Kungiyoyin Matasa 12 Ke Goyon Bayan Takaran Ibrahim DanKwambo A Lardin Zazzau —Musa Gambo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Kungiyoyin Matasa 12 Ke Goyon Bayan Takaran Ibrahim DanKwambo A Lardin Zazzau —Musa Gambo

Published

on


 

An bayana cewa, gamayyar kungiyoyin matasa 12 ne dake lardin Zazzau a cikin jihar Kaduna suka mika bukatarsu na neman gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwanbo ya fito takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da za a gudanar a shekarar 2019, domin imanin da suka yi na cewa, shi ne kadai dan siyasan da zai iya kawo wa kasar nan ci gaban da ake bukatar a wannan lokaci da dukkan bangarorin rayuwar ‘yan Nijeriya ke fuskantar kalubale na musamman. Shugaban kungiyoyin makaranrun Islamiyoyi masu bin darikun sufaye na jihar Kaduna, ALHAJI MUSA GAMBO ZARIYA ya tattauna da wakilinmu BELLO HAMZA a kan dalilinsu na bukatar takarar gwamna Ibrahim Dankwambo da kuma yadda suke fatan cimma wannan manufa nasu, ga dai yadda hirar ta kasance. Zamu so ka gabatar wad a masu karatunmu sunan ka.

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, suna na Musa Gambo daga unguwan Rimin Kambari a cikin birnin Zariya City.

 

Alhaji kuna ta fafutukan ganin mai girma gwamnan jihar Gombe Ibrahin Hassan Dan Kwambo ya fito takaran shugabancin kasar nan, zuwa yanzu ya yanayin hakan na ku ya ke?

Lallai hakar mu ta kusa cimma ruwa ko ma in ce ta cimma ruwa, domin kiran da muke ta yi a kan Ibrahim Dan Kwambo Gwamnan jihar Gombe kuma Talban Gwambe ya fito takaran shugabancin kasar nan muna da kungiyoyi da dama wandanda suna karkashinmu wanda kuma ko wancan zaben da aka yi an yi amfani da mu kuma muka yi muka tankwara mabiyanmu a tafiyan kungiyoyi wanda mu a tafiyan kungiyoyi kuma suka amsa mana sakamakon alkawura da suka yi mana suka yi wa talakawan kasa lallai kam sai muna tunanin ko mulkin nasu zai kasance abin da suka fadi haka zuciyarsu take amma sakamkon akasin haka muka dauki kudirin a zukatan mu yanzu kam ba mu yarda ba sai da muka bi sawu muka ga waye zai zaman mana alkairi sai muka ga talban Gombe Ibrahim Hassan Dan Kwambo shi ne zai zama mana alhairi shi ya sa muke kira ga Ibrahim Hassan Dan Kwambo ya gaggauta bayyanar da kansa domin tsayawa takarar shigaban kasar nan.

 

Wani Shirri kuke das hi kuma?

A kan haka mun umarci wadanda suke biye da mu domin muna yi masu jagoranci bisa kyautatawa bamu cin amanar su shi ya sa suke biye damu kuma su wadannan mutane shi yasa mun tara mabiyan mu a kungiyoyi muka ce, ku zo ku taimaki mutanen nan sun ce zasu taimaki talakawa ga halin da ake ciki ga kashe-kashe ga kaza sai abu ya karu. Yanzu ka ji abinda ke afkuwa a Birnin Gwari, abin da ke afkuwa a Zamfara abin da ake cewa an kawo karshen shi a shiyyan su Maiduguri, Yobe da Adamawa gashi ya dawo kuma idan suka tashi magana babu magana mai dadi babu wani tausayawa, shi ya sa muka ce lallai kam mu zo mu yi Ibrahim Dan Kwambo Talban Gombe domin muna da tabbaci yadda ya rike jihkr Gombe da adalci, misali ka ga kungiyan kwadago  da suka tashi taro ina suka je? sai  suka je jihar Gombe domin shi ne Gwamnan da  yake sauraron koke ya ke sauraron talakawa. Suka kai koke kuma nan take Gwamnan jihar Gombe ya amsa masu abin da suke so na a kyautatawa talakawa domin talaka yau in aka ce albashi yayi kyau lallai talaka zai ji dadi zai dara, dan kasuwa zai samu ciniki manomi zai samu kayan noma amma daga lokacin da an karanta albashi lallai kam kasa ana cikin wani hali. Kuma Ibrahim Hassan Dan Kwambo idan sauran jihohi suna cewa babu kudi shi rijiyan kudi yake da shi? Kyautatawa ne da tausayi dan haka lallai Ibrahim Hassan Dan Kwambo shi ya cancanta ya zama shugaban kasa a Nijeriya, gashi matashi ba kamar irin wadannan gwamnatocin da mu matasa muka taimakesu suka kai gaci domin tsoho ba abin da zai yi amma sai ga tukuicin da suka yi mana har suna cema matasa cima zaune, mun ji matasan Nijeriya cima zaune ne amma kar su manta sun yi alkawari kafin su kai gaci in sun kai gaci sun ce zasu samar da ayyukan yi zasu samar da kamfanoni. Ayyaukan yi nawa suka samar a yanzu kamfanoni nawa suka tayar yanzu ko a nan jihar Kaduna cikin kamfanonin nan da suka durkushe har yau babu kamfani daya da aka tayar sai ma kokarin korar wasu ma’aikata a raba su da hanyar abincin su wanda gasu nan suna cikin lahaulu walakuwwata wanda gashinan ba koro ya ke yi ba kara ma’aikata ya ke yi da noma, yau mutane sun ce talakawa a yi noma talakawa an yi noma amma baya daraja a kasuwa kai an sayar maka da taki da tsada amma ba a zo an sayi abincin ka da daraja ba amma mutanen waje su zo su sayi kayan abincin ku to ya suke so su yi da mutane? ‘Yar manuniyar mu ta nuna kuma madubin mu ya nuno mana lallai Ibrahim Dan Kwambo shi ya cancanta ya zama shugaban kasa a Nijeriya, kuma Ibrahim Dan Kwambo mutum ne adali wanda ba ya nuna banbancin  kabilanci ko banbancin addini kuma a mulkinsa a mulkin jihar Gombe bai jawo ‘yan uwansa ya ce, duk ku zo a’a kowanne bangare an sa su a gwamnati ba irin gwamnatin da suka jawo ‘yan uwansu na jini suka kewayesu suna abin da suka ga dama ba, kamar ba al’umma suke mulki ba.

 

Su kungiyoyin nan naku sun takaita ga jihohin arewacin kasar nan ne ko kuna da reshe na kungiyoyi masu hankoron ganin Dan Kwambo ya zama shugaban kasa a sauran sassan kasar nan?

Alhamdulillahi, akwai kungiyoyi na addinai wanda su muke jagoranta wanda kamar nine mai maganar nan ina daya daga cikin shugaban kungiykr makarantun Islamiyya mabiya darikun Sufaye wanda ni ciyaman ne a kungiyan kuma lallai mun yi amfani da daluban mu muka sa kowanne suka je suka yi katin zabe, a cikin garin Zariya muna da dalubai wadanda suka isa jefa kuri’a sun fi dubu dari biyu kuma ai dama shugabancin namu ba ya tsaya cikin garin Zariya bane, don haka kuma akwai kungiyoyi wanda yanzu haka muke rokon su don Ibrahim Dan Kwambo ya fito takara, akwai kungiyoyi da dama wanda akwai S.A dinsa Alhaji Abdullahi Babayo wanda ma shaida ne, domin ya zo ya jagoranci zama a nan cikin karamar hukumar Zariya ya jagoranci zama wajen kashi uku ya ga matasa yadda suke hankoron Ibrahim Hassan Dan Kwambo wasu suna cewa ko kudi ake bayar wa muka ce wallahi Ibrahim Hassan Dan Kwambo ba a taba ido biyu ba da shi bare a karbi kudi mu muna wannan na kishi ne domin mu ga yaya za a yi mu ceto kasar mu daga halin da ake ciki mu kori yunwa mu kori kashe-kashen mutane, mu kori talauta ‘yan kasuwa, mu kori rashin samar da ayyukan yi domin gwamnatin Ibrahim Hassan Dan Kwambo ta samar da ayyukan yi.  Mu yanzu mun aje batun wani jam’iyya, ba ,maganar jam’iyya ake yi ba mutum ake yi, Ibrahim Hassan Dan Kwambo ko a wanne jam’iyya arty ya ke ba PDP ba za mu bi shi, kuma za mu sa a bi shi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!