Gwamnatin Tarayya Tana Tsimin Naira Biliyan 24 Duk Wata Ta Tsarin TSA – Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Tana Tsimin Naira Biliyan 24 Duk Wata Ta Tsarin TSA – Buhari

Published

on


Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewar gawmanatin sa, tana yin tsimin jimlar Naira biliyan 24.7 duk wata sakamakon kaddamar da Asusun bai daya TSA da kuma dakile ma’aikatan bogi. Buhari wanda ya sanar da hakan a taron fasaha da ake ci gaba da gudanarawa a Birnin Tarayyar Abuja da aka fara a ranar Litinin data wuce. Ya kuma umarci hukumar kimiyya da fasaha ta kasa NITDA wadda ta shirya taron da ta kai rahoton dukkan ma’aikata da hukumar da suka gaza wajen kammala ayyukan sun a kimiyya kafin a wanzar da aikin. Shugaban ya bayyana cewar, gudunar da fannin da sadarwa da fasaha na kasa, ya sanya an samu kari daga kashi 10 bisa dari a shekara 2017 zuwa kashi 11.8 bisa dari zangon shekara ta biyi na 2018. Ya ci gaba da cewa, tsaurarawar da aka yin a yin amfani da tsarin na TSA da tsarin bayanai da kuma tsarin BBN sun samar da ci gaba wajen aiwatar da ayyukan gwamnatin. Acewar sa, bayan dakile ma’aikatan na bogi hakan ya sanya gwamnatin ta tara kimanin Naira biliyan 24.7 harda kuma samun rarar Naira biliyan1.6 daga TSA.Shugaba Buhari ya ce, “ in zaku iya tunawa a jawabin da na yi shekarar data wuce a taron da aka gudanar na bijiero da maganganun da suka shafi fasaha gudunmawar da kimiyya zasu bayar wajen ciyar da tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da kimiya da kuma gudunmawar da kuma gudunmawar da fannin zai bayar na kimanin kashi 10 bisa dari na arzikin kasar nan.”Buhari ya kara da cewa, “Ina son in sanar daku cewar, wannnan magana ce babba data shafi ma su ruwa da tsaki a kan kokarin da suke yi a fannin kimiyya da fasaha, wanda anyi kokari sosai a fannin a cikin zangon shekara ta biyu ta 2018, inda aka samu kashi 11.81 bisa dari na karuwar arziki.” A nasa jawabin a wurin taron, Ministan Sadarwa Mista Adebayo Shittu ya ce, kimaiyar a kasar nan ta karu daga kashi10 bisa dari a 2014 zuwa kashi 23 a cikin watan Okutobar 2018.Ya ce, fannin na ICT na kasar nan, a bude yake ga ma su son zuba jari, inda ya kara da cewar jarin da kamfanonin kasar waje suka zuba a fannin na kai tsaye, ya karu daga dala biliyan 3.2 a 2015 zuwa dala biliyan4 a 2018. Shi kuwa Darakta Janar na NITDA, Dakta Isah Ibrahim Pantami a nasa jawabin ya ce, daukacin kasashen duniya sun a gusawa daga tsohuwar hanyar yin amfani da kimiyya zuwa ta zamani don ciyar da tattalin arzikin su.Acewar sa, a dalilin hakan ne ya sa aka zabo taken taron na bana na daukaka tattalin arziki ta hanyar yin amfani da fasaha da kimiyya ta hanyar sanya idon da ya dace. Shima tsohon Shugaban Hukumar yaki da cin jhanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewar, sabon tsarin na kimiyya zai taikama wajen yaki da cin hanci da rasahawa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!