Majalisar Dattawa Ba Ta Da Ikon Dakatar Da Ni –Omo-Agege — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Majalisar Dattawa Ba Ta Da Ikon Dakatar Da Ni –Omo-Agege

Published

on


Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Delta ta tsakiya, Sanata Obie Omo-Agege ya ce, takwarorinsa a majalisar ta Dattawa da ma majalisar wakilai ba su da karfin ikon dakatar da shi.

Omo-Agege, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi ga manema labarai a filin saukar Jiragen sama na Osubi, da ke Warri, Jihar Delta, inda wasu al’ummun mazabar na shi suka tarbe shi.

“Majalisar wakilai ko ta Dattawa, kai ko ma wace irin majalisa ce, ba su da ikon iya dakatar da duk wani dan majalisa,” in ji shi.

Dan majalisar dattawan ya sha alwashin bijire wa duk wani matsin lamba daga majalisar domin ta dakatar da shi daga zama a cikin majalisar, domin a cewarsa, hakan yana nufin haramtawa kabilar Urhobo wakilci ne.

“Ba wanda ya isa ya hana ni a cikinsu, kenan kun hana Urhobo wakilci kenan. Hakan ba zai yiwu da ni ba.”

Ya yi wannan maganan ne kwanaki biyar bayan da Majalisar wakilai ta bayar da shawarar dakatar da shi har na kwanakin zaman majalisar 180, a kuma hukunta shi bisa zargin keta alfarman majalisar Dattawa.

Hakan ya biyo bayan watanni uku ne da suka gabata, inda wasu da ba tantance ko su wane ne ba suka farmaki zauren Majalisar ta Dattawa suka hargitsa zamanta tare da guduwa da sandar majalisar.

Omo-Agege ya yi imanin cewa, fadan da yake yi ne da cin hanci da rashawa ya sanya cin hancin da rashawa ke bibiyarsa da yaki.

Ya kara da cewa, “Dukkansu suna son musguna mani ne saboda goyon bayan da nake baiwa bukatar neman sake zaben Buhari.

“So suke su yi amfani da ne wajen rabewa su yaki tare da musguna wa Shugaba Buhari, amma sai suka zabi hanya marar kyau, domin in da a ce sun san ko ni wane ne, da sun janye, domin ni ma zan yake su ne.

 

Advertisement
Click to comment

labarai