Duk Duniya Ana Yabon Buhari Kan YAki Da Cin Hanci Da Rashawa-Isah Tafiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Duk Duniya Ana Yabon Buhari Kan YAki Da Cin Hanci Da Rashawa-Isah Tafiya

Published

on


ALHAJI ISAH TAFIDA ya na Daya daga cikin ’yan kwamiti ingatatu na Kungiyar yaKin neman zaBen shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a zaBen 2019 da ke tafe. A tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU ASABAR, Tafida ya jaddada cewa, a ko’ina a duniya a na yabon shugaban Kasar kan KoKarin da ya ke yi wajen yaKi da cin hanci da rashawa, musamman ma irin yabon da shugaban ya ke samu daga manyan Kungiyoyi a ko’ina da Kasashen duniya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

 

Me za ka ce kan wasiKa da ’yan Sabuwar PDP su ka rubuta wa Shugaba Buhari cewa ba a sauraran su?

Da farko dai kamar ni, mamaki abin ya bani; mamaki a cewa Kungiya guda ta shiga ta haDe da wasu Kungiyoyi ta kafa jam’iyya, bayan gudanar da wannan jam’iyyar shekara uku , har yanzu ta na cewa ba a yi da ita; to dan Allah ta yaya a ka gudanar da jam’iyyar? Shekaru uku nan me suke yi? Lokacin da gwamnati takafu, mene ne ya sa ba su yi kukar suba? Ba lokaci da kuka ya zamanto baya da kyau kamar yanzu. Ita uwa jam’iyyar kansa, a rurufe take tafiya, amma yanzu an kafa kwammiti na gyara; gami da haka, koke-koken kowa za a samu sulhu, na tabbata baza a rasa matsayi a uwar jam’iyyar da za a ba su wanda zai kamanta biyan buKatansu ba.

 

Sun ce duk abinda su ka nema, kusan ba basu ba; KoKari da suka yi suka nemi shugaban Majalissan Datawa, wato Bukola Saraki ke nan? Sun ce a na yaKi da su kamar su ba ’yan APC ba ne…

Duk dai, lokaci baci ba a inda ba za a fitar ba. Lokacin da zuciya ya Baci kuma, ba irin magana da mutum ba zai zarta ba; amma dukka, zama da datawa  na aiki da hankali; yi haKuri, na yi. bari wannan, na bari, shi zai gyara matsalar. Ni dai, a sona, ni na fara ce masu su yi haKuri. ‘Saraki’, na ce masa, ‘ka yi haKuri kai dattijo ne. Baban ka, mu yara Kanana  ne a KarKashin sa. Shafa kanmu yake yi ya yi mana albarka. Kuma muna tare da shi har Allah ya Dauki ransa. Allah ya jikan shi. Kai ma muna nema da kai. Ka zo ke nan ba zaka fita ba. Duk abin da ya Bata maka rai, Saraki ka yi haKuri.’

Danjuma Goje kai mutumi na ne. Tun muna yara tare muke duk wurin da muka haDu mu ’yan’uwa ne. Yanzu kuma ina cewa ka yi haKuri. Duk abin da ya same ka, duk muzguna wa da aka yi maka kokake tsamani anyi maka, muna ganni, muna ji. Haka sauran waDenda na sani da waDenda suka sanni a cikin wannan nPDP, mu na ce masu su yin haKuri. Kuma in Allah ya yarda za a tuntube su ta hanyan databge irin su Tinubu, Su Maitaimain Shugaban Jam’iyyar na Arewanci Kasan nan. Kuma in an samu sabbi shugabannin Din za a zauna da su. Duk abin da ya kamata za a yi ma su.

Duk rigimar da Buhari ya zo ya tarar, duk yana cikinsu, ta hanyan da ya da bai haDu ba. WaDenda yaKiKira, kowa idonsa kalon sama ya ke yi.  Shi ya sa kagan idan akwai matsala babba, yakan kira kamar su Janar Danbazau.  Ya tura su. Ka san dalili? Saboda amana tun suna soja kuma Danbazau mutum ne wanda in ya yi niyyar zai yi abu, ko in an ce je ka yi abu, ya kan saka dukanini Karfin sa yagan cewa ya ci nasara. In APC ta na da irin sa guda goma, ba yanda abubuwa suke ba za su kasance. A cikin Dari, kashi sitin na APC a matsala take. In aka nemi hanyoyin gyara matsalolin kafin a zaBe sabon Shugaba, za mu fi gamsuwa.

 

Akwai  koke-koke da dama cewa ’yan sabuwar PDP sun shigo APC ne domin a rabu da su a kan tuhumar cin hanci da rashewa da a ke masu. Ko da hakan, kana cewa za sasanta komai da su; yaya za yi da zargin da ake masu?

Kowa da yake zargi a kan sa, do ka za ta hukun ta shi.  Ka tuna cewa Buhari rantsuwa ya yi akan hakan. Kuma duk duniya yabon shi ake yi cewa a batun cinhanci da rashewa ya yi KoKari a zo a gani.

 

Jama’a da suka halarce taron PDP da aka yi a jihar Katsina da Jigawa, ita APC ba ta fara tsoro cewa PDP ta fara Karfi kuma ba?

Yaro ni professional ne a harkokin hotuna. Ya gano yanda aka yi manipulation hotuna da ga taron domin mutuna su aza cewa akwai babban halarta. Duk manipulation ne da ka sa a media. Ita APC, lafiya lau take. Abubuwa da dama da PDP ba ta iya ba a shekaru masu yawa, APC ta ci nasara a cikin shekaru uku. Manomi kuma suna jin dadi kwarai. Amma ina shawarce Buhari cewa ya bada oda ga jamiyar tsaro su tabatar cewa ’yan bindigogi masu sata mutane an kama su kafin watan Augusta domin manoma su iya tafiya gonaki su.

 

Yaya kake gani cewa zaBen 2019 za ta gudana?

Nasara ce da APC a kowani fani domin KoKari da ta yi na tafiyar da Kasa a fanin raya Kasa da ci gaban Kasa. Ita APC ta tsayar da Buhari a matsayin me takarar shugaban Kasa kuma, su jam’iyoyi da suka rage suna iya tsayar da kowa da su ka so, amma na san cewa, ko ma wanne ne, nasara na wurin Buhari domin talakawan Najeriaya suna tare da shi domin sun san KoKari da ya ke yi na tafiyar da Kasa yanda ya kamata. Ba kuma a Najeriya kaDai ba amma duka Duniya. WasiKoKi da wanda ba su son cin gaba su ka rubuta ba zai kawa matsala ba domin talakawa sun san cewa Buhari mai gaskiya ne. Baka gan yanda shugaban Kasan Amerika ya tarbe shi lokacin ziyaran sa Amerika ba a makonin da suka wuce ba? Wani shugaban Kasar Najeriya ne Amerika ta taba masa hakan? Sun san KoKarin Buhari shi yasa suka bashi babbar namba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!