Mafi Karanci Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Ki Halartar Zaman Sulhu Da Gwamnatin Tarayya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Mafi Karanci Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Ki Halartar Zaman Sulhu Da Gwamnatin Tarayya

Published

on


Gamayyar kungiyoyin kwadago sun ki halartar zaman sulhu da gwamnatin tarayya a yau Lahadi, a shirya zaman sulhun ne don a samu bakin zare kan aiwatar da mafi karancin albashi a adadin Naira 30,000 wanda kungiyoyin kwadagon suka nace shine zai zama sabon albashi ba Naira 22,000 ba, kamar yadda kungiyar gwamnoni ta bukata.

Gwamnatin tarayya ce ta shirya zaman sasantawar da kungiyoyin kwadago, da kuma masu ma’aikatu masu zaman kansu, a tsara za a yi zaman ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, a yau Lahadi.

A ranar Juma’a da ta gabata kotun ma’aikatu ta kasa ta yanke hukuncin hana kungiyoyin kwadago shiga yajin aikin da suka tsara za su fara a ranar 6 ga watan Nuwamba, amma ‘yan kwadagon sun yi biris da umarnin, saboda a cewarsu kotun bata da hurumin hana su shiga yajin aiki.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!