Murabus Din Sheikh Ibrahim Khalil Ya Sake Zaizaye Gwamnatin Ganduje — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Murabus Din Sheikh Ibrahim Khalil Ya Sake Zaizaye Gwamnatin Ganduje

Published

on


Daga dukkan alamu ficewar fitaccen malamin addinin Islama kuma shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, daga gwamnatin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta hanyar ajiye mukaminsa na mai bada shawara kan ayyuka na musamman, ta kara nuna yadda gwamnatin ke cigaba da zaizayewa gabanin babban zaben Najeriya na 2019 da ke sake karatowa.

Hakan ya fito fili ne sakamakon yadda kwanaki kalilan kenan da wani fitaccen malamin addinin Musuluncin kuma kwamandan Hizba na jihar ta Kano, wato Malam Ibrahim Daurawa, ya fito karara a hudubarsa ta Juma’a ya soki lamarin yadda a ka nuna bidiyon gwamnan a na zargin ya na amsar cin hanci daga ’yan kwangila.

Masana siyasar jihar Kano na nuni da cewa, malamai su na da matukar tasiri a siyasar jihar. Don haka su na da muhimmiyar rawar da su ke iya takawa a lokacin zabe.

Shi dai Sheikh Khalil baya ga kasancewarsa malamin addini mai dalibai da mabiya masu yawa a jihar, ya kuma kasance daya daga cikin kwararrun ’yan siyasa jihar da a ke matukar giramamawa, saboda kyakkyawar alakara da ya ke da ita tsakaninsa da malamai da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar jihar.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi malamin don jin ta bakinsa kan dalilinsa na ajiye mukamin, Sheikh Khalil ya bayyana ma sa cewa, a yanzu ba ya son cewa komai game da lamarin, amma dai ya tabbatar ma sa da cewa gaskiya ne batun ajiye mukamin.

Duk da cewa, malamin bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar ba, to, sai dai kuma wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, shehin malamin ya na shirin koma wa jam’iyyar PRP ne, jam’iyyar da a yanzu a ke gani a matsayin wacce ke cigaba da samun karbuwa da tagomashi a fadin jihar, saboda yadda zakakuran ’yan siyasa ke faman tsunduma a cikinta daga manyan jam’iyyun jihar, wato ita APC da kuma PDP.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto shi kuwa Malam Daurawa ba a samu labarin ko zai ajiye mukamin nasa ko a’a ba. Bayanai dai sun nuna cewa, tsohuwar jikakkiya ce tsakanin Ganduje da Daurawa, inda a ke ganin cewa, malamin ya samu matsala da gwamnan ne tun lokacin auren zawarawa da gwamnatin ta gudanar, inda a ke zargin ta hana hukumar Hizba ikon kashe kudaden da a ka yi hidimar auren da su.

Shi kuwa Sheikh Khalil a na danganta ficewarsa daga cikin gwamnatin ne, don ya nesanta kansa daga yadda mutuncin gwamnatin ke cigaba da zubewa a idanun jama’ar jihar tun bayan da badakalar hoton bidiyon Gandujen ta fito fili.

Hakazalika, mabiyan an ce malamin ya na samun matsin lamba daga mabiyansa kan ya ajiye wa gwamnan mukaminsa, saboda su na zargin gwamnan da nuna mu su rashin mutuntawa a lokacin da a ke gwagwarmayar neman mukamin mataimakin gwamna, bayan da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafizu Abubakar, ya ajiye mukamin.

An ce duk kasancewar Gwamna Ganduje bai amsa kiraye-kirayen da a ka yi ta faman yi ma sa kan ya bai wa shehin malamin mukamin mataimakin gwamnan, bugu da kari kuma bai mutunta shi ta hanyar neman zama da shi, don kwantar wa mabiyan malamin hankali ba, wadanda su ne su ke so malamin nasu ya fito takarar gwamna tun da dadewa.

A yanzu haka dai an zura idanu a ga jam’iyyar Sheikh Khalil zai koma ko kuma ya cigaba da zama a cikin APC a jira a gani ko Ganduje zai fadi a zabe, sannan a zo a gyara jam’iyyar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!