Connect with us

LABARAI

Babban Taron Kasa: APC Ta Dakatar Da ‘Yan Takara 19

Published

on

Gab da fara gudanar da babban taro na kasa na Jam’iyyar APC, kwamitin Jam’iyyar mai sauraron kararraki wanda gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ke shugabanta ya ce, ya zuwa yanzun har ya dakatar da ‘yan takara 19.
A lokacin da yake yi wa manema labarai bayani sa’ilin zaman kwamitin a Abuja, ranar Asabar, ya ce, sun sami koke ne kan masu neman mukaman, Sakataren tsare-tsaren Jam’iyyar na kasa, Shugabar Matan Jam’iyyan ta kasa da sauransu, baccin masu hankoron mukaman shugabancin Jam’iyyar da kuma na babban Sakataren Jam’iyyar.
“In ma har akwai wanda muka wanke, amma kuma akwai wani koke a kansa, muna da daman soke shi ko mu tabbatar da shi, ya danganta ne da ingancin koken da ke kansa.
Ya ce, rahoton kwamitin na shi da shi ne za a yi aiki a dukkanin abubuwan da Jam’iyyar za ta yi, sai dai bai bayyana sunayen ‘yan takarar da suka soken ba.
Ya kuma ce, zuwa ranar Litinin ne za su mika rahoton kwamitin na su, sannan ya ce, duk wani koken kuma sai bayan taron ne za a duba shi.
Sai dai kuma, babban daraktan kafar yada labarai ta Muryar Nijeriya, (BON), sannan daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar ta APC, Osita Okechukwu, ya ce, kwamitin na Rochas ba shi da karfin hana wani dan takara tsayawa ko kuma hana shi sake tsayawa takaran.
Osita Okechukwu, ya yi wannan bayanin ne ranar Lahadi a Abuja, sa’ilin da yake mayar da martani kan jita-jitar cewa, gwamnan na Jihar Imo, zai iya yin amfani da karfin ikon kwamitin na shi ya soke takarar mutane uku da suka fito daga yankin na kudu maso gabas na kasarnan, wadanda shugabannin sashen suka rigaya suka albarkaci takarar na su.
Mutane ukun sune, Osita Izunaso; mai neman mukamin Sakataren tsare-tsaren Jam’iyyar ta APC, Emma Eneukwu da George Moughalu; dukkan su masu neman mukamin mai binciken kudi na jam’iyyar ta APC na kasa.
“A iya sani na, kwamitin Gwamna Masari, bai soke takarar daya daga cikin su ba. Don haka shi kanshi Oorocha ya san ba shi da wannan karfin na yin amfani da koke a kansu ya soke takarar na su.
Babban daraktan na BON, ya kore dukkan shakku, ya ce, tabbas babban taron Jam’iyyar na ranar Asabar 23 ga watan Yuni, zai gudana ne sumul kalau, saboda babu mai ja da Shugaba Buhari a matsayin yin takarar Shugabancin kasarnan a 2019.
Mista Okechukwu, wanda yana daya daga cikin wadanda aka zaba a matsayin wakili a babban taron Jam’iyyar, ya yi hasashen cewa, yawancin wakilai duk tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshimole, ne za su zaba a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar na kasa. Tun da shi ne Buhari ke so.
Ya karkare da cewa, “marawa Shugaba Buhari baya da suka yi bakidayansu, shi ne ya saukaka samun hadin kan da suka samu gabanin babban zaben na 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!