Jam’iyyar APC A Jihar Kano Ta Kafa Kwamitoci Biyu Don Sasanta Mambobinta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC A Jihar Kano Ta Kafa Kwamitoci Biyu Don Sasanta Mambobinta

Published

on


Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya kaddamar da wasu manyan Kwamitoci guda biyu wanda suka hada da Kwamitin Sasantawa da kuma Kwamitin Tuntuba, Alhaji Abdullahi Abbas ya bayyana dalilan kafa Kwamitoci da cewa an samar da su ne domin yiwa kallon wasu daga cikin abubuwan da ake kallo kamar suna da matsala domin kamo bakin zaren.
Shugaban Jam’iyyar ta APC a Jihar Kano ya ci gaba da cewa anyi dukkan mai yiwuwa domin zakulo wadannan jajirtattun mutane wadda idan dai kima da mutunci ake bukata to daga kan wadannan mutane sai dai ayi addu’a a tashi, yace Jam’iyyar APC da Jam’ar Kano sun gamsu da kyawawan ayyukan da Shugaban Kasa tare da Sahibinsa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje keyi, don haka kace wai kwace goruba a hannun kuturu ba wahala bace, to muna jiransu a bakin akwatunan zabe, kuma ina tabbatarwa da ‘yan Jam’iyyar APC cewa ficewar wancan da ake cewa wai kila a bashi takarar Gwamna a waccan Jam’iyyar, muna taya su addu’ar Allah yasa su bashi takarar su ga yadda zamu yi dashi a akwatun kofar gidansa, wanda ko akwatin da yake dabe ba ya iya lashewa, balle ace wai zai kara da Khadimul Islam.
Don haka sai shugaban Jam’iyyar ya tabbatarwa da jama’ar Kano cewa kowa ya kwantar da hankalinsa a tsaye muke, kuma alhamdulillahi ai zai yi wahalar gaske yadda jam’ar Kano suka ga luguden ayyukan alhairin Gwamna Ganduje, kuma ace mutanen da ake yiwa ihu a wuraren taruka, sune zasu ce sun shirya karbar mulkin Kano? Saboda haka sai shugaban Jam’iyyar ta APC ya bukaci Kanawa da cewa kowa yaje ya karkade kuri’arsa domin mu da ita zamu fatattaki wadancan domin mu bama tsafi balle bokanci.
Alokacin taron shugaban Jam’iyyar ta APC na JIhar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya kaddamar da Manyan
Kwamitoci guda biyu wanda suka hada da Kwamitin Sasantawa da kuma Kwamitin tuntuba. Inda Kwamitin Tuntuba ke karkashin shugabancin Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Kaboiru Alasa Rurun a matsayin shugaba, sai kuma mamboibin kwamitin da sukia hada da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Sanata Barau Jibrin, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, Abdullahi Tijjani Mohd Gwarzo, Sulaiman Abdurrahaman Kawu Sumaila, Murtala Sule Garo, Musa Iliyasu Kwankwaso, Alhaji Hamza Darma, Nasuru Yusif Gawuna, Nadu Yahaya, Alhaji Ahmad Rabiu, Barista Hajiya Damakka, Hajiya Gaje ‘Yar Mulki Sale A. Jeli, Alhassan Zainawa da Shehu Maigoro a matsayin Sakatare.
Haka kuma Shugaban Jam’iyyar na APC ya kaddamar da Kwamitin Sasantawa wanda ke karkashin shugaban kwamitin yakin neman zaben Gwamna Ganduje Alhaji Nasiru Aliko Koki, Alhaji Sabo na Nono, Hon. Yusif Abdullahi Ata, Alhaji Usman Alhaji, Mal. Ibrahim Khalil,Ambasada Kabiru, Murtala Sule Garo, Baffa Babba Dan Agundi, Haruna Zago, Musa Salihu Doguwa, Mustapha Buhari Bakwana da Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano a matsayin Sakataren Kwamitin.
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da kwamitocin guda biyu Kakakin majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Kabiru Alasan Rurun ya tabbatarwa da shugaban Jam’iyyar cewa da yardar Allah zamu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nasarar wadannan Kwamitocin biyu, sannan Kuma ya alkawartawa Jama’ar Kano cewa lokacin zaben kawai muke jira domin yiwa Gwamna Ganduje da Shugaban kasa Muhammadu Buhari luguden Kuri’u kamar yadda Gwamna ya alkkartawa Shugaban kasa.
Cikin wadanda suka halarci bikin Kaddamar da Kwamitoci akwai Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Majalisar Wakilai Abdurrahaman Kawu Sumaila, Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kano, shugabannin Jam’iyyar APC a matakin Jiha da kananan Hukumomi da sauran dubun dubatar ‘yan Jam’iyya da suka halarci taron wanda ya gudanar a shelkwatar Jam’iyyar dake Hotoro Kan titin zuwa Maiduguri a Jihar Kano.

‘Zan Samar Da Wakilci Na Gari A Karamar Hukumar Sabon Gari’
Honorabul Salisu Adamu Muhammed, ya sha alwashin kawo canji a yankin mazabarsa ta karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.
Matashin dan siyasan ya tabbatar wa da jama’arsa cewa, in har suka bashi kuri’unsa a zabe mai zuwa na 2019 a karkashin jamiyyar APC to shi ma zai cika masu alkawarin da ya dauka na kawo canji mai ma’ana ga jama’arsa
Honorable Salisu ya bayyana hakan ne a yayain da suke zantawa da walilinmu na shiyyar Zariya a ofishinsa dake kan titin wariya zuwa Sokoto Jim kadan bayan ya gama tattaunawa da kwamitinsa na bayar da tallafi ga marasa karfi da zai fara aiki a cikin sati mai zuwa.
Matashin dan siyasan ya ce, a kasancewarsa ya yi karatun a mazabarsa don haka yasan duk kalubalen da mazabarsa yasa take fuskanta kuma ya yaje wasu gurare yaga ci gaban da suke kawowa yankinsu a siyasance.
Haka kuma yace shi bashi da niyyar fitowa Takara amma bisa yadda al’ummar dake tare dashi suka nuna damuwarsu da ya kamata ya fito takarar don ya wakilcesu a kujerar majalissar tarayya hakan ne ya bashi kwarin guiwar fitowar sa takarar duk da yake sun bautawa jambiyar a shekarun baya.
Kuma yace in Allah yaso zai canza siyasar karamar hukumar Sabon Gari ya zuwa siyasa mai tsafta da baiwa kowa damarsa ba tare da wani matsalaba.
Yace Allah yayi wa mazabarsa albarka ta bangarori da zama musamman bangaren Ilmi wanda shine gishirin zaman duniya tunda a mazabarsa ne zaka sami duk abin da ake bukata karatun ko aiki babu wanda basu dashi don haka yace, baiga dalilin da yasa za a bar matasa kara zube ba.
Matashin dan siyasan ya sha alwashin in har ya ci zabe zai hada kai da sauran yan majalisa abokansa don kawo wa jihar Kaduna canji mai dorewa.
Kuma ya ce, zai zama mai karbar shawara a duk lokacin da aka kawo masa, kuma yana mai biyayya ga uwar jambiyar tun daga Jiha har zuwa karamar hukumar.
Haka kuma ya yi kira ga yan siyasan da su zama masu kishin al’umarsu ba kishin Kansu ba.
Kuma ya jinjina wa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari na sama wa matasa aiyukan yi tare da kaddamar da manyamanyan aikin ci gaban kasa baki daya.
Haka nan kuma yayi yabo ga mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rafa’i akan yadda yake gudanar da aikinsa a jihar Kaduna Baki daya kuma yayi fatan jama’ar jihar kaduna zasu ci gaban da bashi gudumnawa ta kowani fanni.
Malam Balarabe samaru na daya daga cikin masoyansa dake gundumar Bomo shima yabo yayin ga matashin dan siyasan Honorabul Salisu Adamu Muhammad, a kan yadda yake gudanar da siyasarsa a karamar hukumar Sabin Gari bani daya ya ce, ya zuwa yanzu ba a sami wani dan takara dake nuna kowa nasane ba kamar Honorable Salis Nayaya don haka ya ce ya kamata yan siyasan suyi koyi da halinsa don kawowa jambiyar APC ci gaba.
Ya zuwa hada wannan rahoton tuni Honorable Salisu Adamu Muhammed ya fara bin gundumomin da suke yankin sa don zakulo mata gajiyayyu da marayu don tallafa masu da wani abin masarufi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!