Abin Da Ya Sa Na Tsunduma Yi Wa ‘Yan Siyasa Waka - Real Boi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Madubin Rayuwa

Abin Da Ya Sa Na Tsunduma Yi Wa ‘Yan Siyasa Waka – Real Boi

Published

on


Shaharren mawakin zamanin nan Dan shekara goma 11 da haihuwa mai suna Ismail Aminu, wanda aka fi sa ni da Real Boi da ke karkashin Kungiyar Arewa Empire, ya bayyana dalilinsa na yi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufai, da Dan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC, Malam Uba Sani, waka na musamman, wanda shi ne karonsa na farko da ya taba yima wani Dan siyasa waka.

Ismail Aminu wanda akafi sa ni da real Boi, ya bayyana haka ne ga manema labarai jim kadan bayan da ya kaddamar da wata wakar mai taken “Elrufai Uba Sani Za Mu Yi”, wakar wacce ya kaddamar a Dakin taro na et cetra city, da ke Barnawa a Garin Kaduna.

Ismail Aminu ya ci gaba da bayyana cewa, “ Na zabi nayi ma Gwamnan Jihar Kaduna waka ne musamman yadda na lura da yadda ya gyara harkar ilimi a Kaduna, sannan ya mayar da ilimi kyauta a Kaduna, ga abinci da litattafan karatu da ake baiwa Dalibai kyauta. Sannan ya dauki ingattatun Malamai masu hazaka.”

Real Boi, ya kara da bayyana cewa, “Idan ka dauki harkar tsaro kawai, dole a nan ma ka kara jinjina ma gwamna, saboda yadda ya dauki harkokin tsaro da matukar muhimmanci sosai a fadin wannan jiha. Sannan ya dauki dimbin Matasa aikin yi a fannin tsaro sosai, musamman Kastelia, ‘Yan Bijilante, da dai sauran su.”

Da kuma ya juya dangane da Dan takarar kujerar Sanata a tsakiyar Kaduna, wato Malam Uba Sani. Real Boi cewa ya yi, “Abin da ya bani mamaki da wannan bawan Allah shi ne, duk sadda mutum yaje naiman wani abun alheri wajen Gwamnan Jihar Kaduna, zai ce maka kaje ka sami Uba Sani, shi ne ke kyauta da dukiyarsa, ni bana taba kudin gwamnati, domin kudin Al’umma ne. Amma shi Uba Sani, da dukiyarsa na halak yake kyauta.”

“Wannan abun da gwamna ke fadi akan Uba Sani, da kuma yadda yake taimakon Al’umma, musamman Mata da Matasa, shi ne yaja hankalina na yanke shawarar raira masu waka ta musamman domin nuna godiyarmu akan abin da suke yi ma Daukacin Matasan Jihar Kaduna.” A cewar Ismail Aminu, wanda akafi sani da Real Boi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!