Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ya Kashe Abokinsa Sakamakon Gardamar A Kan Kudi

Published

on

Wani mutum mai suna Tobi Adeleke ya hadu da ajalinsa a hannun abokinsa Michael Mathew sakamakon gardamar a kan kudi.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne a cikin wani kamfani ranar  Asabar da misalign karfe 11 na dare a layin Adewunmi Adebiyi na Jihar Legas, yayain da suke kokarin raba kudin da aka ba su tare da abokansu, sai fada ya barke a tsanin su yayin rabon kudin. A yayin kokarin raba fadan, sai Mathew ya dauko fasasshan kwalba ya sokama Adeleke a wuyansa. Majiyar ta ce, an garzaya da Adeleke Asibiti na kusa da inda al’amarin ya faru sannan daga bisani aka tafi da shi Asibitin koyarwa na Jihar Legas dake Ikeja domin shan magani. Daga baya kuma Likita ya tabbatar da mutuwar Adeleke. ‘Yan sanda sun cefke Matthew.

Da yake ba da mayani a kan al’amarin, abokin marigayin ya ce, marigayin mutum ne mai kyawawan dabi’a kuma ya hadu da ajalinsa ne sakamakon yin aikin alheri.

Ya kara da cewa “ na dawo daga aiki da misalin karfe 10 na dare ina zaune a kofar gidana sai ga Matthew ya zo hucewa, yana jana da wasa sai na ce masa ya keleni domin na gaji.

“Bayan wasu dan lokuta sai na ji hayaniya kamar ana fada, ina zuwa wajen sai na tarar Matthew ya dabawa Adeleke kwalba.

“ Na yi sauri na shiga cikin mutanan da suke  kokarin kai Adeleke Asibiti na kusa da inda abun ya faru kafin daga baya a kai shi Asbitin koyarwa na Jihar Legas dake Ikeja inda ya mutu.

“Na tabbata Adeleke baya cikin wanda suke fada, shi dai yana cikin wanda suke raba fadan da ya kaure sakamakon rabon kudi. Bai san cewa Matthew yana rike da makami ba.”

Ya kara da cewa, lokuta da dama mutane na gagadin Matthew a kan wannan dabi’an nashi na daukan makami idan ana fada da shi, ba wanda ya san cewa wannan tsautsayin zai sauka a kan Adeleke. Na yi kokarin magana da maman mamacin amma kasancewar ba ta da miji tana wajan yar’uwarta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Chike Oti ya tabbatar da faruwar lamain, ya kara da cewa suna gudanar da bincike.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: