Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mahaukaci Ya Yi Kokarin Yi Wa Matar Aure Fyade A  Kasuwa

Published

on

Wani wasan kwaikwayo ya auku a sananniyar kasuwar Ogbeogonogo dake garin Asaba, cikin jihar Delta a yayin da wani da ake zargin mahauci ne ya yi mai matsakaicin shekara lokacin da ya yi kokarin yiwa wata matar aure fyade a cikin kasuwar.

Lamarin ya auku ne a ranar asabara data gabata kuma lamarin ya auku ne da misalign karfe biyu na rana a lokacin da matar take kan sa’anar ta ta sayar manja da kayan masarufi.

Wata ganau mai suna Janet Agbou ta shedawa kafar Daily Post cewar, mahaukacin mai suna Simeon wanda yake sanye da yagaggun sitira ya yi kokarin hawan bayan matar, inda hakan ya janyo farfashewar kwalaben ta dake cike da manja.

Janet Agbou ta kara da cewar, mahaukacin ya samu nasarar cire mata zani har ya samu danne ta kuma ga dukkan alamu mutumin mahaukaci ne. A cewar Janet Agbou  mahaukacin ya yi kokarin sanya alurar sa a cikin gaban matar, inda masu wucewa suka kawo mata dauki suka kuma fara danawa mahaukacin na jaki.

Daga baya an mika mahaukacin ga ‘yan sanda na gundumar “A”, inda bayan da suka gudanar da bincike suka gano cewar mahaukaci ne. Da take hira da kafar ta Daily Post matar wadda ta bukaci kar a ambaci sunan ta tace lamarin ya girgizata.

A cewar matar, “ Ji kawai na yi an kama ni ta baya, kuma wanda ya kama ni din yana ta kokarin keta mutuncina, wanda a kokowar da muke yi ne sai muka fadi a kasa a tare, inda na fara ihun a kawo mini dauki. Gungun mutane sun bashi kashi daga baya aka mika shi ga ‘yan sanda.

Ta kara da cewa, ni matar aure ce mai ‘yaya uku, wannan aikin shedan ne kuma na godewa Allah da ya tsyar da abin a nan domin ban taba sanin wannan lamarin zai auku dani ba. Da yake jawabi akan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Aniamaka Andrew ya ce, duk da jibgar da mahaukacin yasha bai ce uffan ba.

Ya sanar da cewar munyi amannar a bisa binciken da muka gudanar mutumin mahaukaci ne kuma baza mu iya tsare shi ba mun dai kashi asibi don ayi masa magani.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: