2019: NNPP Za Ta Ceto Al’umman Bauchi Daga Mawuyacin Hali –Barde — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: NNPP Za Ta Ceto Al’umman Bauchi Daga Mawuyacin Hali –Barde

Published

on


ALHAJI MUHAMMAD BARDE, Shi ne shugaban jam’iyyar NNPP mai alamar Kwando da kayan dadi. A hirarsa da LEADERSHIP A Yau, ya shaida cewar, jam’iyyarsu ita ce kadai ta shirya shawo kan matsalolin da suka yi wa jihar Bauchi katutu, yana mai bayyana cewar suna kuma da tabbacin a zaben 2019 sune za su shimfida mulki a jihar Bauchi a sakamakon so da kaunarsu da jama’an jihar ke yi, har ma ya tabbatar da cewar za su kara da PDP da APC kuma za su kayar da su a zaben 2019. KHALID IDRIS DOYA ne ya zanta da shi kamar haka:

Da wa muke tare a wannan lokacin?
Sunana Alhaji Muhammad Barde, nine zababben shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Bauchi.

A wace yanayi jam’iyyarku take ciki a yanzu, ganin cewar an gama yin zabukan fitar da gwani a jam’iyyu?
Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, wanda shi ne ya bamu ikon kawo wannan jam’iyyar mai albarka zuwa jihar Bauchi, kuma Allah ya haska mana ita da dukkanin nau’o’in nasarori. Tambayarka gareni. A daidai wannan lokacin ina tabbatar maka jam’iyyar NNPP jam’iyya ce wacce muka gudanar da zaben cikin gida muka tsaida ‘yan takara bisa adalci da kwanciyar hankali, zabukan da muka yi a kujeru sun kai 47, a sakamakon adalcin da muka yi a cikin zaben nan, babu wani wanda ya je ko kafar sadarwa guda daya ya yi korafi kan zabe, ka ga mun yi adalci sosai a tsakanin ‘yan takararmu, wanda hakan ya kara hada mana kan ‘yan takara da sauran wadanda basu samu nasara ba. mun yi zabe mai inganci sabanin sauran jam’iyyu wadanda in ka bincika za ka tabbatar ba zaben suka yi ba, kama-karya suka yi wa ‘ya’yansu. Kamar misali idan ka dauki jam’iyya mai mulki ta APC sai ma dai na jajanta wa ‘yan uwana ‘yan siyasa a bisa halin da suka fada karfa-karfa da aka yi musu da danniya, da rashin mutunci irin ta siyasa, aka je aka yi rubutu kawai aka gama, wanda har yanzu ana korafi kan zaben cikin gida da APC ta yi, wanda hakan bai kamata ba kuwa, amma mu adalcinmu ya tabbatar wa duniya mun yi shirin kwace mulki domin mune za mu yi wa jama’an jihar Bauchi adalci, idan ka gaza iya adalci a cikin gidanka wani adalci kuma za ka iya yi wa na waje?, don haka ko a nan dan jihar Bauchi ya san mun ja damarar kyautata masa rayuwa bayan zaben 2019, dazarar muka shiga gidan gwamnatin jiha.

Waye ku ka tsaida takarar gwamnan jihar Bauchi na zaben 2019?
Mun tsaida Ambasada Shu’aibu Ahmad, shi ne zai fito ya kara da saura jam’iyyun da za su shiga zaben 2019, kuma tabbas muna kan ganin nasara da yardar Allah.
Kana ta kokarin nuna cewar jam’iyyarku a dinke take, amma kuma mun ga wasu daga cikin mambobin jam’iyyar sun fice, ciki har da Sakataren jam’iyyarku, me za ka iya cewa a matsayinka na shugabanta?

Ka san daman ita siyara ra’ayi ce, don haka ba za ka taba rasa ra’ayi da ‘yan abubuwa wadanda ba a rasa ba, domin dukkanin dan siyasa yana da ra’ayinsa na ya zauna a cikin jam’iyya ko ya fita, duk lokacin da ya ga dama zai iya zama mamba a kowace jam’iyyar siyasa, kuma idan ka kalli jam’iyyar NNPP ai har yanzu cif muke kanmu lallai a hade yake, wadanda suka fice daga cikin jam’iyyar ba wani yawa suke da shi da har za a iya nunasu a ce gashi a zo a gani ba, kamar yadda jama’a suke ta maganganu a kai, idan ka hada mu da jam’iyya mai mulki ta APC a lokaci guda daya Sanatoci kusan 15 suka fice a cikinta a lokaci guda, ga shi ‘yan takara da mambobin jam’iyyar sai ficewa suke yi, abun takaici dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fita daga cikinta, wanda ya yi takaran shugaban kasa a jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya fita daga jam’iyyar, Kakakin Majalisar tarayya ya fita, shugaban majalisar dattawa ya fita, mutane muhimmai sun fice daga cikin jam’iyyar, don haka idan kana maganar fita daga cikin jam’iyya ne ai ba ma zaka yi maganar wai wani ya fita daga cikin jam’iyyar NNPP, a kowani lokaci mu mutane kawai muke karba, kamar yadda ka zo ka samemu yau ka duba yadda dandazon jama’a suke ta shigowa cikin sabuwar sakatariyarmu kowa sai sambarka da neman mu hau mulki domin kyautata shugabanci a jihar Bauchi.

NNPP kamar ta fi karfi a jihar Bauchi, ga kuma rikicin cikin gida da ke binku, ta wacce hanya ne za ku iya kwace mulki daga APC?

Ina mai tabbatar maka ita batun kwace mulki a hanun Allah ake nema, kuma da yardar Allah mune za mu kafa gwamnati a zaben 2019 a jihar Bauchi. Kuma yadda karfinmu yake muna daram babu gudu ba ja da baya, yanzu haka mun sake sabon salo, mun shirya mun ja damarar kwace mulki daga hanun APC, mun kuma yi sabon tsari tun daga kasa, a kullum sai amsar sabbin mambobi muke yi, daga jihar APC ne, PDP ne da sauran jam’iyyu kullum sai amsar sabbin mambobi muke yi.

Wai shi wacce sindabaru ne za ku yi amfani da ita har ku iya yakar PDP ku zarce kan APC har ku dale kan mulki?

Ai daman idan ka dauka a jihar Bauchi dai jam’iyyun siyasa guda biyu ne, da jam’iyyar adawa ta PDP da kuma jam’iyyarmu mai albarka NNPP mai Kwando da kayan dadi aljanna mai masoya da yawa. Ita PDP ai jam’iyyace da ake mata lakabi da dan-ba-kara, gurguwa da auren nesa. Don haka ina mai tabbatar maka cewar za mu karbi gwamnati a jihar Bauchi cikin ruwan sanyi, kowa ya gani ai yadda muke da jama’a da daman gaske a jihar nan, mune muka yi taro a lokacin nan kafin cike gurbi, taron da a tarihin siyasa jihar Bauchi zai yi matukar wahala ka samu wannan jam’iyyar da za ta iya tara wannan taron, koma jam’iyyar da take kan mulki ne kuwa. Don haka idan ana maganar jam’iyyar adawa da za ta kwace mulki a jihar Bauchi mune ai, babu wata jam’iyyar da take samanmu kuma indai a wannan lokacin ne, kawai jam’iyyar da ke mulki za ka iya cewa suna da iko ne kawai don suna kan mulki, amma gobarar da take cikin gidansu babu ita a cikin jam’iyyarmu kwata-kwata.

Wasu na cewar jam’iyyarku nan ta ‘yan kwangilace ma kawai, shin haka ne?

Kan wannan maganar da wasu ke cewar jam’iyyarmu ta NNPP ta ‘yan kwangila ne, wannan duk labari ne kawai. Domin zan bayyana maka banbancin da ke tsakanin kwangila da jam’iyya ta gaskiya, mutane a jihar Bauchi dukkaninsu wayayyoyi ne, ‘yan Bauchi gogaggu ne a harkar siyasa, mutanen Bauchi sun san abun da suke yi, masu lissafi ne, gari ne da ke da malamai, matasa masu tsayuwa domin doharo da kansu, ga mata masu sana’o’i da ilimi da sanin ya kamata. Don haka ba kowace maganace za a zo a fada wa jama’an jihar Bauchi ta yi tasiri ba, jama’an Bauchi sun rigaya sun gama sanin cewar jam’iyyar nan mai kayan dadi itace kawai mafitarsu a wannan lokacin, don haka duk wani farfaganda da wani yunkurin dakusar da tafiyar ba zai kai ga nasara ba, irin wadannan maganganun da kake jin wadanda suka tabbatar mun tsokale musu ido ne suke fitowa da ita domin neman yarfe, amma jam’iyyar ta fi karfin hakan. Jam’iyyar nan ne jama’an suka tabbatar ta yi shirin tunkarar gwamnatin mai ci har ta kwace mulki a jihar Bauchi.

Dan takararku da kuka tsayar na gwamna, ya zaka bayyana nagartarsa da kake wannan tutiyar?

Idan kana tambayana Ambasada Shuaibu Ahmad ne, to ina tabbatar maka wannan bawan Allah, idan da za a ce hadakar kasashen Afirka za su hadu su fitar da nagartacce mutum daya a matsayin shugaban kasa, lallai Shuaibu Ahmad ya cancanta, balle gwamnan jihar Bauchi. Dalilina na fadin hakan ba a taba samun dan takarar da yake da nagarta wanda idan ka dagashi, ka kade shi zaka tarar baida zunubi irin na siyasa kamar Shuaibu Ahmad.

Ambasada Shuaibu Ahmad wani bawan Allah ne da ya rike mukamin mai bayar da shawara wa gwamnatin Ahmad Mu’azu kan harkokin kudi, ya zama kwamishina na tsare-tsare da harkar kudi, ya taba zama sakataren gwamnatin jihar Bauchi, shi ne wanda ya mika ragamar mulkin gwamnatin Ahmad Mu’azu a 1999 zuwa 2007 shi ne ya mika wa sabuwar gwamnati, har yau ba a taba bincikarsa kan ya dauki tsinken sakacen gwamnatin jihar Bauchi ba. sannan idan ka dauki jihar Bauchi Ambasada Shuaibu a lokacin da suke gwamnatin baya, shi ne ya saita albashin jihar Bauchi ya sanya ta akan kwamfuta, shi ne idan ka kallesa mutum ne mai ilimi, mutum ne wanda jama’a suka shaida nagartarsa, a dukkanin ‘yan takarar gwamna a fadin Nijeriya ina shaida maka ina kuma kalubalantarka ba za ka taba cire wani dan takarar da ya kaisa nagarta ba.

Dan takararmu ne a lokacin da suna gwamnatin Muazu shi ne ya je ya yi fadi tashi ya amso dajin Yankari har ya zama mallakin gwamnatin jihar Bauchi a lokacin da yana hanun gwamnatin tarayya. Wannan nagartacccen mutumin da muka tsayar lallai babu irinsa a jihar Bauchi, shi ne ya yi Ambasada a kasar Katar. Irin su Ambasada Shu’aibu sune jihar Bauchi take nema a wannan lokacin, mutum ne wanda ya kware kan harkar kudi, ya samu lambobin yabo a ciki da wajen kasar nan, ya samu takara rawa sosai, kana shi ne nagartaccen kuma kwararen masani kan harkar kasuwanci.

Wasu gazawar gwamnatin jihar Bauchi mai ci kuka gani da ya sanya kuke shirin kwace mulki a hanunta?

Gazawar da gwamnatin jihar Bauchi ai sun fi rana bayyana, yanzu nan inda muke hira da kai idan ka daga kanka daga wannan saman benen za ka hango titin da ya tafi Federal Low Cost a sakamakon tafiyar hainiya da wannan aikin ke yi, masu asima kawai da zaka kirga da wannan titin ya illata baka isa ka kirgosu ba, shekaru uku ana faman gina titin da bai wuce kilimomi shida zuwa biyar ba, yanzu idan ka dauko mace mai ciki a wannan titin na Federal Low Cost sai dai ta haife maka jaririn a kan titi mata ‘yan uwanta su zo su yi kokarin tsallar da ita, wannan fa a nan kusa da wurin da muke magana nake fada maka, a jihar Bauchi karkashin wannan gwamnatin babu wani aikin da gwamnatin nan ta fara ana kammala har zuwa yanzu, jama’a suna ta batu kan basu ga aiyuka ba.

Wani tabbaci ne za ku baiwa jama’an jihar na cewar idan ku kuka zo gwamnati za ku yi aikin da jama’a suke so?

Mu ai muna da banbanci da wannan gwamnatin, banbancin idan ka kalli zubinmu kawai za ka gane mu asalin ‘yan jihar Bauchi ne, ita kuma jihar Bauchi tana bukatar a samu asalin dan jihar Bauchi ne da zai shugabancenta, idan ka samu dan jihar nan ne ka nemi a yi maka aiki, dukkaninmu idan ka duba mun kai munzalin da za a je wurin wane ya tsawatar mana ko ya jinjina mana. Mai daki shi ne ya san inda ke masa yoyo. Kuskuren da ake yi shi ne, jama’a ba ma wajen kamun kifin kadan za su tsaya ba, sai su tashi su je har Kogi dauko maka kwado su daura maka shi a kan kujera, wanda ko kujerar tsinare ba zai daina tsalle ba. don haka mu ai babu hadi, aiki ne a gabanmu da kishin jihar domin mune ‘yan jihar.

Kan dai batun rikicin cikin gidanku, meye gaskiyar cewar akwai wadanda aka turo don su bata tafiyar jam’iyyarku?

Wannan ai daman shi ne abun da aka shirya, an yi dukkanin wadannan abubuwan, gwamnati ta shigo ciki ta turo ‘yan kwangilanta suna kuma cewa wai mune ‘yan kwangila. Mu ‘yan adawa ne da muke tunkarar gwamantin mai ci, kowa kuma ya sani a jihar nan.

Kuna zargin a cikinku din akwai wadanda aka sayesu ne?

Eh kwarai kuwa, ai idan ana maganar kwangila, yanzu misali ka tambayi ‘yan PDP shin akwai adawa a tsakanin PDP da NNPP ne? babu adawa a tsakanin jam’iyyun adawa, dukkanin jam’iyyun adawa ai suna adawarsu ne da gwamnati ba da jam’iyyun da basu mulki ba. su akuya ne suke saka fatar kura sai su dawo su jingina suna yakar wasu.

Wai shin ma su waye ne kuke zargi da kwangilar?

Ka san mu bamu taba cewa ga kaza ka gaza ba, amma jama’an jihar Bauchi sun san su waye ‘yan kwangila. Amma ba dai ka zo mu ka ce mune ‘yan kwangila, jama’an jihar Bauchi sun san yadda muka tayar wa gwamnati mai ci hankali, sun san mune kawai masu amsar mulki. Ina tabbatar maka yadda jama’a suka gamsu da mu jama’a za su zabemu ne a bisa nagartarmu, mata, matasa, ‘yan fansho da sauransu kowa zai zabemu.

Ba ka ganin za a iya magudi a zaben 2019?

Eh to muna kyautata zaton cewar a wannan lokacin ba za a yi magudin zabe ba, domin jami’an tsaronmu muna da tabbacin za su iya takara rawa. Babu yadda za a yi tsohon shugaban kasa Jonathan zai samar da na’urar tantance kuri’a a samu sahihin zabe, su kuma su zo su yi nasara a ta wannan hanyar, kuma muna sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai bayar da damar yin magudin zabe ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!