Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sace Sandar Majalisa: An Canza Wa DPO Wurin Aiki

Published

on

Shakatar ‘yan sanda ta kasa dake birnin tarayyar Abuja, ta karyar ta yamadin da ake yi cewar ta canzawa DPO din ta dake tabbatar da tsaro a majalisar tarayya  Sulu-Gambari Abdul zuwa jihar Adamawa ko zuwa jihar Yobe kamar yadda kafar gidan talabijin ta TBC News ta yada.

Kakakin ta Jimoh Moshood ya karya hakan a hirar da kafar ta TBC News ta yi dashi ta hanyar wayar tafi da gidan ka a Abuja a ranar asabar data gabata, inda ya ce, babu wani abu makamancin hakan.

Sai dai, wata majiyar ‘yan sanda da ta  tseguntawa TBC ta ce, kakakin zuki ta malle ce kawai yake fada, inda majiyar ta ta hakikance akan aukuwar hakan ganin cewar, tuni aka tura sabon DPO don ya cike gurbin Abdul a majalisar.

Majiyar ta ci gaba da cewa, DPO din an canza masa aiki zuwa jihar Adamawa ne ba jihar Yobe ba.

Majiyar ta kara da cewa, DPO da aka canza masa wurin aikin, yaje gidan kwana da na majalisar don tattara kayan sa, sam-sam, Jimoh karya ce kawai yake zugawa, domin an tura wani ya cike gurbin sa.

Har ila yau, wata majiyar a majalisar,   ta tabbatar da cewar, shugaban ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris ya bayyana cewar tsohon DPO din ya wuce makadi da rawa wajen fallasa bayanan da suka shafi harkar tsaro a lokacin da karamin kwamitin majalisar, da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Sanata  Bala Na’Allah da kuma Betty Apiafi suke jagoranta suka gayya ce DPO din don don yin bayani a gaban kwamtin  akan kawanyar da aka yiwa majalisar a kwanan baya da kuma sace sandar majalisar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: