Connect with us

LABARAI

Olisa Metuh Ya Kwashi Jiki Ya Fadi A Kotu

Published

on

Tsohon Sakataren Watsa Labarai na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Olisa Metuh ya kwashi jiki ya fadi rinjim a babban kotu a Abuja lokacin da ke gaban kotu domin ci gaba da sauraron karar da aka maka sa.

Ya kwashi jikin ya fadi ne a lokacin da ke kokarin shiga zuwa ga katankar tsayuwar masu laifi da ke cikin kotun.

Olisa Metuh dai ya kasance a gaban kotun ne a bisa zarginsa da aka yi kan wasu kudade da suka kai miliyan dari hudu (N400million) kadaden wacce ake zargin da hadaka da tsohon mai bayar da shawara kan hidimar tsaro Kanal Sambo Dasuki (Mai ritaya).

Olisa ya kwashi jikin ya fadi ne da misalin karfe tara da minti daya na safiyar Jiya Litinin (9.01am) a lokacin da ke cikin dakin kotun.

Metuh, wanda yake gurfane a gaban Alkalin Justice Okon Abang.

Alkalin ya tsaya inda ya baiwa wani likita damar kula da lafiyar Metuh bayan kwasan jiki da fadi rinjim.

Inda jami’an lafiya na kotun suka kawo masa dauki cikin gaggawa da misalin karfe 9.19 safiyar jiyan.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: