Baragurbi Ke Haifar Wa Da Gwamnatin Buhari Cikas –Dakta Bature — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Baragurbi Ke Haifar Wa Da Gwamnatin Buhari Cikas –Dakta Bature

Published

on


Wannan wata hira ce da ABDULFATAH GOMBE ya yi da shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, DAKTA BATURE ABDUL’AZIZ a karshen makon da ya gabata. Shugaban ya yi bayani kan irin nasarorin da gwmanatin Shugaba Buhari ta samu, da irin tarnakin da wasu ‘yan ta-kife ke haifarwa da gwamnatin. ga yadda hirar ta kasance:

Ko za ka gabatarwa mai karatu da kanka?
Assalamu alaikum, suna na Dakta Bature Abdul’aziz MON, Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya.
Shin Mene ne matsayar ‘yan Kasuwar Nijeriya Dangane da abubuwan da ke faruwa a kasa?
Kamar yadda ka nemi ‘yan kasuwa su ce wani abu, to ni ina ga a nan ‘yan kasuwa suna da abin da za su ce, domin duk hayaniyar nan da ake yi a kasar nan tamu, to muna ganin ‘yan kasuwa ta fi cutarwa, domin in da babu hayaniyar mu kawai ciniki za mu yi ta yi.
To a nan doka da ta killace mutanen da ake tuhuma da cin hanci da rashawa kan cewar wanda yake cikin tuhuma zai kare dukiyarsa ba zai taba ta ba sai an gama tuhumarsa. Saboda wadannan da suke da dinbin dukiyar nan ai suna daukar wannan dukiya fituntinu da suke faruwa a kasar nan na siyasa, da na addini, da na kabilanci, to da yawa daga ciki akwai hannunsu.
Kuma ganin suna da kudin shi ya sa suke juya akalar shugabannin baya yadda suke so, kuma sun yi suna zare ido kan cewa su fa sun fi karfin kowa. To idan aka bar kudin nasu sakaka, da yawa wadanda suka yi rub da ciki din nan aka dukiya, da yawansu fa sun tsorata, kuma da yawansu zare dukiyarsu suke da kadan da kadan suna sake mata wajen ajiya.
To amma idan aka ce kowa an kulle, an datse ma’ajiyar kudinsa, kuma an karbe Fasfo dinsa, to ka ga hakan zai ba da damar a yi bincike sosai, wadanda ba su da laifi a sake su. Amma muna takaicin yadda aka bar su suke ta zungure-zunguren fitina, to wadannan tsofaffi, musamman shi babban tsohon nasu, shi ne fa ake cewa kusan duk Shugaban da yake Afirka ba mai arzikinsa, kuma duk Shugaban da ke Afirka ba mai kadararsa, to ta ina kadarorin nan ko arzikin nan suka samu?
Saboda haka wadannan masu hayaniya da yawan maganganu da za su hada tarzoma a kasa da kuma hada tarzomar ma, da kuma yadda suke sukar Shugaban kasa, kuma Shugaban kasar nan har yau bai ce masu komai ba, da raha ne kwanaki yake cewa za a binciki wani, ka ga daga cewa za a bincike shi, ka ga yadda ya cika duniya da bayanai. Wato a nan in kana da gaskiya aka ce za a bincike ka, to da wa za ka yi fada, kuma fadan me zaka yi? ni ina ga wannan ba abu ne na fada ba, ka bari kawai a bincike ka, ‘Sarki goma zamani goma’ in ka mayar da kanka Allah na wasu Shugabannin da suka wuce, to ina ga Buhari baka ma ishe shi kallo ba, don mene ne, don wanda ya dogara ga Allah, kuma yake jin tsoron Allah, na tabbata ba shi da fargabar kowa, kuma ba ya jin tsoron kome zai same shi akan kishin kasa, kuma akan kishin gida Nijeriya ya mayar da ita tafarkin da za mu yi alfahari da shi a idon duniya, wanda an riga an fara alfaharin, kuma ba ma an fara ba an yi nisa wajen alfahari, saboda duk Shugaba da aka yi a baya, da yake su turawa suna daukar duk wani Shugaba daga Nijeriya mai cin hanci da rashawa ne ba shi da wata kima.
Amma ka ga kamar Shugaban kasa Buhari yadda yake da kima a idon duk duniya gaba daya, amma ka ga a yanzu babu wani Shugaba da yake yi wa Buhari wannan kallo, misali ka ga yanzu babu Shugaban da ya kai na Amurka girma a duniya. Amma ka ga duk da haka Shugaban kasar Amurka, da Shugaban Jamus, da Shugaban kasar Ingila yadda suke ta rububin Shugaba Buhari akan ya kama hanya ta gaskiya. Kuma nan ba da dadewa ba kasashen Afirka kasa 54 suka taru suka sa shi mai girma Shugaban kasa Buhari ya zama shi ne wato wani Shugaban karya cin hanci da rashawa na tarayyar Afirka, kuma ba da jimawar nan ba aka dauki wani dan Nijeriya, wanda abokin aikin Buharin ne aka mayar da shi Shugaban yaki da cin hanci da rashawa ‘Comon Wealths’.

Me za ka ce game da wadanda ke ganin kura-kurai a matakan da Shugaba Buhari ke dauka na yaki da rashawa?
Duk wanda ya ga laifin Shugaban kasa akan ya ce, za’a rufe lalitar mutane, to dan tafiyar su ne, kuma dan uwansu ne, kuma ko da ba dan uwansu bane bai da kishin kasa, soyayyar da yake yi wa mutanen da wawashe dukiyar kasa, to soyayyar tasa ya fi sonsu fiye da kasarsa. Amma muddin mutum yana kishin kasarsa, kuma yana son kasarsa ta kai matsayin da yake so, to ai wadannan mutune da aka sa masu wannan takunkumi ya wajabta, ai siyasa ma mai zuwa za ka ga ta yi tsarki.
Wannan doka ta ba wa soja karin karfi, ka ga ta ba wa ‘yan sanda karin karfi, wannan doka ka ga ta ba wa DSS karin karfi, da cewa mutum ko wanene a takaice ya zasu iya cakumo shi a bincike shi. Idan kundin tsarin kasa a can ya takaita doka, kuma ya ba wa Shugaban kasa dama cewa za a iya tuhumar mutum, kuma za a iya ajiye shi, koko za a iya jigine kayayyakinsa sai an tabbatar da gaskiyarsa, to ya kamata wannan doka ‘yan Nijeriya su goyi bayanta, a karbe ta dari bisa dari. Wanda bai kamata a zuba a mutanen da tun da muka dawo Dimukuradiyya kashi na biyu a kaice sun hana Nijeriya ci gaba, sun hana ta ta kai matsayin da ya kamata ta kai, an ba da kudin wutar lantarki sun cinye, an ba da kudin kashe rigimar nan tun kafin ta yi karfi sun cinye, sun fidda hanyoyi na jiragen ruwa inda za su rika zuwa suna kawo mai, kuma ba a sauke man ba jirgin ya koma da man, an yi wannan babu iyaka.
To ai kasar ba taku bace ku kadai, ai bai kamata a zuba maku ido ta haramtacciyar hanya ku rika lalata arzikin kasa, shi wancan tsoho da ake cewa ya fi ko wane Shugaba kudi a Afirka, tsitsin nan da ake yi talauci, in da za a baje dukiyarsa a fito da ita a rabawa ‘yan Nijeriya, ko wanne sai ya samu naira 250,000. To akalla mutane suna da irin wannan dukiya, amma a kullum su suke aza wutar fitina, su suke aza wutar rigima, yaya za su yi su kawo fitina a kasa yaya za su yi su kawo hargitsi a kasa, yaya za su yi su kawo kabilanci a kasa.
To bari in gaya wa ‘yan uwa ‘yan Nijeriya, wato lokaci yayi da za mu gane cewa wadannan mutane su ne fa masu ba wa ‘ya’yanmu kwaya, suna sayawa ‘ya’yanmu makamai, ‘ya’yan namu ba sa cin riba, sai dai kawai su ba su kwaya, ko su saya masu makamai su kashe kansu. Amma da zarar sun ci zabe to ganin su ma mutum bai isa yayi ba, wadanda a lokacin zaben suke amfani da su idan sun ci zaben da zarar sun gansu a kofar gidansu sais u sa a kama su, saboda suna zaton ko sun zo ne su yi masu dabanci a gida, sun manta su suka sa su dabar.

Al’umma na ganin cewa har yanzu canjin da ake fata bai samu ba. mene ne ra’ayinka akan haka?
Ni ina ganin manufofin nan na Shugaban kasa abin da yake so jinkiri da hakuri, da kuma kowa ya ba da tasa gudunmawar, ta wayar da kan mutane, da addu’a, da kuma ba da bayanai ta hanyar duk inda ya ga wani abu da bai dace ba ya je ya fada don a dauki mataki akan wannan abu. Kuma in dan yi tsokaci, kwanaki da IMF suke cewa mu Nijeriya mu ne na karshen talauci a duk duniya, to karya ne, wanda duk ya fadi haka karya ne. Kasa da aka sani a duniya wadda take cikin lissafi kasa 180 ce da wani abu, to kasa 180 din nan da wani abu, Wallahi tallahi babu kasa 40 a cikinsu wadda tafi Nijeriya rayuwa kamar yadda muke rayuwa. A ce wai muna rayuwa a kasa da dala biyu kullum, to ai in ka duba cewar masu rayuwa a babu komai ma ko ma kasa da haka, ai a kasashen Afirka ma sun fi 40, da akwai lokaci da na kirga maka su daya bayan daya tsakanin Afirka ta Yamma da Afirka ta Arewa, da Afirka ta Kudu, da Afirka ta Tsakiya, kuma Afirka ta Gabas, da na kirga maka su daya bayan daya.
Za Mu Ci Gaba Gobe…

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!