Jami’ar FUTA Ta Fara Gudanar Da Noman Kasuwanci — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Jami’ar FUTA Ta Fara Gudanar Da Noman Kasuwanci

Published

on


Jami’ar kimiyya da aikin noma (FUTA) dake garin Akure ta gabatar da sabin irin tumatir.

Jami’ar ta yi hakan ne don cika daya daga cikin dalilin da da ya sanya aka kafa jami’ar.

Da yake kaddamar da shirin, shugaban hukumar jami’ar kuma tsohon sanata Joseph Waku, ya danganta matakin da cewar yazo akan gaba.

Waku ya nuna jin dadin sa akan wannan namijin kokarin, inda ya yi nuno da cewar, kokarin ba wai kawai zai wadata jami’ar bane kawai da kuma garin na Akure ba, harda kuma samar da kudin shiga ga jami’ar.

Ya kara da cewa, wannan kokarin ya nuna a zahiri yadda jami’ar ta tsarewa tsara wajen daukar matsayin ta na habaka aikin noma wanda kuma zai amfani makwabta da samarwa da jami’ar kudin shiga.

A cewar Waku, ta hakan kuma za’a ilimatar da kananan manoma akan dabarin noma na zamani.

Shima a nashi jawabin, mataimakin shugaban jami’ar  Joseph Fuwape, ya nuna jin dadin sa ga hukumar jami’ar a bisa amincewa da bukatar yin noman zamani a jami’ar.

A cewar sa, saboda mahimmanci da aikin yake dashi da kuma kudin da ake bukata, mahukuntan jamikar sun yanke shawarar yin hadaka da masu ruwa da tsaki dake ciki da wajen jami’ar.

Da yake jadda dawa akan maganar mataimakin jami’ar, mataimakin sashen ci gaba Philip Oguntunde, ya bayyana cewar, don a tafiyar da aikin akan yadda ya dace da kuma cimma bukatun kuddin da ake bukata, dukkan sassan koyar da darussan kasuwanci an sanya su a cikin aikin.

An sanya gonar akan aka sha biyar kuma ta hada da yin kyankyasa da noman kifi da dabbobi.

A jawabin sa a wurin taron akan ci gaban, Shugaban sashen makarantar koyon darasin aikin noma da fasa, Farfesa Taye Amos, ya baiwa Waku da mahukuntan jami’ar cewa za’a lura da aikin yadda ya kamata.

Don nuna a zahiri akan aikin, Waku tare da mataimakin jami’ar sun Farfesa  Fuwape da kuma Farfesa Amos, sun nuna yadda ake shuka masara irin da jami’ar ta samar, inda suka zuba takin zamani.

Don a kula da aikin, an nada Dakta O. P. Aiyelari a matsayin Janar Manaja na riko  na kamfanin Farm Serbices tare da Dakta S. O. Aro a matsayin koodinata na sahen kamfanin dabbobi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!