Connect with us

FILIN FATAWA

Hukuncin Kashe Kwado A Musulunci

Published

on

Assalamu alaikum Malam menene ingancin hadisin da yake cewa: “Annabi SAW ya hana kashe Kwadi saboda kukansu Tasbihi ne ga Allah”?
Wa alaikum assalam, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lambata: (5269) da kuma Nas’i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Manzon Allah akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi ya hana shi kashe su”.
Baihaki ya rawaito daga maganar Abdullahi Bn Amri bn Al-Ass cewa “Kada Ku kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Ubangijinsu”. Duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa ya ji ne daga Manzon Allah saidai Hafiz Bn Hajar yana cewa “ Abdullahi bn Amr bn Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman Yahudu da Nasara don haka ba dole ne ya zama daga Annabi SAW ya ji ba.
Kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nasa’i da ya gabata. Allah ne mafi sani

Hukuncin Wasan Kwallon Kafa A Musulunci
Malam ina tambaya ne akan kwallon kafa, a kwai wanda yake neman aurena sana’arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake komai, so malamina kokonto akan wannar sana’ar tasa, kada ya kasance sai an yi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana biyansa idan suka yi wasa, to shi ne malam ko a takaice a sanar da ni wani abu a kai, saboda musan makamarmu, nagode.

To ‘yar’uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai suna kasa kwallo gıda uku :
1. Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu su hadu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan kam ta hallata mutukar ba ta kautar daga ambaton Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .
2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su hada kudi su sayı kofi wanda a karshe kungiya daya za ta dauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a tsakanin ‘yan kwallo.
3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari’a ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin abin da aka togace, sannan akwai barna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu. Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau’i na na biyu ko na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki ji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar dake da haramun.
Don neman karin bayani duba Fataawaa Al-lajna Adda’imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad bn Ibrahim 8/116. Allah ne mafi Sani.

Zakkar Gidan Haya Da Motar Haya

Assalamu alaikum. Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?
Waalaikumussalam. To dan’uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za’a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa .
Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kudin kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za’a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa. Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado(189)
Assalamu Alaikum inayimaka fatan alheri malam mutum yamutu yabar matar aure da yara mata 5 sai yan,uwa shakikay 3 sannan akwai li,abbai malam yaya rabon zaikasance Allah yakara lafiya.
Wa alaikum assalam. Za’a raba gida (24), a bawa matarsa kashi (3) yaransa mata kashi (16) ragowar sai a bawa ‘yan’uwa shakikai. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Kari Ko Ragi A Cikin Al’ada
Assalamu Alaikum. Da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan ALLAH mal ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Na gode
Wa’alaikumus Salam. To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa: “Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bukhari 1\426. Allah ne mafi Sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!