NAERLS Ta Horas Da Kungiyoyin Manoma 40 Hanyar Amfani Da Sabbin Na’uran Noma — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

NAERLS Ta Horas Da Kungiyoyin Manoma 40 Hanyar Amfani Da Sabbin Na’uran Noma

Published

on


Cibiyar bincike da samar da dabarun aikin gona NAERLS dake jami’ar Ahmadu Bello Samaru Zariya samar wa da manoman kasarnan wasu sabbin kananan na’urorin aikin gona na zamani tare da horas dasu hanyoyin amfani da na’urorin, na’urorin sun hada dana yin haro da huda da shuka da noma da sa taki da girbi da sussuka da shekewa har da durawa cikin buhuna.

Da yake jawabi a wajen taron manoman, Malam Murtala Galadima wanda kuma shi ne shugaban sashin wayar da kan manya da kananan manoma, ya ce, cibiyar tasu ta dade tana neman hanyar da zasu samar wa da kananan manoma na’urorin da zasu sami saukin aikace-aikace aikin gona, sai a wannan lokacin Allah ya basu ikon yin haka, musamman ganin cewar, karamin manomi baya iya saye ko daukar hayan “Tarakta”,

Haka kuma, Malam Murtala Galadima ya tabbatar da cewar duk manomin da ya mallaki wadannan na’urar, idan yana noma hekta daya ne a da, to a yanzu zai iya noma hekta biyar ko sama da haka.

Daga karshe ya ce ,wadannan na’urorin  mutum zai iya saye don ya mallake su, in kuma haka bai samu ba, zai iya daukar hayan su cikin kankanin farashi.

Wakilinmu ya sami zanta wa da Malam Bashir Magaji da Malam Musa Garba Badamasi da Malama Binta Yunus da Malama A’ishatu Ibrahim Sani, wadanda suka sami damar halartan taron inda duk cikansu suka nuna matukar godiyarsu ga Allah da ya sa wannan cibiyar ta kafu a Arewa, sannan kuma ya kadarta duk wani ci gaba idan ya zo su ke fara amfana da shi, sannan kuma sun tabbatar ta cewar, na’urorin za su iya habbaka aikin gona cikin dan karamin lokaci. Sun kuma bayyana matukar amfana da horaswar da suka samu, sun kuma yi alkawarin yada ilimin da suka samu ga sauran manoman da basu samu zuwa taron ba.

A nasa jawabin, shugaban cibiyar Farfesa Kabir Othman Wanda mataimakinsa Farfesa Emanuel Ikena ya wakilta, ya yi kira ne ga manoman dasu yi amfani da duk shawarwarin da suka ji daga bakin kwararrun masana, sannan kuma ya karfafesu dasu yi kokarin mallakar wadanan sabbin na’urorin a daidaikunsu ko kuma a kungiyance, domin cika wa gwammanatin tarayya burinta na wadata kasarnan da abinci.

 

Advertisement
Click to comment

labarai