An Karrama Gwamna Ganduje A Kasa Mai Tsarki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Karrama Gwamna Ganduje A Kasa Mai Tsarki

Published

on


Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu Gayyata daga Manajan  Global Foundatuon dake Kasar Saudiya Masu aikin dinkin rigar Ka’aba  da Kuma Masallachin Annabi dake Madina  bisa umarnin Sarki Abdussalam na Makka. An kuma zagaya da Gwamna Ganduje wuraren da wannan Kamfani ke gudanar da ayyukan sa wadda manajan kamfanin ya jagoranta.

Manajan Kamfanin dake aikin gudanar harkokin dinka rigar da ake sanyawa Ka’aba da Masallachin Annabi dake Madina, ya yaba bisa Kwazon Gwamna Ganduje  musamman  kan Kokarin sa na musuluntar da Maguzawa, Gina Masallatai da kuma tallafawa duk wata harkar addini.

Da yake gabatar da jawabinsa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya godewa Allah  wanda ba don amincewarsa ba da wannan nasarorin basu samu ba,  Saboda haka sai Gwamna Ganduje ya bukaci daukacin al’umamr Musulmi aduk inda suke a Duniya dasu sa Jihar Kano, Nijeriya da dama Duniya baki daya cikin addu’o’insu, musamman acikin wannan wata mai albarka tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. An Karrama Gwamna Ganduje da Kyautar Alkur’ani mai tsarki.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!