Arsenal Tana Gab Da Kammala Cinikin Torreira — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Arsenal Tana Gab Da Kammala Cinikin Torreira

Published

on


Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kusa kammala cinikin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Sampadoria, Lucas Torreira dan asalin kasar Uruguay

Tun bayan fara aikin koyar da kungiyar, sabon kociya Unai Emery ya bayyana cewa zai kara karfin yan wasan tsakiyar kungiyar domin gogawa da takwarorinta na Manchester City da Manchester United a wajen neman lashe gasar ta firimiya a kakar wasa mai zuwa.

Dan wasan a kakar wasan data gabata ya buga wasanni 36 a kungiyar ta Sampadoria a dukkanin wasannin da kungiyar ta buga sannan kuma ya zura kwallaye hudu sannan kuma ya taimaka anzura kwallo daya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana kungiyar kwallon kafa ta Sampadoria ta kusa kammala siyan dan wasan tsakiyar kungiyar  Lokomotib Zagreb wanda zai maye mata gurbin Torreira din.

Kungiyar Sampadoria dai tayiwa dan wasan nata kudi fam miliyan 22 ga duk kungiyar datake son daukar  dan wasan sai dai tuni aka bayyana cewa Arsenal batada matsalar biyan kudin dan wasan muddin dan wasan ya amince zai koma.

Kungiyar kwallon kafa ta Eberton ma dai tana zawarcin dan wasan wanda a yanzu haka yana kasar Rasha domin wakiltar kasar sa a gasar cin kofin duniya.

Advertisement
Click to comment

labarai