Gwmanatin Katsina Ta Yi Hadaka Da Wani Kamfani Don Bunkasa Ayyukan Ci Gaba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwmanatin Katsina Ta Yi Hadaka Da Wani Kamfani Don Bunkasa Ayyukan Ci Gaba

Published

on


Gwamnatin jihar Katsina da wani kamfani mai suna mutual construction company sun sha wata yarjejeniya ga wata kwangila ta aikin gina madatsar ruwa a garin Danja.

Kwamishinan albarkatun ruwa Alh. Salisu Gambo Dandume wanda ya sa hannun a madadin gwamnatin jiha ya bayyana cewa aikin gina madatsar ruwa zai lakume kudi kimanin naira miliyan dubu takwas.

Kwamishinan ya ce ana sa ran kammala aikin cikin shekaru 2.

Alh. Salisu Gambo Dandume ya bayyana cewa aikin ginin madatsar ruwan na daga cikin kudurin gwamnati mai ci yanzu na kashe makudan kudade wajen samar da ruwa domin amfana yau da kullum da noman rani.

Sai dai kwamishinan ya hori kamfani da aka hannatama aikin da ya yi aiki mai nagarta ya kuma kammala aikin daidai lokacin da aka kayyade.

Ya yi kira ga al’ummar da zasu amfana da aikin dasu ba kamfanin goyon baya da hadin kai domin kammala aikin yadda ya dace.

A jawabinsa manajan Darakta wanda ya sa hannu a madadin kamfani ya sha alwashin bin ka’idoji da dokoki yarjejeniyar da aka yi wajen aiwatar da aikin.

Babban sakatare a hukumar kula da ma’aikata ta jiha Alh. Nasiru Bawale Danja ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jiha bisa aiwatar da aikin wanda zai bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankin dama na jiha baki daya.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin jihar Katsina ta duba ci gaba da aikin gina hanyar data tashi daga Dabar-Kakutu-Sundu dake yankin karamar hukumar Danja.

Gwamna Aminu Bello Masari ya zagaya wurin ne a lokacin ziyarar duba aiki da babban sakataren ma’aikatar ayyuka Alh. Hafiz Iliyasu wali.

Gwamnan ya samu rakiyar daraktan aikace aikace na ma’aikatar injiniya Salisu Mamman Daura.

Gwamna Aminu Masari wanda ya tuka motarsa a cikin jerin gwanonin motocin ya tsaya a wata korama da ake kira Barwa yayin day a bada umarnin a canza hanyar da ruwa ko korama kebi ta hanyar zuba akwatin kwalbatin wadda tuni an fara.

Haka kuma, gwamnan ya duba ginin hanyar burji ta tashi daga Dan-maigauta wadda ta hada babbar hanyar dake daf da zuwa Kakumi.

Gwamnan ya bayyana gamsuwar ayyukan da ake aiwatarwa a hanyoyin guda 2.

Kazalika gwamna Aminu Bello Masari ya tsaya inda ya duba wani sabon ginin reshen Bankin Access wanda tuni ya fara aiki a garin Danja.

A dukkanin wuraren da aka ziyarta al’ummomin yankunan sun nuna farin ciki da kuma yin maraba lale da gwamnan.

 

Advertisement
Click to comment

labarai