Annobar Almajirci: Sarakunan Gargajiyan Arewa Sun Yi Taro A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Annobar Almajirci: Sarakunan Gargajiyan Arewa Sun Yi Taro A Kaduna

Published

on


Sarakunan gargajiya karkashin jagorancin Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar 111 da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF sun bayyana ra’ayinsuna kan yawa da karin yara da ke gararanba a kan titinan arewacin kasar nan basa zuwa makaranta a yankin Arewa, sun kuma tattauna yadda za a yi maganin lamarin.

Da yake jawabi a taron na kwana 2 mai taken ‘Building Collectibe Committment and Action on Out-of-School Children in Northern Nigeria: Issues and Reaponsibilities’, Sarkin Musulmin ya amince da cewa, yankin Arewacin Nijeriya ke da yara mafi yawa dake gararamba a kan titi basa zuwa makaranra, a halin yanzu a kwai yara fiye da Miliyan 13.5 da basa zuwa makaranta a fadin Nieriya gaba daya.

Ya ce, taron wadda hukumar UNICEF ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi da hukumar UBEC da hukumar yaki da jahilci ta kasa da kuma gidauniyar ‘Sultan Foundation for Peace and Debelopment’ zai taimaka matuka wajen maganin  wanna matsalar data addabi yankin gaba daya.

Ya kuma kara da cewa, “Ba wai Nijeriya bata da tsari da kuma hanyoyin magance matsalolin bane amma abin da aka rasa shi ne aiwatar da abin da aka shirya na shawarwarin da aka zartas.

“Lallai akwai matukar bukatar a kawo canji mai ma’ana a saboda haka ne masu ruwa da tsaki suka hadu don yin aiki tare.

“Bai kamata wannan taron ta tafi kamar yadda sauran tarukka suke tafiya ba”, inji Sarkin Muslmin.

A nata jawabin, mataimakiyar wakiliyar hukumar UNICEF a Nijeriya, Pernille Ironside, ta ce, binciken da ma’aikatan ilimi ta gudanar ya nuna cewa, akwai yara fiye da Miliyan 10.5 masu shekara 6 zuwa 14 dake gararamba a titi ba tare da zuwa makaranta ba.

“Idan muka yi naganar yaran da basu zuwa makaranta sai mu kasa gane su, amma binciken da aka yi na bayabaya nan ya nuna cewa, kashi 69 na yaran da basa makaranta sun fito ne daga yankin Arewa, jihar Bauchi keda yara mafi yawa, da Miliyan 1.1 million sai jihar Katsina ta zo na biyu da yara 781,500 da basa zuwa makaranta”, inji ta.

Ta kuma kara da cewa, “idan muka hada hannu za mu samu yanayin da yara da dama za su ci gaba da zuwa makaranta ba tare da wani matsala ba.”

Ta kuma ce, sanya jari a kan yara kamar sa jari ne a kan rayuwar kasa ne gaba daya, ta kuma kara da cewa, “A madadin kungiyar UNICEF, Ina karfafa kafa wata hadaka tsakanin Sarakuna gargajiya da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da iyaye don su hada hannu wajen tilastawa gwamnati ta tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga dukkan yaran Nijeriya gaba daya.

“In har Nijeriya na son cimma muradun karnin na majalisar dinkin duniya yana da mahimmanci a yi kyakyawar kokarin don cimma burin da aka sa a gaba.”

Babban sakataren hukumar UBEC, Hamid Bobboyi yace, lamarin yaran da basa zuwa makaranta a yankin Arewacin Nijeriya abin na da ban tsoro in kuma ba a iya yin maganinsa ba zai iya rusa tsarin ilimi na yankin baki daya.

“dole Arewa ta tashi daga barcin da take yi, tuni duniya ta yiu nisa a fanni kimiyya da fasaha sauran bangaririn Nijeriya na ta kokarin kamo su ta hanyar sanya yaransu a makarantu, amma yankin Arewa na can a baya ba tare da fuskantar cikakken abin da ilimi ke nufi bana san mutumcin mutum da ci gabanta.”

“A yankin Arewa dukkan matsalolin dake kare ci gaba samun iimin boko ya yi katutu, wadanda suka hada da auren wuri da al’amarin almajirci da kuma halayyar iyaye a kan harkar ilimin yaransu da kuma karancin ilimi na iyaye da sauransu.”

“Abin takaici ne da damuwa, a da yankin Arewa kafin wanna lokacin yake da tarihin tsayayen harkar da tsarin ilimi amma a yau ana kallon yankin a matsayin na baya a dukan sashin kasar nan baki daya, har ta kai ga kasashen duniya na tausaya mana saboda rashin ci gaba a fannin ilimi abin da kuma dake haifar da talauci”, inji Bobboyi.

Cikin wadanda suka samu halartar taron a kwai Shehun Borno da John Cardinal Onaiyekan da sarkin Kano da na Badeh da Daura da Zamfara da Hadejia da Katagun da sauran jama’a da dama.an kuma kaddamar da rukumin ofisoshi na gidauniyar ‘Sultan Foundation for Peace and Development.’

Advertisement
Click to comment

labarai