Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Yobe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Yobe

Published

on


Rundunar sojan Nijeriya- a ranar Asabar, ta bayyana cewa ta dakile aniyar kungiyar Boko Haram, a wani yunkurin afka wa kwambar sintirin sojojin a garin  Sasawa da ke karamar hukumar Tarmowa, a jihar Yobe.

Birgediya-Janar, Tedas Chukwu, kuma Daraktan hulda da jama’a a rundunar sojan, a Maiduguri ya bayyana hakan ga manema labarai.

Bayanin Mista Chukwu, ya bayyana cewa a ranar Asabar ce zaratan sojan Nijeriya suka yi artabun mayar da martanin kwanton-bauna wanda mayakan suka yiwa kwambar sojojin, wanda karon battar karfen ya jawo halakar mayakan da dama; a garin Sasawa da ke karamar hukumar Tarmowa, a jihar Yobe.

Ya ce, Boko Haram sun kitsa kai farmaki ne a kasuwar Babbangida da nufin wasoson kayan abinci, wanda suka yiwa sojojin da ke yin sintiri a yankin kwanton-bauna.

“a yau 21 (ranar Asabar) ga watan Yuli, kan hanyar Sasawa a karamar hukumar Tarmowa a juhar Yobe, sojojin Bataliya ta 233, ta rundunar Lfiya Dole ta dakile yunkurin Boko Haram, ta hanyar fafatawa mai gauni, a sa’ilin da suka yiwa ayarin sojan kwanton-bauna”.

“sojojin sun yi bata-kashin kare kai daga harin kwanton-baunar, a lokacin da suke gudanar da sintirin kakkabe gudaddun mayakan Boko Haram, wadanda ke watangarereniyar neman mafaka tare da kayan abinci”. Inji bayanin.

Birgediya Chukwu ya bayyana cewa, wasu daga cikin sojojin sun rasa rayukan su, amma dai zancen da ake yi, sun kwantar da kurar.

Mai magana da yawun sojojin ya sake bayyana cewa, baya ga sojojin da aka jibge masu jiran ko-ta-kwana, akwai karin sojan sama wadanda ke shawagi, da zasu gano burbushin mayakan wadanda suka yi shigar burtu.

Har wala yau Kuma, Mista Chukwu ya yi kira na musamman ga jama’a a yankin da su zuba ido tare da bayar da hadin kai dangane da wannan ci gaban da ake samu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!