpson(1981:137) ya kira oral interpretation, simultaneous and consecutibe translation, kuma sunan da aka lakaba wa salon fassara da ake kira literal translation maimakon fassara kai tsaye. a irin wannan nau’in na fassara  mai isar da sako a tushen fassara yana magana kuma mai fassara (bayar da ma’ana) cikin harshen fassara yana yi a lokaci guda. Ko kuma mai fassara ya karanto rubutaccen sakon da yake cikin tushen fassara, sannan ya mayar da ma’anar cikin harshen fassara  a lokaci daya.

irin wannan nau’in fassara yana da wahala kwarai da gaske. Saboda mai fassara ba shi da cikakkiyar dama ko lokaci na yin tunani mai zurfi, musamman dangane da zabar  kalmomi da jimloli da kuma salon da ya fi dacewa. bugu da kari mai fassara ba shi da lokacin tantancewa da kuma yin la’akari da abubuwan lura yayin fassara. Idan kuma aka samu rauni, ko matsala awani bangare, to ana iya sauya ma’anar sako na asali. Yin haka kuwa tankwabawace a aikin  fassara. wannan yana nuna cewa,. wannan yana nuna cewa, tilas ne mai fassara ya mallaki dukkan rukunonin fassara da suke kunshe cikin Sarbi (2005 da 2008) kamar haka kwarewa a harsunan da fassara ta shafa: sanin al’adun batun fassara: samun horo a aikin fassara; hakuri da juriya. za mu tsaya a nan, sai mako na gaba da yardar Allah za mu ci gaba daga inda muka tsaya,

 

Advertisement
Click to comment

labarai