Hukumar NAHCON Ta Qaryata Batun Barin Alhazai 17,000 A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Hukumar NAHCON Ta Qaryata Batun Barin Alhazai 17,000 A Nijeriya

Published

on


Hukumar Kula da Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta qaryata rahoton da aka fitar na cewa an bar maniyyata 17,000 a Nijeriya yayin jigilar alhazan bana.

Kwamishina mai kula da gudunarwa na hukumar, Alhaji Abdullahi Modibbo ne ya qaryata wannan zargi yau a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Birnin Makkah.

Alhaji Modibbo ya qalubalanci wadanda suka shirya wannan rahoto na qage da su kawo madogarar wannan labari. Inda ya ce, an cimma nasarar kwaso gabadaya maniyyatan Nijeriya, idan banda daidaiku da suka samu sabanin bin jirginsu kamar yadda aka tsara.

“Abin da muka sani shi ne ya kamata dan jarida ya tabbatar da ingancin labarinsa kafin ya buga.

“Wannan labarin cewa an bar maniyyata 17,000 a Nijeriya qarya ne. Sanin kowa ne cewa muna da hanyoyi biyu na kawo alhazai zuwa qasa mai tsarki – walau ta hannun jihohi ko kamfanonin jigilar maniyyata masu zaman kansu (wadanda aka tantance).

“Ina qalubalantar masu wancan rahoton da su bayyana mana jiha guda da aka samu sama da maniyyata 10 da ba a yi jigilarsu ba. Don haka wannan zance, ba komi bane face qarya tsagoronta.” Inji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!