Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 2 A Jihar Ogun

Published

on

Hukamar kiyaye hadururruka reshen Sango-Ota ta ce, mutane biyu sun mutu hudu kuma sun ji mummunar raunika sakamakon wani hadari da ya auku a toll-gate) Sango-Ota ranar Asabar.

Shugaban hukumar reshen Sango-Ota Mista Adekunle Oguntoyinbo ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake hira da manma labarai a garin Ota, ya kara da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:45 na safe.

Oguntoyinbo ci gaba da cewa, babbar motar daukar kaya mai lamba kamar haka GGE 80 DJ wacce ta taso daga Abeokuta zuwa Legas ta samu kwacewar birki sakamakon mugun gudu sai ya murkushe motoci guda biyar. Ya kuma lissafa sauran motocin da lamarin ya faru da su, bas kiran Bolkswagen mai lamba kamar haka KTU 899 DR, Bolkswagon LT, (GGE 44 DL), Coaster Cibilian (LSR 604 DD), Ibeco Trailer (DB 190 MLF) da kuma bas kiran Mazda (KJA 667 DP). Ya ce mutane guda 15 ne lamarin ya rutsa da su amma mutane biyu ne suka mutu yayin da guda hudu suka samu mummmnar rauni.

Shugaban reshen ya ci gaba da bayanin yana cewa a cikin mamatan, daya ya zo shiga bas ne, dayan kuma ya zo tsallaka titi ne sai wannan mota ta buge su.

“An dai aje gawarwakin da lamarin ya faru da su a babban asibitin Ifo yayin da su kuma wadanda suka ji raunika aka kai su babban asibitin Ota domin shan magani, inji Oguntoyinbo. Ya ce kuma hukumarsa tare da hadin gwaiwar jami’an kula da tituna suna kokarin kauda duk motocin dake kan hanya domin a samu saukin zirga-zirga.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: