Connect with us

KASASHEN WAJE

Za A Samu Mutuwar Yara Kanana A Kasar Kongo

Published

on

 

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Duniya UNICEF, ya ce yara fiye da 400,000 suna fuskantar hadarin rasa rayukansu a dalilin tsananin yunwa, muddin ba’a dauki matakai na gagawa ba.

Asusun na UNICEF ya dora alhakin gagarumar matsalar a kan kazamin yakin da ake gwabzawa tsakanin sojin kasar ta Jamhuriyar da kuma ‘yan tawaye a lardin Kasai.

Majalisar dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mutane miliyan daya da dubu dari uku ne suka tsere daga yankin na Kasai tun bayan fara wannan yaki a watan Agustan shekarar 2016.

Rahoton majalisar ya ce dubban iyalan da suke tserewa gidajensu a halin yanzu na fama da rashin isasshen abinci da ruwa, dalilin da ya jefa su cikin munin yanayi.

Jimillar yaran da ke fama da rashin samun abinci mai gina jiki sun kai 770,000, daga cikinsu ne kuma 400,000 ke fuskantar hadarin hallaka muddin basu samu taimakon gaggawa ba.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: