Connect with us

LABARAI

Mun Kwato Tiriliyoyin Naira Daga Barayi –Buhari

Published

on

A jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tun daga darewarsa karagar mulki a shekarar 2015 zuwa yau, ya cimma nasarar kwato Tiriliyoyin Naira daga barayin Gwamnati.

Haka kuma Shugaban ya aminta cewa yaki da cin hanci da rashawa ba abu bane mai sauki, domin annobar ta yi rassa a dukkanin fannonin rayuwa.

Shugaban ya yi watsi da zargin da ke cewa, gwamnatinsa na bibiyar wadanda ba su tare da shi ne kawai a lamarin yaki da rashawan da take yi.

Shugaba Buhari ya bayyana wadannan kalamai ne a jawabin da ya gabatar yayin bude sabuwar hedikwatar Hukumar EFCC wanda ke da matsuguni a Jabi dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa a karkashin gwamnatinsa ‘yan Nijeriya sun gamsu cewa duk wani ma’aikaci ko jami’in da ba shi da gaskiya sai ya shiga hannu, komi jimawa kuwa.

Ya ce, a tsawon rayuwarshi ya muhimmanta lamarin yaki da cin hanci da rashawa fiye da komi.

“Wannan wani sabon faife ne aka bude a yaki da cin hanci da rashawa.

“Tun bayan hawa na kan karagar mulki a shekarar 2015 nake fatattakar rashawa, ba tare da wani rangwame ba.

“Daga shekarar ta 2015 zuwa yau mun cimma nasarori masu yawan gaske a yaki da cin hanci da rashawa. ta yadda kowa ya aminta da kokarinmu. Mun cimma nasarar kwato tiriliyoyin naira daga hannun barayin gwamnati.” inji shi
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: