Connect with us

KASUWANCI

CBN Ya Roki ’Yan Nijeriya Su Rika Mutunta Naira

Published

on

 

Babban Bankin Kasa (CBN) ya zargi bankunan kasuwanci dake kasar akan yiwa bankin zakon kasa akan kokarin sa na canza kudaden takarda da suka lalace da sababbi.

Daraktan riko na sasashen bayanai na CBN Mista Isaac Okorafor ne ya bayyana hakan a jihar Legas a. Okoroafor yana mayar da martani ne akan korafin da ‘yan Nijeriya suke yi akan lala cewar kudaden takardu a kasar nan.

Ya ce, bankin yana sane da hakan kuma ya dauki mataikan da suka dace don magance matsalar a kasar nan. A cewar sa, daya daga cikin matankan da bankin ya dauka shine don kwashe kudaden takardun da suka lalace da kuma rage canjin da CBN yake yiwa bankunan kasuwanci na ware takardun kudaden da suka lalace daga naira 12,000 zuwa naira 1,000 na ko wanne akwati.

Okorafor  ya ci gaba da cewa, ragin da aka yiwa bankunan zai kai har tsawon wataanni uku daga biyu ga  watan Janairu zuwa ranar ashirn da takwas ga watan Maris. Ya bayyana cewar wannan damar an iyakance ta ne akan naira hamsin da naira ashirin da kuma naira goma.

Mafi yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna bakincikin su akan yadda kudaden takardun da suke yawo a cikin alumma, inda sauran kudaden takardar suka hada da; naira biyar da naira goma da naira ashirin da naira hamsin da kuma naira dari. Ya bayyana cewar, CBN ya kuma dauki wata dabarar ta janye kudaden da suka lalace da suke  yawo a cikin alumma mai makon dogaro akan bankunan kasuwancin dake kasar nan.Okorafor ya kara da cewa, CBN ya fara yin amfani da kungiyoyi ‘yan kasuwa don wayarwa da ‘yan kasuwa kai akan canza kuaden da suka lalace da sababbi.

A cewarsa, tuni CBN ya kai wannan sabon tsarin zuwa jihohin   Kano, daKaduna  Abuja kuma za a kai sabon tsarin zuwa kuancin kasar na.

A karshe Okorafor ya roki ‘yan Nijeriya dasu rika kula da kudaden kasar nan su kuma rika girmama darjar da kudaden keda dashi kazalika, ‘yan Nijeriya su hakikance akan a basu lafiyayyun takardun kudi daga bankuna mai makon wadanda suka ji jiki.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!