Mai Tsaron Raga Joy Hart Ya Koma Kungiyar Burnley — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Mai Tsaron Raga Joy Hart Ya Koma Kungiyar Burnley

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Burnley ta sayi mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5.

Shugaban kungiyar Sean Dyche ya sayi mai tsaron ragar ne tare da saurarn masu tsaron raga biyu wato Nick Pope da Tom Heaton.

Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa Manchester City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin kalubale na FA guda daya.

Hart, ya fara nuna sha’awar barin Manchester City ne tun bayan da Kocin kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci wanda hakan yasa yatafi aro kungiyar Westham a kakar wasan data gabata.

Sau daya Hart ya kama wa Manchester City wasa tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016.

Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham ta kasar Ingila duk da cewa baiyi kokari a Westham din ba.

Hakazalika kasar Ingila ba ta je dashi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018 ba wanda hakan yasa ake ganin kamar rashin buga wasa a babbar kungiya ne yaja masa haka.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!