Real Madrid Ta Rage Farashin Ronaldo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Rage Farashin Ronaldo

Published

on


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta rage farashin dan wasa Cristiano Ronaldo daga farashin datayi masa tun farko na fam miliyan 873 zuwa fam miliyan 105 domin samun kungiyar da zata iya biya.
Rahoton kuma ya bayyana cewa kudin da kungiyar tayi masa tasaka dokar cewa banda wata kungiya daga kasar Sipaniya kuma da kungiyar PSG dake kasar Faransa sai dai kowacce kungiya zata iya biyan kudin idan tana son dan wasan.
Ronaldo, wanda a yanzu haka yake kasar Rasha inda yake wakiltar kasarsa a gasar cin kofin duniya ya bayyana cewa yanada niyyar barin kungiyar tun ranar da suka lallasa kungiyar Liberpool a wasan karshe na cin kofin zakarun turai a watan daya gabata.
Kungiyoyi hudu da suka hada da Manchester City da Chelsea da Arsenal da kuma AC Millan duk sun nuna sha’awarsu na daukar dan wasan sai dai an bayyana tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United tana kan gaba a jerin kungiyoyin da ake zargin yanason komawa.
A na zaton Ronaldo zai bayyana makomarsa a Real Madrid bayan an kammala gasar cin kofin duniya a wata mai kamawa

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!