Connect with us

RAHOTANNI

Jan Kafa Wajen Bai Wa Kotuna Cikakken ’Yanci, Barazana Ne Ga Fanin Shari’ah

Published

on

Bangaren Shari’ah yana daya daga cikin muhimman fannoni dake taimakawa wajen samun adalci, daidaito, ci gaba da kuma wanzar da zaman lafiya da aminci a cikin al’umma.

Samun bangaren shari’ah mai cikakken cin gashin kanshi shi ne matakin farko na karfafa shari’ah ta yadda za ta yi aiki cikin adalci babu sani kuma babu sabo ba tare da la’akari da matsayi ko arzikin mutum ba. Wanda wannan shi ke sa gwamnati da al’umma su girmama shari’ah domin ta fi karfin kowa babu wanda yafi karfin doka ta yi aiki a kan shi ko kan ta.

Cikakken cin gashin kai ga bangaren shari’ah yana bai wa ma’aikatan fanin shari’ah tun daga Alkalai, Magatakardun Kotu da masu taimaka masu wajen cire tsoro su zage dantse domin yin aiki a cikin gaskiya ba tare da kallon abin hannun masu kara ba ko karbar wani abu daga wajen su ba.

Rashin wannan cikakken ’yanci ya yi karan tsaye ga jin dadi da walwalar ma’aikatan kotuna wanda takai ga karbar na goro daga wanje masu kara a inda masu hannu da shuni da kuma masu iko suka raina kotu, a inda kuma talakawa a kasar nan tamu suka yanke kauna da samun adalci a gaban shari’ah. Duk da cewa ba’a taru aka zama daya ba, akwai Alkalai da sauran ma’aikatan kotu wanda kudi ko matsayin masu kara ba shi ne a gaban su ba face yin adalci domin bai wa mai gaskiya hakkin sa.

Hakika ma’aikan kotuna sun sha fafutuka da fadi tashi wajen kyautatuwar yanayin aikin su wanda zai kawo karshen samun matsaloli wajen gudanar da shari’o’i musamman zargin karbar ci hanci wanda ya yi wa ma’aikatan kotuna da dama sanadiyyar barin aiki ta hanyar kora ko ritayar dole saboda rashin kyakkyawan yanayin aiki.

Wannan fafutuka tun lokacin sojoji ake yinta haka bata cimma ruwa ba. Lokacin da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya karbi mulki a matsayin shugaban kasa na farar hula ya ci karo da wannan bukata ta bai wa kotuna cikakken ‘yancin cin gashin kansu tun daga matakin jihohi wajen basu kudaden gudanarwarsu kaitsaye. Amma sai wasu daga cikin gwamnoni suka ki amincewa da wannan bukatar kamar yadda basa son cire tsarin nan na asusun hadaka da kananan hukumomi. Haka wannan magana ta lalace.

Bayan zuwan Marigayi tsohon shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya yi irin wannan yunkuri na ganin an bai wa kotuna cin gashin kansu, amma matsalolin rashin lafiya da ya sha fama dasu suka kawo masa cikas.

Ma’aikatan kotuna basu hakura da wannan yunkuri nasu ba bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki, wanda yasa Gwamnati ta dubi wannan bukata ta neman bai wa kotuna cikakken yanci wanda a karin farko aka amince da shi a matakin kasa. Amma sai ga shi ana tsammani fara aiwatar da tsarin a cikin watan Satumba na wannan shekara damu ke ciki sai ga shi har mun kai karshen watan Nuwamba ba’a fara ba wanda bai rasa nasaba da wasu da basu son aiwatar da shi a matakin jihohi.

Hakika tarihi ba zai manta da kai ba a matsayin shugaban da a lokacin sa aka bai wa kotuna cikakken cin gashin kan su.

Mai girma Shugaban Kasa kar ka bari wani ya kawo maka cikas a cikin wannan kyakkyawar niyyar taka da za ta kawo gyara a bangaren shari’ah. Domin bangaren shari’ah shi ne ginshikin ci gaban kasa, ci gaba da dorewar zaman lafiya.

Ado Umar Lalu

adoumarlalu57@mail.com

 

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: