Connect with us

WASANNI

Chelsea Za Ta Iya Siyar Da Hazard

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na iya sayar da Eden Hazard don ta samu kudaden sayen sabbin ‘yan wasa, a cewar Stebe Clarke tsohon mataimakin mai koyar da kungiyar.

Hazard mai shekara 27 shi ne ya taimaka wa Chelsea daukar kofin FA a Wembley a ranar Asabar bayan da ya zura kwallo a bugun fanariti a ragar Manchester United inda aka tashi 1-0.

Chelsea ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba kaka mai zuwa bayan kammala gasar firimiya tana matsayi na shida a tebur.

Tsohon mataimakin mai koyar da kungiyar Stebe Clarke ya ce dole Chelsea na bukatar zubin sabbin ‘yan wasa domin dawowa hayya cin tad a kuma matsayinta na da.

Mista Clarke ya ce abu mai yiyuwa ne Hazard ya bar Chelsea idan an bude kasuwar musayar ‘yan wasa.

Shekaru biyu suka rage yarjejeniyar Hazard ta kawo karshe da Chelsea sai dai har yanzu Hazard bai sake sabon kwantaragi ba a kungiyar kuma tuni kungiyar Real Madrid tafara zawarcin dan wasan.

A shekarar 2012 ne Chelsea ta dauko Hazard daga Lille ta kasar Faransa dan wasan na Belgium ya karbi kyautar gwarzon dan wasan Ingila a shekarar 2015 da ya lashe kofin firimiya.

Tuni mai tsaron ragar kungiyar ta Chelsea Thibaut Courtois ya bukaci shugabannin kungiyar  su yi zubin sabbin ‘yan wasa idan har kungiyar tanason cigaba da zama a sama a gasar firimiya da nahiyar turai gaba daya.

Akwai yiyuwar mai saron ragar dan kasar Belgium zai bar Chelsea idan kwangilar shi ta kawo karshe da ungiyar kuma kungiyar Real Madrid tana zawarcinsa.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: