Yan Fansho A Kebbi Sun Sha Alwashin Gurfanar Da Gwamnati A Gaban Kuliya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yan Fansho A Kebbi Sun Sha Alwashin Gurfanar Da Gwamnati A Gaban Kuliya

Published

on


Wani gungun yan fansho  da suka ajiye aiki tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013  da suka dade suna gwagwarmayar neman a warfare cogen da aka yi wajen biyan su hakkokan su na ajiye aiki  sun yi ittifaki a kan za su gurfanar da gwamnatin jihar Kebbi a gaban kuliya manta sabo  bisa ga dalilin kin biyan su hakkokan su yadda ya kamata.

Da ya ke zantawa da wakilin mu a gidan sa da ke Argungu, Alhaji Buhari Gulma wanda ya ke yana daya daga cikin jagororin wannan tafiyar, ya bayyana masa da cewa bisa ga dukkan alamu gwamnatin Sanata Atiku ba ta da niyyar yi musu adalcin biyan su hakkokan su yadda ya kamata  saboda duk hanyoyi na da’a da ladabi sun bi don ganin ko da Allah zai sa gwamnatin ta biya amma duk a banza.

Ya ce tun farko dai wannan kungiyar ta rubuta wa ofishin shugaban ma’aikatan jihar wacce ta ke ita ce da alhairin biyan hakkokan ma’aikatan da suka ajiye aiki a jiha, ta kuma rubuta wa wani babban kwamiti mai aiki kan al’amurran da suka shafi fansho wanda Alhaji Muhammadu Kwaido ke jagoranta ranar 30/11/2015,  ta kuma rubuta wa hukumar ladubba da da’ar ma’aikata (code of conduct bureau), ta kuma rubuta wa hukumar suraren koke-koken jama’a (public complaints commission)  ranar 23/6/2015), ita kuma hukumar ba ta yaushe hannu ba inda nan take ta rubuta wa gwamnatin jihar ta hannun shugaban ma’aikata ranar 26/10/2015 zungureriyar takarda inda ta nemi a duba matsalar wadannan mutanen tare da daukar matakin biyan su hakkokan su,  ta kuma rubuta wa majalisar dokoki ta jihar inda har ma majalisar ta yi abin da za ta yi ta kuma mika wa gwamna don ganin an biya amma a banza,  har wa yau dai wannan kungiyar ba ta yi kasa a gwiwa ba ta garzaya wajen sarakunan gargajiya don neman ta sa baki don ganin an biya su hakkokan su, hukumar yan sanda  ma wannan kungiyar ta nemi ta saka baki inda ta kai wa Kwamishinan yan sanda takaradar neman ya tsoma bakin sa.

Gulma ya cigaba da cewa duk wadannan hanyoyin sun bi su ne saboda su nuna su ma’aikata ne kuma masu da’a ga shugabanni, inda har wadansu kungiyoyi sun kawo musu goron gayyata zuwa wajen yi wa gwamna azumi da kuma addu’o’in Allah tsine  amma suka ki.

Ya kuma bayyana wa wakilin na mu da cewa  matakin da kungiyar ta ke kan sa yanzu shi ne ta rubuta wa ofishin shugaban kasa da kuma  jam’iyyar APC ta kasa wanda kuma idan abin ya faskara to a nan ne za mu gurfanar da gwamnatin jihar sannan kuma za mu kuma dauki matakin gaya wa Allah ta hanyar addu’o’i.

Kowa ya sani gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi makuddan kudade don biyan hakkokan jama’a da ke kan gwamnatocin jihohi amma wadansu azzalumai sai suka sauya akalar kudaden zuwa wajen shari’o’in zabe da kuma sharholiya.

Duk irin kokarin da wakilin mu ya yi na ganin kwamishin kudi na jihar Alhaji Ibrahim Augie ya ci tura amma ya same shi ta wayar tarho kuma ya tambaye shi inda aka kwana dangane da cika wannan gibin da aka zabtare wa ma’aikatan da suka ajiye aiki a shekarun 2012 da 2013 inda ya ce ba zai iya amsa wannan tambayar ba a yanzu, ya kuma yi alkawarin zai kira, amma dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira ba.





Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!