Mun Kafa Gidauniyarmu Ce Domin Tallafa Wa Al’umma --- Salisu Salinga — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Mun Kafa Gidauniyarmu Ce Domin Tallafa Wa Al’umma — Salisu Salinga

Published

on


Saboda tsananin rayuwar da al’umma ke ciki, tun daga matasa da suka kammala karatu, amma babu batun aikin gwamnati ko na kamfani, ga matasa da ya kamata su rungumi karatu da hannu biyu, halin kuncin rayuwa da iyayensu ke ciki, hakan bai samu ba, ga mata da mazansu suka rasu, suka ba su da yara da yawa, babu mai tallafa ma su, sai mai duka, ga kuma marasa lafiya na tafiya da cututtuka a jikinsu, rashin kudi, ya sa dole sun sa wa sarautar mai duka ido.

Kan wadancan matsaloli da mu ka zayyano su, da kuma matsaloli da yawa da ba mu yi ma tunaninsu ba, ya sa fitaccen dan jaridan nan da ke garin Kaduna mai suna SALISU UMAR SALINGA ya sami taimakon Allah, inda ya bude wata gidauniyar da ta ke tallafa wa al’umma mai suna SALINGA DEBELOPMENT FOUNDATION da cibiyar gidauniyar ke garin Kaduna, wannan gidauniyar ta yi fice wajen tallafa wa al’umma ma su mabanbantan matsaloli da suke cikin garin Kaduna da kuma wasu jihohi da suke sassan Nijeriya.

Wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ya samu damar tattaunawa da jagoran gidauniyar, jim kadan bayan sun kammala taron yaye wasu mata da matasa da suka kammala koyon sana’o’i daban–daban a karkashin wannan gidauniya, wanda taron ya gudana a makarantar sakandare ta tunawa da MAIMUNA GWARZO da ke garin Kaduna.

Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Ko za ka bayyana mana dalilan da suka sa ka kafa wannan gidauniya?

Babu shakka, makasudin kafa wannan gidauniya shi ne, domin tallafa wa marasa galihu, musamman marayu da iyayen marayun, wato mata ke nan da suke rike da marayunsu da kuma suke kula da su,sai yara mata da aka ci zarafinsu, wato kananan yara mata da aka yi ma su fyade da yara maza da ake yi ma su Luwadi, da kuma wadanda aka kwace ma su wani abu, suna neman hakkinsu, saboda ba su da karfi, suna ganin hakkinsu, amma ya yi ma su nisa, mu kan shiga wannan matsala, mu ga me ya dace mu yi, domin mu tallafa ma su, su sami mafita daga matsalolin da suke ciki, a wannan bangare, mun sami nasarori ma su yawa.

A kalla daga kafa wannan gidauniya, kun tallafa wa al’umma guda nawa?

A kalla tun daga shekara ta 2006 da kafa wannan gidauniya,mun tallafa wa al’umma da yawan gaske,amma fa farar da garaje, ba zan iya bayyana ma ka yawan wadanda suka amfana da tallafin koyon sana’a ko tallafin neman hakki da dai sauran ayyuka da wannan gidauniya ta ke yi ba.

Zuwa yanzu, wannan gidauniya a cikin garin Kaduna ta ke gudanar da ayyukanta?

Babu shakka, farkon kafa wannan gidauniya a garin Kaduna mu ka kafa ta, amma a halin yanzu, amma daga kafa ta zuwa yau, mun sami nasarar bude ofishin wannan gidauniya a daukacin jihohin arewacin Nijeriya har ma da Abuja,kuma a jihohin arewa ko wace jiha mu na zuwa domin aiwatar da ayyukanmu da na bayyana ma ka, na tallafa wa al’umma da suke jihohin arewa.

Kamar wasu ire-iren tallafi ake ba al’umma, baya ga wadanda ka bayyana ma na a baya?

Mu na bayar da tallafi a bangarori da dama,misalign ayyukan da zan fara bayyana ma ka shi ne, a kwai gida da mu ka gina wa wata baiwar Allah, da mijinta ya rasu ya bar ta da yara tara, ya rasu ya bar ma su daki daya, sai dakin ya rushe, dakin da ya rushe na kasa ne, amma da mu ka je gidan, mu ka lura da matsalolin bukatar muhalli da wannan mata ta ke da shi, sai mu ka gina ma ta dakuna uku da kicin da  wajen tsuguno da kuma wajen wanka.In kuma an sami matsalar iska,a na bukatar kwanon rufi, mu kan je mu bayar da gudunmuwar kwano, domin rufe gida ko kuma dakunan da aka sami matsala ko kuma matsaloli.

A bangaren marayu kuma, wannan bangare a ko wane lokaci mu na cikin ayyukansu, na kula da ci gaban karatun da suke yi da abincin da za su ci da tufafin da za su sa da kuma kul;a da lafiyarsu, sai kuma lokutan azumi da lokacin kirisimeti, in dai mu na da abinci a rumbun da mu ke a je abinci, mu na fitowa da su mu raba wa wadanda suke bukata a ko wane lokaci.Wannan ne ya sa ako wane lokaci, in ka`leko ofishinmu, musamman nan Kaduna, za ka ga yadda al’umma ke zuwa domin mu warware ma su matsalolinsu.

A bangaren sana’o’i kuma wasu tsare–tsare ku ke yi, domin tallafa wa al’umma?

Kamar yau da ka same ni a wannan makaranta ta tunawa da Maimuna Gwarzo, mun yi taron yaye wasu dalibai ne da mu ka koya ma su sana’o’i, kamar yin takalma da jakunkuna da dunki da saka da dai sauran sana’o’I ma su yawan gaske.

Me ku ke yi ga wadanda ku ka koya ma su sana’a, domin su ci gaba da yin sana’ar da kuka koya ma su?

Lallai mu kan koya ma su dabarun yadda za su ci gaba da yin sanar da mu ka koya ma su,da farko mu kan dauko wani masani a kan abubuwan da mu ke koya wa wadanda mu ka sa a gaba za mu koya ma su sana’ar, bayan an koya ma su, a kan kuma nuna ma su yadda za su ci gaba da yin sana’ar, wato in na sayar ne dai –dai, za mu nuna ma su, in kuma a dunkule za su sayar, za mu nuna ma su ta yadda za su amfana da sana’ar da aka koya ma su.Kuma wannan hanya da mu ke bi, ta na haifar ma na da ‘ya’ya ma su idanu fiye da tunanin ka.

Kuma mu kan koya wa wadanda mu koya ma su sana’ar yadda za su rika aje wani abu na daga cikin kudaden da suke samu, na abubuwanda suka sayar bayan sun kammala abubuwanda mu ka koya ma su.Yanzu haka mun sa su a kan wasu hanyoyin samun rancen kudi da gwamnatin tarayya ke bayarwa ta

wasu bankuna,mu na kuma nuna ma su yadda za su biya kudaden da aka ba su rancen, bayan sun kammala sana’ar da suke yi.

Daga shekara ta 2006 da ka kafa wannan gidauniya, za mu iya cewar ko kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?

Babu ko shakka, kwalliya ta biya kudin sabulu fiye da yadda mu kanmu da mu ke jagorantar wannan gidauna ta SALINGA a nan garin Kaduna da sauran jihohi mu ke tunani, da kuma sauran jihohi da suke arewacin Nijeriya.Domin a wasu lokuta a kan hanya ko a kasuwa da dai sauran wuraren da al’umma ke taruwa, sai ka ga mutum ya tsayar da kai ya na nuna godiyarsa na yadda wannan gidauniya ta tallafa wa rayuwarsa, ya sami rike kansa, har kuma ya sami damar koya wa wasu al’umma sana’ar day a iya.

A karshe, menene burin wannan gidauniya ta ‘SALINGA DEBELOPMENT FOUNDATION’ a shekaru ma su zuwa ?

Tun farko babban burin wannan gidauniya bai canza ba, kuma nan da shekaru ma su zuwa, ba zai canza ba.Wato, tun farko burinmu shi ne mu ga mun tallafa wa al’umma, kamar yadda na bayyana ma ka a baya, kuma na bayyana ma ka ire –iren tallafin da mu ke yi wa al’umma na kusa da kuma na nesa. Mu dai addu’armu ita ce, Allah ya ci gaba da ba mu tunanin yadda za mu aiwatar da ayyukan da mu ka tsara aiwatarwa a cikin wannan gidauniya, amin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai