Bazawara Ta Tona Asirin Tsohon Gwamnan Jihar Taraba Nyame – EFCC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Bazawara Ta Tona Asirin Tsohon Gwamnan Jihar Taraba Nyame – EFCC

Published

on


Hukumar  yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana yadda wata bazawara ta bai wa hukumar damar gano badakalar kudi da tsohon gwamnan jihar Taraba Rabaran Jolly Nyame ya tabka.

Hukumar  ta sanar da hakan ne a cikin rahoton da ta wallafa a mujallar ta mai suna EFCC Alert, inda ta ce, lamarin badakalar ta rincabe wa Nyame ne bayan da wata bazawara mai suna  Hauwa Usman ta rubutawa hukumar takardar koke a kan almubazzarancin kudin wani kamfani da wani mai suna Suleiman, ya yi kani ga marigayin majin ta ya yi.

Suleiman ya ci gaba da jan ragamar kamfanin ne daga marigayin wanda shi ne Manajin Daraktan kamfanin da ake kira Alusab.

EFCC ta kara da cewar, a yayin da take tuhumar Suleiman ne aka gano sauran naira miliyan 100 da tsohuwar gwamnatin sa ta biya kamfanin na Alusab don aikin samar da ruwan sha.

Gwamnatin ta bayar da Chek na naira  135,794,607  ga kwamfnin a zaman kudin kwangilar gyran aikin ruwa na Ibi Wukari, amma Suleiman ya karbi Chek din ya zuba kudin a wani asusun banki na daban da ya daina aiki na bankin Zenith Bank Plc dake garin Jalingo.

A cewar EFCC, Hauwa ta nemi ta taimaki EFCC don maido da kudin, inda kuma hukumar ta soki   Suleiman wanda yaci gaba da jan ragamar kamfanin ya kuma yi almubazzaranci da kudin.

Daga baya, EFFC ta gayyaci Suleiman don ya amsa tambayoyi, ida daga nan asiri ya tonu.

Hukumar ta ce, a lokacin da take tuhumar Suleiman ya amsa karbar Chek amma ya hakikance cewar bai almubazzarantar da kudin ba kamar yadda ake zargin sa ya kuma ce aikin na samar da ruwa da ake Magana ana kan yin sa tun kafin rasuwar yayan nasa.

Suleiman ya bayyana cewar, dukkan abin da ya aiwatar ya yi a bisa umarnin Nyame.

In a za a iya tunawa a ranar 30 ga watan Mayu ne kotu ta yankewa Nyame hukuncin zaman gidan Yari na shekara sha hudu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!