Kowa Na Da Gudummawar Da Zai Bayar Wajen Ci gaba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Kowa Na Da Gudummawar Da Zai Bayar Wajen Ci gaba

Published

on


Idan kowa yana  yin abin da ya dace tun daga shi kansa, sai kuma sauran mutanen da suke karkashinsa, a ce ana yin haka wato duk hakkokin da ya kamata ya yi ya kasance yana yi, ai tuni  da an yi nisa da kuma samun gaggarumin ci gaban da kowa zai yi sha’awa da kuma alfahari da shi. Wannan ma na magidanci daya ne don haka idan abin ya kasance a na yin duk abubuwan da suka dace sai unguwa ta inganta, in ya kasance haka ashe ke nan da babu wasu matsalolin da ake fuskanta da suka yi kama da na yanzu. Kamar jinka idan ana bukatar a dora bisa tafarfara, ai mutane ke tashi su kama har a samu dora ita jinkar. Hakanan shi ma cigaba bai samuwa sai kowa ya bada hadin kai da kuma gudunmawa, ba wai ya tsaya daga wani wuri ba, ya rika cewar masu kokarin yin wani abin da zai kawo ci gaba ba su iya ba, shi kuma din da yake ganin ya iya, bai da wata katabus.

Maganar tafiyar da Nijeriya da kuma wasu abubuwan da zasu kawo ci gabanta hakkin kowa ne, ba wai sai wani ya tsaya yana hangen na wani ba, bayan shi kuma bai na shin ba, wanda abin da ya kamata ke nan. Kowa yana da abin da ya dace amma sai yaki yana hangen na wani can , yana cewa ai bai dace ba, saboda dama ai laifi ance tudu ne taka naka  ka hango na wani.

Idan kowa yana yin abin da ya dace da shi tun daga ciki har waje ai da tuni zuwa yanzu halin da muke ciki ba wanda zai ji haushin wani dangane da wani abu can daban.

Ita kasar Nijeriya duk ta kunshi dukkan abubuwan da mutum yake tsammani, a matsayinta na uwa da uba wadda ta haifi manyan ‘ya’ya  har ma da jikoki, wadanda za a ce a shekarunta da suka kusa kai hamsin da takwas kamata ya yi, yanzu sai dai ta zauna, a rika yi mata abubuwa.  Maimakon haka sai aka samu rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yanta, aka koma ana yin zaman ‘yan marina wato kowa da inda yasa gabansa, duk wannan ma ba wani abu bane idan dai har daga karshe za a tuna cewar da akwai fa abubuwan da suka kamata ayi.  Ba wani cigaban da za a samu musamman idan rarrabuwar kai ta yi kamari, ya zama ruwan dare gama duniya. Duk ba ayin hakan musamman ma idan aka yi la’akari da yadda ita Nijeriya ta kasance cikin nan dumi can zafi, wani wurin kuma wuta  c e ke  ci bal- bal, wannan sai mutum ya tuna da yadda ake shekarun baya da suka wuce. Kara samun rarrabuwar kan da ake samu ku san wannan  ana iya cewar duk rana ce, wanda hakan ya sa ba a fadawa wa juna gaskiya,  bare ma har akai ga ma yin tunanin ya fa kamata a yi abubuwan da zasu kawo cigaba na ko ina ne ma ake tun daga unguwa har akai zuwa babban birnin tarayya.

Ci gaba ai zai  yi wuya da kuma nisa da al’umma muddin dai har ya zuwa wannan lokaci da ake ciki, akwai miji mai cutar matarsa, haka ita ma matar da akwai mai yiwa mijinta hakan. Da yana zaluntar mahaifinsa, shi ma mahaifin sai ya kasance wani yana yin haka. Mahukunta su rika cutar talakawa, suma idan sun samu damar ba bari zasu yi ba, shugaba ya rika cutar na kasa da shi, hakanan suma idan sun samu damar sai sun yi sama da shi daganan su sako shi kasa su taka. ‘Yan kwangila wasu suna yin kashe mu raba da wadanda suka basu ita kwangilar, ana aikata ayyukan ashsha muraran a fili babu ko tsoron Allah, wani lokaci ma har wanda ya aikata abin zai fito yana bayyanawa mutane ai shi ne ya aikata abu kaza da kaza. Babu ko kunya babu tsoron Allah. Ta yaya za a cigaba bayan akwai wuraren da ake ba Fasikai muhimmanci, mummunai su kasance ba a ganin mutuncinsu. Wasu ‘ya’ya yanzu su suke neman maye gurbin Iyaye, su Iyayen wasu kuma yanzu sune suka koma makwafin ‘ya’ya.

Kamar yadda aka fara shimfida tabarma da cewar shi cigaba kowa yana da gudunmawar da zai bada, wannan abu haka yake, sai kowa ya san matsayinsa da kuma duk wasu abubuwan da suka kamata ya yi. Amma ba yadda ake kara zube ba sai an canza alkibla, bayan nan a tuba kuma tubar ta kasance ba irin ta mazuru ba, ana iya yin sa’a ta hakan saboda ko da ace shi cigaba yana tafiya da kan shi domin zuwa wuraren da ya dace, to akwai fa wurare masu yawa da ba zai ko mafarkin zuwa ba.

Gaskiyar al’amari an yi nisa da cigaba saboda kuwa duk ya gane ashe, bamu ma son junanmu, kwarai kuwa domin an yi nisa da gida kwarai da gaske. Bugu da kari kuma ga rarrabuwar kai wadda ke faruwa tsakanin ko wane jinsi, don an yi nisa da irin tafarkin so da kaunar juna wanda aka gina mu da shi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!