Ba Kyan Namiji Ne Zai Mun Zaman Aure Ba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SOYAYYA

Ba Kyan Namiji Ne Zai Mun Zaman Aure Ba

Published

on


Rayuwar soyayya akwai dadi kuma yana yin ta yana saka masoya cikin nishadi da mararin juna, ta wani fuskar kuma takan saka kunci da kuma damuwa idan har akayi rashin dace, ba kowanne masoya ne soyayyarsu take kai su da aure ba, ma fi akasari an fi samun masoyan da suka tafka soyayya da juna ba tare da sun auri junan nasu ba,walau a karshe su rabu saboda wani dalili na daban wanda ya gifta ta tsakiyar soyayyarsu ko kuma dayan ciki ya rasu. A bisa bincike irin na masana soyayya sun gano faruwar hakan dai-daiku ne suke iya auran junansu ko da kuwa sun auri junan nasu soyayyar wasu ba ta karko dan ba a iya karshen ta a gidan aure nan gaba kadan zan yi bayani game da wannan matsala ta masoya. Da yawan lokaci wannan shafi yakan karbi bakin masoya daban-daban don jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rayuwar soyayyar su don sauran masoya su ji su kuma kara kyautata soyayyar su wanda yake na gyara, su gyara. A yau ma wakiliyar wannan shafi Muhiebert Abdullahi ta karbi bakuncin hadaddiyar masoyiya ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:

Barkanki da kasance wa cikin wannan shafi na soyayya da shakuwa

Yauwa barka dai.

Da farko  za mu so mu ji cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi da kuma dan takaitaccen tarihinki.

Sunana shi ne Fateema Muhammad Argungu amma an fi sani na da Zarah Bint Muhammad, Shekaru ta 22 ni haifaffiyar garin birnin Kebbi ce a nan na yi  firamare da sakandire dina, bayan na kammala na samu admission a jami’ar Usman Dan Fodio da ke  Sakkwato inda nake karanta Pure Islam a mataki na 3(300 lebel)

Masha Allah! Shin malama Fatima kin taba soyayya ko kuwa tukunna dai?

Ehh na taba but not that serious irin sama-sama haka.

 Me ya ja hankalinki har kika fara soayya?

Gaskiya ba zan iya cewa ga abin da ya ja hankalina wajen fara soyayya ba, kawai na tsinci ni da fara ta.

Za ki kamar shekara nawa kina soyayya, kuma kina kamar shekara nawa kika fara soyayya?

Gaba daya ba a shekara biyu ba, kasancewa ta a ciki har ma da fara ta din.

Shin a cikin shekara biyun da ki kai da fara soyayya kin taba samun wani kalubale ciki?

Ehh a gaskiya na taba samun kalubale

Ko za ki iya fada mana irin kalubalen da kika taba fuskanta?

Kalubalen da na samu shi ne genotype dinmu, combination din bai yi daidai ba, saboda dukkan mu mun kasance carrier.

Baya ga haka ba ki taba samun wani kalubale ba?

Ehh akwai wani but wannan family issue ne

Bayan da kuka gano ku carrier ne kun ci gaba da soyayyar ne ko kuwa rabuwa kuka yi?

A’ah Ba ma tare rabuwa muka yi.

Wacce hanya kuka bi wajen rabuwa da junanku musamman yadda kuka sha soyayya?

Ta hanyar tawakkali ga Allah, yarda da kaddara saboda haka Allah ya tsara Kuma shi ne ma fi alkairi a rayuwarmu.

Ya batun yaudara da ake ta yawan maganarta shin an taba yaudararki?

A’ah ba a taba yaudara ta ba.

Ko za ki iya yi mana bayani yanda yaudara take a takaice?

Toh yaudara ma  kashi-kashi ce, yaudara wata hanya ce wanda namiji ko mace kan iya bi wajen cutar da junansu ta hanyar soyayyar karya da makamantan haka.

 Gaskiya ne! Idan kika ci karo da wanda ya yaudare ki shin wanne mataki za ki dauka?

Ehh toh idan har Allah ya jarrabe ni da mayaudari, toh matakin da zan dauka shi ne hakuri saboda shi ne maganin komai a rayuwa, idan ka bar wa Allah komai shi ne zai ma ka magani Kuma yai maka zabi ma fi alheri.

Masha’Allah! kasancewar muna cikin watan Ramadan ya kike gudanar da soyayyarki misali kamar wajen ba wa junanku kula wa zuwa zance ko makamancin hakan?

Ehh toh Ba na soyayya a yanzu gaskiya

Ke nan tun bayan rabuwarku da wancen baki kara ci gaba da soyayya ba?

Ehh

 

Me ya hanaki soyayya a yanzu ko kuwa zafin rabuwa da shi ne ya janyo daina soyayyarki duk da kin ce soyayyar da ki kai ba tai tsanani ba?

A’ah ba zafin rabuwa ba ne gaskiya saboda can baya na fada I am not addicted, kawai na zauna abina ne haka nan.

Hakane! Idan na fuskance ki gaba daya rayuwar soyayyar ta ki da mutum daya kika yi ta haka ne?

Ehh haka ne.

Yanzu kuma ba ku tare saboda wasu dalilai shin yaushe kike tunanin za ki ci gaba da yin soyayya?

Ni kaina ba zan ce miki ga lokacin ba, Allah kadai ya san ko wanne lakaci ne.

Gaskiya ne, wanne irin farin ciki kika taba fuskanta cikin soyayya?

Toh Alhamdu Lillah na samu farin ciki ta yanda nake samun kulawa daga wajen shi

Masha’Allah! Wasu masoyan sukan kira soyayya da munanan kalmomi kamar soyayya masifa ko bala’i da dai sauransu ya zaki kwatanta yanda soyayya take a wajenki?

Ehh it’s defends da irin wanda kuke tare duk wanda kika ga ya kira soyayya da mummunan kalma to yana da dalili, haka ma wanda ya yaba to Shi ma yana da nasa dalili,but gaskiya ni am not addicted da ita.

Wasu Mazan idan suka ga mace a hanya suka ji suna santa sukan yi kokarin ganin sun tsaida ita domin sanar mata da abin da yake zuciyarsu, shin idan hakan ya faru a kanki za ki tsaya? kuma ya za ki dauki soyayyar ta sa a lokacin?

A’ah ba zan iya tsaya wa ba. Ba na ganin ya dace namiji ya tare ni a hanya cewar yana sona, ban son irin wannan halayya kuma idan ma hakan ta faru gaskiya ba zan ba shi kulawa ba duk da cewa wani lokacin babu yanda za su yi wannan ita ce damar da suka samu, kuma idan ta wuce shike nan may be ba za su kara gani na ba.

 

 Hakane! toh wanne irin namiji kike son aura?

A rayuwa ta ina burin auren namiji wanda ya kasance well educated both Islam da na boko haka wanda ya san darajar mace  da ta iyayenta,haka ya san darajar addininsa.

 

 Wanne irin namiji ne kuma ba ki so ?

Ban san namijin da bai wadatu da ilimi ba both na Arabia da na zama sannan wanda bai sani darajar dan’adam ba, saboda irin wadannan ko darajar aure ba za su sani ba.

Ya batun kyau fa? Wasu matan ma fi akasari sukan ce sun fi son namiji kyakkyawa, fari wanda kamar shi ya yi kansa, mai kudi da dai sauransu, shin ya hakan yake a wajenki?

Ba na duba da wannan, saboda ba kyan ne zai min zaman aure ba, kyan halayyar sa shi ne zai sa aure ya dore.

 Haka ne! Ya batun kishiya fa? Shin kina cikin matan da suke son a yi musu kishiya ko kuwa ya abin yake?

Toh auren fiye da mata daya dama ce wacce maza suka samu daga Allah(SWT) fargaba ta ita ce ban san wacce zan tarar ko wacce za ta tarar da ni ba,fatana idan har ina da rabon zama da kishiya Allah ya datar da ni da ta kirki.

Da kyau! Na kan ji wasu ‘yan matan na addu’ar cewa Allah ya ba su namijin da iyayensa suka rasu saboda tsoron tashin hankalin uwar miji da ake yawan fada, shin ya hakan yake a wajenki?

A ganina wannan bacewar basira ce, kuma ba haka yake a wajena ba

Da kyau! Wanne irin jan hankali za ki ga masu irin wannan tunanin?

Toh Jan hankali ga mata masu irin wannan tunanin shi ne rayuwar iyayen mijin da rashin ta ba shi ne jin dadin aure ba,wani sa’in ba sa raye amma kuma ba kajin dadin mijin, idan har za ki jajirce ki zama suruka ta kirki sannan kina haduwa da addu’a saboda shi zaman aure sai an hada da addu’a, idan kina hakan insha’Allah ba za ki samu matsala ba, idan ma Kin ga matsala still bayan kina kokari to jarabawa ce daga Allah Kuma idan ki ka yi hakuri za ki ci riba gaba.

 

Da kyau! Idan muka duba yana yin soyayyar yanzu ta fi karkatuwa ne ga social media ya za ki kwatanta soyayyar zahiri da kuma ta soyayyar network a wajenki?

Toh ni a gani na soyayya wacce a kan network kawai ta ta’allaka Kamar bata lakaci ne, sai dai ana iya haduwa a social media har ta kai ga aure but ace haduwar media a yi soyayya a rabu Kuma duk a media duk shirme ne a gani na soyayyar zahiri ta fi tasiri sosai gaskiya.

Idan kika ci karo da wanda ya ce yana sonki a social media  za ki iya yarda da soyayyar da yake miki har ki amince?

Ya danganta da yanda ya tunkare ni da maganar,wani namiji na da hikima wajen iya magana har mace ta aminta da shi wani Kuma magana daya zai yi in ji cewa wannan ban san abin da yake ba.

Wanne irin kalar abinci kika fi so?

Ban da abincin da na fi so, kowanne ya samu Alhamdulillah

 

 Da kyau!  kayan sa wa fa wanne iri kika fi so?

A fanni tufafi na fi son atamfa

 

 Wanne kala ne ya fi burge ki a rayuwarki?

Ash and gold.

 

Wanne suna kika fi so masoyinki ya kira ki da shi?

Duk Wanda ya burge shi ya kirani da shi

 

Da kyau! Wanne shawara za ki ba wa masoya?

Shawara ga masoya ita ce a duk lokacin da zama ya hadaka/ki da masoyi, a yi soyayya don Allah kuma kada a ci amanar juna, sannan dole sai an hada da hakuri sannan za a cim ma burin da ake son akai.

 

 Malama Fatima Zarah muna godiya da fatan za ki sha ruwa lafiya.

Ni ma na gode.

Wannan shi ne karshen tattaunawar da wakiliyar wannan shafi ta yi da Fataima zarah ku kasance wani makon da ganin da mai shafin zai tawo muku da shi, Kusha Ruwa lafiya Masoy._

Advertisement
Click to comment

labarai