Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutumin Da Ya Cinnawa Kansa Wuta A Titin Legas Ya Mutu

Published

on

Wani  mai sana’ar aski da ya kwararawa kansa manfetur ya kuma kyasta ashana  a daidai da rukunin gidaje na Omole kusa da madakatar  motoci dake Akiode cikin jahar Legas ya mutu.

Matashin ya mutu ne a lokacin da aka kai shi asibiti don ayi masa magani, an dai ruwaito cewar mai askin yazo kan titin ne da misalin karfe 4:30 na yammar ranar larabar data gabata  yana rike da litar manfetur mai cin lita biyar, inda ya kwararawa jikin sa mafetur din ya kuma kyastawa kansa ashana.

Wakilin mu ya gano cewar, wasu masu wucewa da suke da nesa da mai akin a lokacin da lamarin ya auku, sun ruga gunsa don su kashe masa wutar.

Matashin mai suna Ahmed,  ana ce ya mutu bayan da jami’an asibin jahar suka iso wurin da motar daukar marasa lafiya suka dauke shi daga wurin da misalin karfe 5:00 na yammar ranar.

Acewar wani ganau mai suna Gabriel, kafin zuwa jami’an asibitin da kuma yan sanda ofishin lardin Ojodu wurin, wani wasan kwaikwayo ya auku, inda a lokacin da wani yake yiwa Ahmed fifita, wasu masu kallo kuwa sai kokarin daukar hoton mai askin suke yi, ya kara da cewar, Ahmed yana yin sana’ar aski ne kafin ya yanke shawarar kashe kansa.

Ya ce, “ na ganshi a lokacin da yake kwararawa kansa man, inda na dauka cewar ko ruwa ne, a cikin yan dakikiki sai naga ya dauko ashana daga cikin aljihun sa ya kyasta bayan ya kwararawa kansa man, amma anyi sa’a wata mai sayar da abinci a kusa da kofa tana da ruwa, wani mutum ya yi saurin daukar ruwan ya kwarara masa har wasu suma suka bi sahu wajen zuba masa ruwa, wannan abin sabon abu ne dana taba gani.”

Wani makwaci mai suna Tolu ya ce, yaga Ahmed yana tafiya akan titi ya kuma bashi shawara cewar, ya bchanza dabi’ar  shaye-shaye da runguma.

Tolu yaci gaba da cewa Ahmed ada yana da shagon aski  a yankin  Akiode ya jima da rufe shagon ya fara yawo a gari kuma yana shaye-shaye da yawa, inda hakan ya shafi kwakwalwar sa.

Acewar sa, bayan kwana biyu na hadu dashi a kan titii nayi masa magana cewar ya kamata ya chanza dabi’ar sa na kuma ce masa zan kai shi Coci ayi masa addu’a ta musamaman, inda ya roke ni in saya masa gasarshiyar Masara na saya masa ya kuma yi alkawarin zai bini zuwa Cocin.

Shi ma wani ganau mai suna Samuel, ya danganta Ahmed a matsayin dan shaye-shaye kuma mutane da dama dake yankin sun san shi, ada mutumin kirki ne kafin ya chanza halin sa yana zama ne tare da iyalan sa a wannan yankin kuma suna sane da halin da yake ciki.

Wani jami’ai ya sanar da cewar, Ahmed ya mutu ne a ranar Juma’a lokacin da ake yi masa magani a asibi, abin takaici bamu iya kubutar da rayuwar sa ba kuma tuni yan iyalan sa suka dauki gawar sa.

Kakakin Rundunar yan sandan jahar CSP Chike Oti, ya tabbatar aukuwar lamarin amma ya ce har yanzu ba’a yi masa bayani  akan mutuar mai askin ba.

Ya ce mutumin  ya yi yunkurin kashe kansa ne ta hanyar cinnawa kansa wuta, amma an kubutar dashi kuma har yanzu, bamu san takamai man abinda ya sanya ya dauki matakin ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: